Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ƙai.
Lahiya Sunnah ce mai ƙarfi ga wanda Allah ya bashi iko.
Da wasu irin dabbobi ake yin lahiya?
Ana yin lahiya ne da dabbobin gida, Raƙumi, Shanu, Tumaki.
Shekarun dabbobi da akeyin lahiya dasu:
Kafin ayanka dabba a matsayin Lahiya dole sai ya cika wa’innan watanni ko shekaru.
- Raƙumi: sai ya cika shekaru biyar
- Shanu: sai ya cika shekaru biyu
- Akuya: sai ta cika shekara guda
- Rago: sai ya cika watanni shida
illolin da suke hana ayi lahiya da dabba
Dabbar da za’ayi lahiya da ita dole ta zamto ta kubuta daga illoli.
kada ta zamto mai ido daya, ko gurguwa ko mara lafiya wanda rashin lafiyan yaci jikinta sosai.
amma kaman jin ciwo kadan wannan baya hana ayi lahiya da dabba, hakanan rashin lafiya wanda bashi da tsanani, wannan shima baya hana ayi lahiya da dabba.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply