Cukurkuɗaɗɗun takardu 4 (Shawara ce)

By Hamza Diso

A tunani ka zamo critical thinker, a mu’amala ka zamo Idealist a hukunci ka zamo realistic, idan ka sake Idealism ya lulluɓe tunaninka; to zaka iya zama mutumin kirki, amma ba zaka fahimci abubuwa dayawa a yadda suke ba, za a dinga samun tazara tsakanin tunaninka da yadda rayuwa take tafiya.

Haka idan ya zama cikin hukuncinka akwai wuce gona da iri a critism to babu wanda zai maka daidai, idan kuma ka zabga Idealism a cikin hukuncinka to nan ma zaka ga ba daidai ba.

Komai kyawun tunani ba zai zamo karɓaɓɓe ba sai idan zai yiwu ayi aiki dashi, kasan ƙissar ɓera mai hikima? wanda yace:

hanyar da za a bi a hana mage yi mana ɗauki ɗaiɗai shine a rataya mata ƙararrawa a wuya, ta yadda tana tahowa zamu ji ƙara mu samfe,”

tunaninsa mai kyau ne, to amma inda gizon yake saƙa shine, wa za a samu yaje ya rataya mata ƙararrawar? Ya za ayi a rataya ba ta gane ba? Ya za ayi a rataya kuma ta kasa cirewa? ….. duk bar wannan ma waye zai je ya rataya mata??? A rayuwarmu muna da hikimomi dayawa irin na wancan ɓeran.

A siyasa ka fara zama ɗan Adam tukunna kafin ka zama ɗan jam’iyya, ka da ka dinga ƙirƙirar ƙarya kawai don ɓata abokin adawa, ka da ka zama mara adalci, ka rufe idonka akan duk alkhairan wasu, a lokaci guda kuma baka ganin naku kusakuran, yin ƙarya da yin rashin adalci mummunan abune a addini da kuma kyakkyawan tunani.

Ni yanzu ka ga na daɗe da ƙulla alaƙa da mai ayabar bakin titi, amma haka bazai sa nayiwa mutanan kirkin da ba sa cin ayaba mummunar fahimta ba.

Siyasa wasa ne tsaftatacce sai dai idan ka munana tunaninka, zafafa ƙiyayya a siyasa kuskure ne, babu wata jam’iyya ta mutanan kirki zalla ko ta mutanan banza zalla, mu (a kasar nan) jam’iyyunmu ba a taɓa tafiyar da su akan wata manufa sananniya, kowa da manufarsa yake zuwa, ta wannan fuskar babu banbanci tsakanin Tsintsiya da Lema da mutanan mu .

Wannan ya sa yau kana wannan jam’iyyar gobe kana waccan, kuma hakan ba laifi ba ne, tun da dama duk jam’iyyun basu da tsayayyiyar manufa, idan an matsa maka a can sai ka matsa ka basu guri.

Na sha faɗin cewar zamu iya siyasa ba tare da tsinuwa ko zagi ko ƙazafi ba, zaka iya sukar duk wanda ka ga dama cikin ƴan siyasarmu ba tare da kayi masa ƙarya ba.

Sannan za ka iya yiwa jam’iyyarku propaganda ba tare da kayi ƙarya ba, misali; zaka iya cewa:

Mu a Kano ai hankalinmu kwance yake ranar zaɓe, tun da Mila road ta haɗe da munduɓawa, kasan kuwa mun fi kowa jama’a, indai dangwalawa za ayi

Wannan 👆🏽misali ne kawai.

Allah ya tashe mu lafiya

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: