DA WAYE YA DACE KAYI ABOKANTA? KUMA A WANI MAJALISA YA DACE KA ZAUNA?
Da yawa daga cikinmu sun haddace suratul kahfi, toh amma da yawa basu tsayawa suyi tunani kan karen Da Allah ya ambaceshi cikin wannan surah, da kuma meye dalilin da yasa ya sami wannan matsayi mai girma haka? Amsa itace ya sameta ne sabida kasancewarsa tare da mutanen kirki, aduk lokacin daka lazumci mutanen kirki, toh alherin da suke tattare dashi sai ya shafeka, haka kuma aduk lokacin da ka lazumci mutanen banza, to laifinsu da halakansu sai ta shafeka. Haka majalisa. Kada ka yadda ka lazumci majalisar barna, domin A karshe kaima sai ka zama daga cikinsu… Allah(subhanahu wata’ala) yace:
ﻭﺇﺫﺍ ﺭﺃﻳﺖ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺨﻮﺿﻮﻥ ﻓﻲ ﺁﻳﺎﺗﻨﺎ ﻓﺄﻋﺮﺽ
ﻋﻨﻬﻢ ﺣﺘﻰ ﻳﺨﻮﺿﻮﺍ ﻓﻲ ﺣﺪﻳﺚ ﻏﻴﺮﻩ ﻭﺇﻣﺎ
ﻳﻨﺴﻴﻨﻚ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻓﻠﺎ ﺗﻘﻌﺪ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺬﻛﺮﻯ ﻣﻊ ﺍﻟﻘﻮﻡ
ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ.
Kuma idan kã ga waɗanda suke
kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to,
ka bijire daga gare su, sai sun
kũtsa a cikin wani lãbãri
waninsa. Kuma imma dai
shaiɗan lalle ya mantar da kai,
to, kada ka zauna a bayan
tunãwa tãre da mutãne
azzãlumai.
ALLAH KAREMU ALLAH BAMU IKON KIYAYEWA..
Leave a Reply