Cukurkuɗaɗɗun takardu (bayanai daga Zuciya) (1)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

By Hamza Diso

Bin Mazhaba hanyace tsararriya ta gina fiƙhu tun daga babu har zuwa matakin mallakar malaka, wato fiƙihu ya zamo maka tamkar numfashin da kake shaƙa. Bin Mazhaba baya nufin watsi da dalilin da ya bayyana ga mutum cewar shine rajihi, sam, mafi yawan manyan malamai da ka sani duk suna da mazhaba, kuma idan dalili ya bayyana ƙarara a gabansu suka ga wata mazhabar tafi tasu a wata mas’ala suna ajiye tasu su bi waccen.

Misali mu a malikiyya zaka ga irin haka a fili a wajen Alƙali Ibnul Arabiy, Alƙali Iyal, babban Shehi Ibnul Abdulbar da sauransu.

Ita mazhaba da kake gani ilimi ne a tsare wanda zai hana ka ruɗewa a matakin karatunka, ya kuma yi riƙo da hannunka sannu a hankali har idonka ya buɗe tun daga kan matakin Mukhtasaratu ƙanana har zuwa kan babban mukhtasar, sannan littattafan da suka ƙunshi dalilai sannan litattafan saɓani na cikin gida sannan saɓani tsakanin mazhabobi.

Kasan ba zai yiwu ace maka kaje ka dinga amfani da ƙwarewarka wajen ciro hukunce hukunce daga dalilai ba, saboda haka kake bukatar wani tsari da za ka bi.

Sannan su dalilai na Shari’a waɗanda ake ciro hukunce hukunce a cikinsu sun wuce guda goma (10), kowanne mujtahidi yana da Usul da yake dogara dasu wajen ciro hukunci, kuma akan waɗannan Usul mabiyan sa suke ci gaba da ciro hukunce hukunce, sannan akwai masa’il dayawa a babin dalalatul Alfaz da abinda suke hukuntarwa waɗanda suna da tasiri a wajen fahimtar nassi da ma wasu abwab dayawa a Usulul fiƙh, kafin ka ƙware a waɗannan abubuwa ka fahimci saɓanin da yake cikinsu har ka rinjayar da abinda kake ganin rajihi, kafin kayi duk wannan ba zaka iya dinga ciro hukunce hukunce da kanka ba. Sannan ilimin mukhtaliful Hadith, a’a ba shi ba, ilimin mushkilul Aathar,( gini akan cewar wannan ilimin na biyu yafi faɗi sama da na farko, don ya shafi duk dalilai da suka ci karo da juna har ma da Hadisin da ma’anar sa bata fito fili ba,) nace, sanin wannan ilimin sharaɗi ne kafin ka fara ciro hukunce hukunce a cikin duk hadisin da yazo gabanka, ka da nayi nisa a maganar, kawai dai kana bukatar cikakken malami da zai riƙo da hannunka, shi wannan malamin idan kayi riƙo da maganganunsa duka to ka mai dashi mazhabarka, kuma dai kasan ba zai yiwu ya iya samar maka da cikakken tsarin irin na mazhabar da ɗaruruwan malamai suka yiwa hidima ba Wannan batun nawa baya nufin cewa a rufe ido a karɓi komai har wanda dalili na zahiri yaci karo da shi, kawai dai nace maka kana bukatar tsari ne kafin ka zama faƙihi. Ni yanzu ba na ganin istizhari a gurin mai al’ada, haka ina ganin ya kamata a karanta bisimillah a Farillah, kuma barin Alƙunut yafi, sannan ba a lissafin shekara a dukiyar kasuwanci har sai ta cika nisabi…… Da mas’aloli dayawa .. amma duk da haka ni bamalike ne.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories