BAYANI DAGA MAJALISAR MALAMAN AFRIKA GAME DA BARAZANAR DA 'YAN UWANMU MUSULMI NA AFRIKA TA TSAKIYA SUKE FUSKANTA(Dr. Mansur Sakkwato)

Danna nan domin shiga karatu Online

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
BAYANI DAGA MAJALISAR MALAMAN
AFRIKA GAME DA BARAZANAR DA
‘YAN UWANMU MUSULMI NA AFRIKA
TA TSAKIYA SUKE FUSKANTA
Kwanan Wata:
13/4/1435H wanda ya yi daidai da
13/2/2014M
Halin Da Musulmi Suke Ciki A Afrika
Ta Tsakiya
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin
talikai. Tsira da aminci su tabbata ga
annabin rahama da shiriya,
Muhammadu dan Abdullahi, da
iyalansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka,
Babu shakkan malamai a wannan
majalisa sun bibiyi labarin abin da ke
faruwa game da ‘yan uwanmu na
yankin Afrika ta Tsakiya a cikin
damuwa kuma sun lura da abubuwa
kamar haka:
1. Akwai wani yunkuri na halaka
al’ummar musulmin kasar a daidai
lokacin da duniya ta sa ido tana
kallo. Abin da ke faruwa a kasar a
halin yanzu ya yi kama da abin da ya
faru a can baya na kisan kiyashi
wanda ‘yan kabilar Tutsi suka
fuskanta a kasar Ruwanda, wanda
yake abin kunya ne a cikin tarihin
‘yan adam da ba a mantawa.
2. Matakan rashin imani da ake
dauka a kan musulmi a kasar sun
hada da kakkatse naman jikin su
bayan an kashe su, da kona su da
ransu a tsakiyar gari kuma masu
daukar hoto suna dauka. Mata da
kananan yara ba su tsira daga azaba
ba. Don haka ya zama dole a tashi
tsaye a riski wadannan yan ta’adda a
gurfanar da su gaban shari’a.
3. Daga cikin abin da ya taimaki
wadannan ‘yan ta’adda a kan wannan
rashin imani da suke yi ma musulmi
har da goyon bayan sojojin Faransa
wadanda suka je da sunan kwantar
da tarzoma da kwace makamai amma
sai suka koma bangare guda.
4. Matsayin da shugabannin addini
na musulmi da na kirista a kasar
suka dauka na neman zaman lafiya
ba a mutunta shi ba. Saboda
wadannan ‘yan ta’adda babu imani
babu tausayi ko dan kadan a cikin
zukatansu.
5. Kungiyar hada kan kasashen Afrika
(AU) ta yi zugum tana kallon abin da
ke faruwa ba tare da ta motsa ko kare
ba. Haka ma sauran kungiyoyi masu
wakiltar al’ummar duniya sun sa ido
suna kallon wannan bala’i da yake
faruwa ga musulmi kamar irin wanda
ya taba faruwa a kasar Ruwanda duk
a cikin nahiya guda; ita ce Afrika.
6. A halin da ake ciki idan ba a
gaggauta daukar mataki ba akwai
alamun barkewar yakin basasa mai
alaka da addini a wannan nahiya
wadda ta sha ganin bala’oi iri-iri a
can baya.
Saboda irin mummunan hatsarin da
wannan yanayi yake dauke da shi,
wannan majalisa na kira da babbar
murya ga al’ummar kasa da kasa da
dukkan kungiyoyi da wadanda suke
rike da madafan iko da su gaggauta
aika sojojin da za su tsayar da
wannan abin kunya, su samar da
zaman lafiya ga ‘yan kasar ga baki
daya na kowace kabila da kowane
addini.
Kuma wannan majalisa tana neman
al’ummar musulmi da yin abubuwa
guda biyu:
1. A kebe hudubobi a masallatan
jum’ah na Afrika gaba daya da sauran
duniya a kan wannan matsala a ranar
jum’ah mai zuwa 21 ga R. Thani
1435H (21/2/2014M) don a wayar
da kan jama’a game da abin da ke
faruwa a Afrika ta tsakiya don
tausaya ma ‘yan uwanmu musulmi da
abin ya shafa da kuma yi masu
addu’a ko Allah na sa a samu aminci
da zaman lafiya a kasar.
2. A gaggauta tara kudade da abinci
da magani don tallafa ma wadanda
abin ya shafa a can cikin kasar da
wadanda suka yo gudun hijira zuwa
kasashen Tchadi da Kamaru da
Kongo na kowa ce irin kabila da
mabiyan kowane addini a matsayin
su na ‘yan adam.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga
annabinmu Muhammad da iyalansa
da sahabbansa baki daya.
Sa hannu
Dr. Sa’id Muhammad Baba Sila
(Shugaban Majalisa)
Da
Dr. Sa’id Burhan
(Babban Sakatare)
BP/P.O.BOX: E525 Tel: (+223)
20790759/76323061 BAMAKO, MALI
Email: [email protected]
www.africanulama.org Fassara Daga
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim
Memba a wannan majalisa
Sauran membobin wannan majalisa a
Nigeria sun hada da:
– Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
– Sheikh Muhammad Sulaiman jos
– Sheikh Salisu Gumel
– Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu
– Dr. Abdurrazaq Alaro (Ibadan)
– Dr. Aminuddin Abubakar
– Dr. Bashir Ali Umar
– Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates