Mai Rubutu: Hamza Diso
Ana yiwa hadisi hukunci ne ta hanya biyu;
ko dai ka yi hukuncin da kanka, kuma ka naƙalto hukuncin a wajen waninka, idan naƙalto hukunci zakayi to akwai littattafai da ake amfani dasu dayawa.
Da farko dai idan hadisin ka yana cikin Sahihaini to babu magana akansu, don duk ingantattu ne, haka ma duk wani hadisi mausuli a cikin Muwaɗɗa, sai dan abu kaɗan da wasu suka ɗan taɓa, haka sahih ibnu Hibban da Ibnu Khuzaima, ka da ka ce min suna da tasahuli don a rajihi tasasulunsu a babi biyu yake
- Haɗewa tsakanin hadisi Hassan da Sahihi
- Sahhaha hadisin rawi majhul, amma dai mafi yawan abinda suka inganta tabbatacce ne, sai dai idan ka ga wani cikin malamai yayi musu naƙadi, akwai magana dayawa akan waɗannan littattafai amma ba yanzu ba.
Haka Mustadrak na Hakim tare da lura da maganganun Zahabi, da kuma littattafan da sukayiwa Sahihaini Takhriji, kamar littafin Abu Awana da Isma’iliy…. Shima littafin Tirmizi zaka samu yana yiwa hadisan sa hukunci, a haƙiƙa akwai maganganu dayawa akan batun tasahul na Tirmizi, wani lokacin yana yiwa hadisi hukunci ne da Shawahid ɗinsa, ba iya hadisin kawai ya kalla ba, akwai hadisan da lallai zakaga ya kamata ayi masa naƙadi, sai dai dama kasan ai cika ta Allah ce shi kaɗai, sai kuma littafinsa. Assunan (ƙarami) na Nasa’i (Almujtabaa/Almujtanaa) yana da sauƙin hadisai masu rauni sosai kuwa, shiyasa wasu cikin malaman mu suke ganin a inganci da ga Muslim sai shi, kuma littafi ne mai fa’ida kwarai a babin Ilimin Ilalul Hadis, shima Abu Dawud yana raunata hadisan da rauninsu yayi muni sosai a mafi yawan lokuta, amma waɗanda yayi shiru akansu suma akwai masu rauni dayawa, ba wannan ce maganar mu ba dai a yanzu. Hadisan da suke cikin Musnad na Imamu Ahmad da kuma Musnad Na Bazzar da kuma Littattafan Ɗabarani duk zaka sami hukuncin su a cikin Majma’u na Alhaithami. Sannan ko wanne fanni akwai inda ake samun hadisansa, kamar fannin gyaran zuciya, ka tafi Almugni na Iraƙiy ko Attargibu wattarhib… Amma hadisan Fiƙhu idan kana son hukunci a kansu to Kabi littattafan da sukayiwa manyan littattafan fiƙhu Takhriji, a sahun farko ka dakko نصب الراية na Imam Azzaila’i wanda takhriji ne na hadisan Alhidaya na malam Almarginani. Wannan littafin na Azzaila’i ya tattare kusan duk hadisan Fiƙhu, da farko ya fara da hadisan Hanafawa sannan yabi bayansu da na hadisan da sauran mazhabobi suke kafa hujja dasu, kuma a lokuta dayawa yana yiwa hadisan hukunci cikin adalci da kwarewa, kuma zaka sami hadisin da kake nema cikin sauƙi don kawai zaka babin da yake da alaƙa da hadisinka, sannan akwai fa’idoji a cikin littafin sosai ga mai koyon ilimin hadisi da takhriji da yin hukunci akan maruwaici, duba hadisin الأذنان من الرأس kaga yadda yayiwa hadisin hukunci kuma yayi raddi ga masu raunata hadisin kuma kaga yadda ya rinjayar da tausiƙin شهر بن حوشب Haka littafin Ibnu hajar mai suna الدراية wanda talkhisi ne na littafin Zaila’i tare da yin ƙari a gurare dayawa. Da sauran littattafan takhriji na fiƙhu waɗanda suna da yawa har kazo kan littafin إرواء الغليل wanda shima babban kundi ne a wannan babin. Muma a Malikance akwai rubuce rubuce da akayi nayin takhrijin hadisan mu na Malikawa, kamar littafin da Dr Aɗɗahir Muhammad Addardiri ya rubuta na takhrijin hadisan Mudawwana, da ma sauran su. Littattafai a wannan babin suna da yawa, waɗannan da na faɗi a taƙaice ne.Shin zan iya samun duk abinda nake biɗa na hadisan fiƙhu da suke da alaƙa da mas’ala guda a guri ɗaya?Kwarai da gaske, mu haɗu a rubutu na gaba
Leave a Reply