DARASI NA BAKWAI (7)
Bismillahir Rahmanir Rahim
Cigaba da karatun littafin mu na
“SHUBUHOHIN SHI’A A
MAHANGAR SHARI’A” na Hamza
Uba Abubakar Kabawa,
gabatarwar Muhammad Aminu
Ibrahim Daurawa.
Duba da korafi da muke samu
daga dalibai game da yawan da
rubutun yake yi, muka gay a dace
idan darasi mai tsayi ne mu rika
rabashi gida biyu ko gwargwadon
yanda hali ya kama.
Yau zamu tashi : –
SHUBUHOHIN SHI’A A KAN
GADON NANA FADIMA (R.A) DA
WARWARE SU A BISA
FAHIMTAR MALAMAI NA
KWARAI.
Shubuha ta hudu da ‘Yan Shi’a
mai limamai goma sha biyu suke
yadawa domin su soki Sahabbai
ita ce: – Sayyadina Abubakar da
Sayyadina Umar (R.A) sun hana
Nana Fadima (R.A) gadonta na
gona. Suna yada haka ne don
karyatawarsu da fadin Manzon
Allah (S.A.W) cewa “Mu Annabawa
ba a gadarmu duk abin da muka
bari na dukiya sadaka ne ga
al’umma baki daya”
Sai ‘Yan Shi’a su ce wannan
hadisin da Sayyadina Abubakar
(R.A) ya kafa hujja da shi wajan
hana Nana Fadima (R.A) gadonta
ya ci karo da fadin Ubanjigi
(S.W.T), “Mazaje Suna da kaso na
gado a cikin abin da iyayensu da
‘yan uwansu suka bari, haka ma
mataye suna da gado cikin abin da
iyayensu suka bari ko ‘yan uwansu
wannan abin kadan ne ko mai
yawa” .
Da kuma fadin Ubangiji (S.W.T)
“Kuma Annabi Sulaiman (A.S) ya
gaji mahaifinsa Annabi Dauda
(A.S)”
Sannan ‘Yan Shi’a sukan kara da
cewa Annabi Zakariyya (A.S) ya yi
Addu’ar Allah ya ba shi dan da zai
gaje shi .
Da a ce ba’a gadar Annabawa da
Annabi Zakariyya (A.S) bai yi
addu’ar Allah ya bashi dan da zai
gaje shi ba.
Jawabi a kan wannan shubuha shi
ne ta fuskoki kamar haka: –
1-Fadin Manzon Allah (S.A.W.)
“Mu Annabawa ba’a gadarmu duk
abin da muka bari na dukiya
sadaka ne ga al’umma baki daya”
Hadisi ne ingantacce kuma ba
Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) ne kadai suka rawaito
wannan Hadisin ba. Bari ma dai,
akwai Sahabbai masu yawa da
suka rawaito Hadisin, har daga
Ahlu Al-baiti kamar Sayyadina Ali
da Abbas dan Abdu Al-Muddalib
(R.A) da matayen Manzon Allah
(S.A.W.).
Wannan ne yasa duk cikin
Sahabbai da Ahlu Al-baiti babu
wanda ya ce: Manzon Allah
(S.A.W.) bai fadi wannan maganar
ba. Hasali ma lokacin da
Sayyadina Abubakar (R.A) ya
fadawa Nana Fadima (R.A) ba ta
kore cewa, Manzon Allah (S.A.W.)
ya fadi wannan magana ba.
2-Ba Nana Fadima (R.A) ce kadai
take da gadon Manzon Allah
(S.A.W) ba. Bayan ita akwai
magadansa kamar Matansa da
amminsa Abbas dan Abdu Al-
Muddalib a haduwar dukkan
malamai, kuma suma ba’a ba su
nasu gadon ba.
Tambaya a nan ita ce me yasa
‘Yan Shi’a basa kawo maganar
cewa Sayyadina Abubakar da
Umar (R.A) sun hana matayen
Manzon Allah (S.A.W) da amminsa
gadonsu, ciki kuwa har da Nana
Aisha ‘yar Sayyadina Abubakar da
kuma Nana Hafsa ‘yar Sayyadina
Umar (R.A), ko su ba su da hakki
ne?
3-Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) sun sarrafa dukiyar da
Manzon Allah (S.A.W) ya bari ne a
tsarin da Manzon Allah (S.A.W)
yake sarrafa ta, ba su amfana da
komai daga cikin dukiyar ba.
Sannan kuma daga baya
Sayyadina Umar (R.A) ya mika
ragamar dukiyar baki daya ga
Sayyadina Ali da Abbas dan Abdu
Al-Muddalib (R.A) bisa sharadin
zasu gudanar da ita kamar yadda
Manzon Allah (S.A.W) yake
gudanar da ita
Ita dai wannan dukiyar da Manzon
Allah (S.A.W) ya bari, daga baya ta
koma karkashin kulawar Hasan
dan Ali dan Abi Dalib, sannan ta
koma hannun Husaini dan Ali (R.A)
, sannan ta dawo hannun Aliyu dan
Husaini (Zainul-Abidina) da Hasan
dan Hasan dan Ali dan Abi Dalib
(R.A), sannan ta koma hannun
Zaid dan Hasan (R.A). Kuma duk
cikinsu babu wanda ya raba
wannan dukiyar da sunan gado.
Tambaya a nan ita ce menene
hukuncin wadannan jagororin na
Ahlu Al-Baiti da suka ki raba gadon
wannan dukiyar, shin suma
azzalumai ne ko ko takiyya suka yi
ko kuwa ya ya lamarin yake?
4- Babu wani daga cikin magadan
Manzon Allah (S.A.W) da ya saba
da Sayyadina Abubakar ko Umar
(R.A) kan sha’anin sarrafa wannan
dukiyar, saboda yadda suka
sarrafa ta a fili yake ga kowa.
Sabanin Sayyadina Ali (R.A) da
suka samu rashin fahimta
tsakaninsa da Abbas dan Abdu Al-
Muddalib (R.A) baffan Manzon
Allah (S.A.W) kan sha’anin sarrafa
wannan dukiya.
5- Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) sun bawa Ahlu Al-baiti dukiya
mai tarin yawa wacce ta ninka
dukiyar da Manzon Allah (S.A.W)
ya bari. Saboda su Ahlu Al-baiti su
ne a matakin farko a tsarin albashi
da kason duk wata dukiya da aka
samu, ta yadda har sun fi
Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) yawan albashi da dukiya a
halin su ne halifofi. Me yasa ‘Yan
Shi’a basa fadar wannan?
6- Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) ba su amfanu da komai ba
daga cikin dukiyar da Manzon
Allah (S.A.W) ya bari. Su dai Ahlu
Al-baiti da ragowar Talakawa da
Miskinai wadanda Manzon Allah
(S.A.W) yake kulawa da su, su ne
suka ci gaba da amfana da ita
kamar yadda ya gabata
7- Sayyadina Ali (R.A) bai raba
gadon wannan dukiya ba har
bayan zamansa Halifa, ya tafiyar
da ita ne, kamar yadda Sayyadina
Abubakar da Umar (R.A) suka
tafiyar da ita.
Me yasa ‘Yan Shi’a basa zarginsa
da kin baiwa Hasan da Husaini
(R.A) gadon Mahaifiyarsu Nana
Fadima (R.A)? Ko shi abin da ya yi
dai-dai ne amma abin da
Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) suka yi zalunci ne bayan duk
irin abu guda suka aikata?
Dangane da maganar da ‘Yan
Shi’a suke yadawa cewa Nana
Fadima (R.A) ba ta sake yiwa
Sayyadina Abubakar (R.A)
magana ba har ta rasu.
Sai mu ce: Maganar wannan
dukiya ce ba ta sake yi masa ba
har ta rasu ba wai magana ta
mu’amala ba. Saboda Hadisin ya
zo ta wata fuskar daga Ma’amar
(R.A) da lafazin “Ba ta sake yiwa
Sayyadina Abubakar (R.A)
maganar wannan dukiyar ba har ta
rasu” Abin da yake dada tabbatar
da hakan shi ne Imamul Baihaki ya
rawaito daga Imam Al-Sha’abiy
cewa “Hakika Sayyadina Abubakar
(R.A) ya je gaishe da Nana Fadima
(R.A). Sai Sayyadina Ali (R.A) ya
ce: da ita ga Sayyadina Abubakar
(R.A) nan yana neman izinin
shigowa gurinki. Sai ta ce idan ka
yarda a bashi dama ya shigo.
Sai Sayyadina Ali (R.A) ya ce: Na
yarda ya shigo. Sai Nana Fadima
(R.A) ta bawa Sayyadina Abubakar
(R.A) izinin shigowa. Bayan ya
shigo gurinta sai ya dinga fada
mata maganganu na kwantar da
hankali har sai da ta nutsu
hankalinta ya kwanta”.
Hafiz Ibn Hajar ya ce: “wannan
Hadisin duk da cewa Mursali ne,
amma isnadinsa ya inganta izuwa
ga Imamu Al-Sha’abiy, kuma da
wannan Hadisin ne, maganar cewa
Nana Fadima (R.A) ta kaura cewa
Sayyadina Abubakar (R.A) ta fito
fili cewa wannan kaura cewar ta
shafi maganar gado ne kawai”
Amma maganar da ‘Yan Shi’a suke
yadawa cewa Nana Fadima (R.A)
ta yiwasiyya ga Sayyadina Ali
(R.A) kada ya gayawa kowa
rasuwarta, ya kuma salla ce ta shi
kadai. Magana ce mara tushe da
asali.
Abin da ya inganta shi ne kamar
yadda ya zo a Sahih Muslim cewa:
– “Lokacin da Nana Fadima (R.A)
ta rasu, sai mijinta Sayyadina Aliyu
(R.A) ya binne ta da daddare ba
tare da ya sanar da Sayyadina
Abubakar (R.A) ba. Sayyadina Ali
(R.A) ya kasance mutane suna
haba-haba da shi, lokacin Nana
Fadima (R.A) ta na da rai. Amma
bayan ta rasu, sai ya fara ganin
canji.
Saboda haka, sai ya nemi
tattaunawa da Sayyadina
Abubakar (R.A), wanda da ma can
bai ma sa mubaya’a a taron jama’a
ba. Sai ya tura yana kiran
Sayyadina Abubakar (R.A) shi
kadai ba tare da kowa ba. Sai
Sayyadina Umar ya ce da
Sayyadina Abubakar lallai bai
kamata ka je gurinsu kai kadai ba.
Sai Sayyadina Abubakar ya ce,
tabbas zan je gurinsu ni kadai
kamar yadda suka nema domin na
san ba zasu cutar da ni ba.
Bayan Sayyadina Abubakar (R.A)
ya je gurinsu, sai Sayyadina Ali
(R.A) ya yi Kalmar Shahada
sannan ya ce: -“Hakika mu mun
san irin falalarka ya Abubakar da
irin girman da Allah ya baka, kuma
ba ma yi maka hassada a kan
alherin da Allah ya baka. Amma sai
dai ka yi mana gaggawa kan
wannan lamari shi yasa muka yi
fushi. Saboda mun kasance muna
ganin muna da hakki a shawarce
mu a kai, duba da kusancinmu da
Manzon Allah (S.A.W). Bai gushe
ba suna tattaunawa da Sayyadina
Abubakar (R.A), har sai da idanun
Sayyadina Abubakar (R.A) suka
zubar da hawaye.
Da Sayyadina Abubakar (R.A) ya
tashi yin magana sai ya ce: – ‘Na
rantse da wanda raina yake
hannunsa, na fi son na kyautatawa
dangin Manzon Allah (S.A.W) fiye
da dangina. Amma Dangane da
abin da ya faru tsakanina daku kan
lamarin wannan dukiya, hakika ni
na tsaya ne a kan gaskiya. Domin
ban bar wani abu da Manzon Allah
(S.A.W) yake aikatawa da wannan
dukiya ba fa ce sai da na aikata.
Sai sayyadina Ali (R.A) ya ce da
Sayyadina Abubakar (R.A): –
Lokacin sallar maraice zan
shelanta yi maka mubaya’a.
Lokacin da Sayyadina Abubakar
(R.A) ya idar da sallar Azahar a
wannan rana, sai ya hau kan
minbari ya yi Kalmar Shahada,
sannan ya sanar da mutane
tattaunawar da suka yi tare da
Sayyadina Ali (R.A) da uzurin da
ya bayar na yin jinkiri wajen
bayyana mubaya’a a fili, sannan ya
nemi gafara ya zauna.
Daga nan sai Sayyadina Ali (R.A)
ya yi Kalmar Shahada, ya bayyana
darajojin Sayyadina Abubakar
(R.A) kuma ya gabatar da
uzurinsa. Sannan ya tabbatar da
cewa ba ya yiwa Sayyadina
Abubakar (R.A) hassada, kuma ba
ya musun irin matsayin da Allah ya
ba shi. Amma dai mun yi fushi ne
saboda muna ganin muna da hakki
na a shawarce mu cikin wannan
lamari amma aka tabbatar ba tare
da an tuntube mu ba, mu kuma
muka ji rashin dadi a matsayin mu
na ‘yan Adam.
Jin wannan magana yasa musulmi
suka yi farin ciki. Sannan suka ce:
‘ka dawo dai-dai kuma ka kyautata.
Sai musulmi suka dada kusantar
Sayyadina Ali (R.A), lokacin da ya
aikata hakan” .
A wannan Hadisin za’a fahimci
abubuwa kamar haka: –
Na daya: – Babu maganar cewa
Nana Fadima (R.A) ta yiwasiyya da
kada a gayawa kowa jana’izarta.
Kamar yadda babu maganar
wasiyyar halifanci ga Sayyadina Ali
(R.A).
Na biyu: – Sayyadina Abubakar
(R.A) ya fi kaunar dangin Manzon
Allah (S.A.W) fiye da danginsa.
Na uku: – Sayyadina Abubakar
(R.A) ya sarrafa dukiyar da
Manzon Allah (S.A.W) ya bari a
tsari na gaskiya kamar yadda
Manzon Allah (S.A.W) yake sarrafa
ta. Domin ya fadi hakan a gaban
Sayyadina Ali (R.A) ba tare da ya
yi masa inkari ba.
Na hudu: – Al’ummar musulmi da
shi kansa Sayyadina Ali (R.A) sun
tabbatar da cewa matsayin da
Sayyadina Ali (R.A) yake a kai na
farko ijitahadi ne wanda ana iya da
cewa ko kuskure.
Na biyar: – Sayyadina Abubakar
(R.A) bai zalunci Ahlu Al-Baiti da
komai ba. Sabanin abin da ‘Yan
Shi’a suke yadawa na karya cewa
ya zalunci Nana Fadima (R.A).
Wani karin jan hankali ga al’umma
shi ne ,’Yan Shi’a ba su tsaya kan
maganar cewa Sayyadina
Abubakar (R.A) ya hana Nana
Fadima gado ba. Bari ma dai sai
da suka kago wani labari na
kanzon kurege da yake nuni da
cewa, Sayyadina Abubakar da
Sayyadina Umar (R.A) sun sa an
yiwa Nana Fadima (R.A) duka har
sai da ta yi bari, kashin
hakarkarinta ya karye. Shi kuwa
Sayyadina Ali (R.A) aka dauro
wuyansa da igiya aka kawo shi ya
yi mubaya’a ta karfi da yaji.
Da sauran irin wadannan kazaman
maganganu marasa dadin ji.
Abu ne sa nanne ga dukkan
al’umma cewa Sayyadina
Abubakar da Umar (R.A), ba su
taba zaluntar wani ko kwa ce masa
hakki ba balantana su zalunci
Nana Fadima (R.A) shugaban
matan talikai, ‘yar shugaban
Annabawa babban abokinsu kuma
babban masoyinsu.
Wannan dan karamin littafi ba zai
isa a kawo irin rayuwa ta adalci da
Tawali’u da tsantseni da gudun-
duniya ta wadannan manyan
Sahabbai guda biyu ba.
Adalcin Sayyadina Umar (R.A) har
ga wanda ba musulmi ba, da irin
yadda ya tsaya tsa yin daka wajen
hana zalunci da kwato hakkin
marasa karfi da kulawa da raunana
da talakawa sa nanne ne,
tabbatacce kuma a fili yake kamar
hasken rana ga al-ummar duniya
baki daya, musulmi da wadanda
ba musulmi ba. Saboda haka a yau
rana tsaka wani ya zo ya ce wai
Sayyadina Umar (R.A) ya zalunci
Nana Fadima (R.A) yasa an doke
ta har sai da ta yi bari, to kamar
yana so ya ce ne rakumi ya fito ta
kofar allura. Wannan kuwa koda
duniyar musulmi sun zama taron
gidan mahaukata babu mai yarda
da wannan magana.
Bugu da kari, idan har abin da ‘Yan
Shi’a suke yadawa dangane da cin
zarafin da aka yiwa Nana Fadima
(R.A) da Sayyadina Ali (R.A) bayan
rasuwar mahaifinta gaskiya ne. Ga
wasu tambayoyi ga ‘Yan Shi’a: –
Ina Sadaukantakar Sayyadina Ali
(R.A) zakin Allah har ya bari aka
yiwa Nana Fadima (R.A) wannan
aika-aika? Sanannen abu ne cewa
mutumin da ya fi kowa ragwanci,
ya kan fi kowa sadaukantaka idan
ya ga za’a taba mutuncin iyalinsa.
Me yasa Sayyadina Ali (R.A.) ya
aurawa Sayyadina Umar (R.A)
Ummu Kulthum ‘yar Nana Fadima
(R.A)?
Shin irin tukuicin da zai sakawa
Sayyadina Umar (R.A.) da shi
kenan na dukan da yasa aka yiwa
Nana Fadima (R.A)?
Ina dangin Manzon Allah (S.A.W)
wato Banu Hashim da Banu Al-
Muddalib suke?
Ina ragowar al’ummar musulmi
cikin masu hijira da Mutanen
Madina suke?
Ina al’ummar musulmi dake zaune
a garuruwa daban-daban suke?
Ina Sahabban da ‘Yan Shi’a suke
riya cewa su kadai ne suke nuna
goyan baya ga Sayyadina Ali (R.A)
irinsu Ammar dan Yasir da Mikdad
dan Aswad suke?
Shin cikin wadannan kashe-kashe
na jama’a babu wanda zai iya
taimakawa Nana Fadima (RA),
koda ta hanyar rawaito kissar ne?
Me yasa wannan kissar bata zamo
sa nanniya ba tare da hadarin
dake cikinta?
Idan’Yan Shi’a suka ce tsoro ne ya
hana dukkan al’ummar Musulmi su
taimake ta.
Sai mu ce: yanzu a hankalce zai
yiwu a ce dukkan Sahabbai, Ahlul-
Albaiti da Musulman da suke
sassan duniya sun hadu a kan kin
taimakon Nana Fadima ?
Yanzu a ce jama’ar da suka yaki
Farisa da Rum suka bude dukkan
garuruwa, suna tsoran Sayyadina
Abubakar da Umar (R.A) har su
kasa taimakawa Nana Fadima
(R.A) shugabar matan duniya,
wacce ta yi saura a cikin ‘ya’ya
Manzon Allah (S.A.W.) ita kadai!
Idan ‘Yan Shi’a suka ce: – Wannan
riwaya ta dukan Nana Fadima
(R.A) ‘Yan Shi’a na farko masu
shige gona da iri su ne suka yarda
da ita, amma ‘Yan Shi’a na yanzu
ba su yarda da ita ba.
Sai mu ce gaskiya ne akwai
manyan malaman Shi’a na yanzu
kamar Husaini Fadlullahi da suke
karyata irin wadancan kazaman
maganganu marasa tushe da asali.
Amma abin mamaki shi ne , a
lokacin da Husain Fadlullah ya
karyata wannan kissar. Sai ga wani
babban malamin Shi’a mai suna
Mujtaba Al-Shairazi ya fito yana
kafirta duk wani wanda bai yarda
da wannan kissar ba. Ciki kuwa
har da Husaini Fadlullah har ta kai
da yana ambatonsa da Husaini
Fadlu Al-Shaidan, ba don komai ba
sai don kawai ya karyata kissar
cewa Sayyadina Abubakar da
Umar (R.A) sun sa an doki Nana
Fadima (R.A) har sai da ta yi bari
kuma wai kashin hakarkarinta ya
karye wa iya Zubillahi.
Na shida: – Sayyadina Ali (R.A) ya
shelanta mubaya’a ga Sayyadina
Abubakar (R.A) ne a taron
al’umma karo na biyu, bayan
mubaya’ar da ya yi masa tun da
farko kamar yadda hadisi ya
tabbata daga Abu Sa’id Al-Khudri
Ya yi hakan ne kuwa don ya kawo
karshen rade-radi da ake yi kan
cewa bai yiwa Sayyadina
Abubakar mubaya’a ba.
Ban da wannan ma, idan yin fushin
Nana Fadima da Sayyadina Ali
(R.A) aibi ne ga sayyadina
Abubakar (R.A). Abu ne sa nanne
cewa wani abu na sabani ya kan
shiga tsakanin Sayyadina Ali (R.A)
da Nana Fadima (R.A) har ta kai
da sun yi fushi kuma sun karya
cewa juna. Kamar yadda hadisi ya
tabbata a Sahihul-Muslim cewa an
samu sabani tsakanin Sayyadina
Ali (R.A) da Nana Fadima (R.A) har
ya yi fushi ya kaura cewa gida.
Kamar kuma yadda lokacin da
Sayyadina Ali (R.A) ya yi yunkurin
auren ‘yar Abu Jahlin, hakan ya
fusata Nana Fadima (R.A) har sai
da ta kai kararsa gurin Manzon
Allah (S.A.W) sannan ya janye
Saboda haka idan fushin Nana
Fadima (R.A) aibi ne ga Sayyadina
Abubakar (R.A), to a nan ma sai ya
zama aibi ga Sayyadina Ali (R.A).
Haka ma idan fushin Sayyadina Ali
(R.A) aibi ne ga Sayyadina
Abubakar (R.A) to a nan ma sai ya
zama aibi ga Nana Fadima (R.A).
Lamarin kuwa duk ba haka yake
ba.
Tare da cewa shi Sayyadina
Abubakar (R.A), sun yi fushi da shi
ne a kan ijitahadi a matsayinsu na
‘yan Adam, kuma abin da suka yi
fushi da Sayyadina Abubakar a
kansa bai shafi Masalaharsa ba.
Amma fushin da suka yi a
tsakaninsu ya shafi Masalahar
junansu ne.
8) Manyan malaman Shi’a kamar
Kulaini a littafinsa “Kafi” da kuma
Imam Al-Dusi a littafinsa “Tahzib”
Sun rawaito hadisi daga Abu
Ja’afar Al-Bakir daga dansa Abu
Abdullah Ja’afar Al-Sadik cewa
mataye basa gadar gidaje ko filaye
ko gonaki.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce me yasa suke tuhumar
Sayyadina Abubakar (R.A) da
cewa ya hana Nana Fadima
gadonta na gona, bayan kuma
abin da ya aikata ya yi dai dai da
hukuncin da aka rawaito daga
limaman Shi’a?
Wata tambayar ita ce shin Nana
Fadima (R.A) bata san da wannan
hukuncin ba ne, ta bukaci gadonta
na gonar da Manzon Allah (S.A.W)
ya bari?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce ta sani.
Sai mu ce me yasa ta je neman
abin da ta san cewa bai halatta a
gare ta ba?
Idan kuma suka ce ba ta sani ba.
Sai mu ce to menene matsayin
wannan hukuncin da aka karbo
daga limamansu cewa ba’a bawa
mata gado na gona?
Ko dai ya zamo abin da Nana
Fadima (R.A) ta aikata shi ne dai-
dai, hukuncin da aka samo daga
limaman Shi’a ya zamo kuskure ko
kuma hukuncin da aka samo daga
limaman Shi’a ya zamo dai-dai
abin da Nana Fadima (R.A) ta
aikata ya zamo kuskure.
Duk ta inda aka juya wannan
maganar ta ruguje tushen akidar
‘Yan Shi’a ta cewa limamansu
Ma’asumai ne basa kuskure.
Dangane da ayoyin da ‘Yan Shi’a
suke kafa hujja da su kan cewa
ana iya gadar Annabawa ta
bangaren dukiya kamar fadin
Ubangiji (S.W.T) “Mazaje suna da
rabo na dukiyar da iyayensu ko
‘yan uwansu suka bari, kamar
yanda mata suke da rabo na
dukiyar da iyayensu ko ‘yan
uwansu suka bari wannan dukiyar
kadan ce ko mai yawa”
Sai mu ce: wannan ayar tana
magana ne kawai a kan dukiyar da
za’a gada, ba ta yi magana a kan
wanda ya kamata a gada da
wadanda ba za’a gada ba.
Abin da yake nuna haka shi ne
dukkan malamai sun hadu a kan
cewa babu gado tsakanin uba
kafiri da da musulmi. Wannan ne
dalilin ma da yasa, Sayyadina Ali
da dan uwansa Ja’afar (R.A) ba su
gaji mahaifinsu Abi Dalib ba.
Wannan hukunci kuwa
tabbataccen abu ne domin har
daga Sayyadina Ali (R.A) an
rawaito hakan kamar yadda ya zo
cikin Bukhari da Muslim.
Dadin dadawa malamai sun
tabbatar da cewa babu gado
tsakanin da mai `yanci da uba
bawa. Hakama babu gado ga
wanda ya kashe mahaifinsa da
gangan don ya gaje shi, ko idan da
da uba suka mutu lokaci guda aka
kasa gane wa ya riga wani
mutuwa.
Don haka, wannan ayar ba ta yi
magana a kan siffar masu cin gado
ba kai tsaye. Bari dai ta yi magana
ne a kan dukiyar da za’a gada idan
sharudan cin gadon sun tabbata.
Kamar yadda Annabta ta ke hana
gado na dukiya. Daga cikin hikimar
rashin gadar Annabawa ta
bangaren dukiya akwai kore musu
tuhumar tarawa ‘ya’yansu abin
duniya.
Kari a kan haka, su Annabawa
iyaye ne ga dukkan al’umma kuma
kaunarsu da fifita su a kan dukkan
komai wajibi ne, don haka sai
dukkan al’umma suka yi tarayya
wajen gadar dukiyarsu, ba tare da
takaituwarta a kan ‘ya’yansu da
‘yan uwansu ba.
Idan `Yan Shi’a suka ce dukkan
wani wanda aka ambata daga cikin
wadanda basa gadar iyayensu ko
‘yan uwansu dalilai ne na shari’a
suka hana gado tsakaninsu.
Sai mu: ce hakama hukuncin
rashin gadar Annabawa ta
bangaren dukiyarsu, dalili na
shari’a ya tabbatar da shi. Kari a
kan hakama shi ne dalilan da suka
ce ba’a gadar Annabawa sun fi
dalilan da suka ce babu gado
tsakanin uba kafiri da da musulmi,
yawa da shuhura da inganci.
10. Dangane da ayar dake cewa
Annabi Sulaiman (A.S) ya gaji
mahaifinsa Annabi Dauda (A.S),
kamar yadda Allah (S.W.T) yake
cewa “Kuma sai Annabi Sulaiman
(A.S) ya gaji mahaifinsa Annabi
Dauda (A.S)”
Sai mu ce wannan ayar ko kadan
ba ta da alaka da gado na dukiya,
bari dai tana magana ne a kan
gado na ilimi da Annabta, kamar
yadda Allah (S.W.T) Yake fada a
farkon kissar cewa “Hakika mun
bawa Annabi Dauda (A.S) da
dansa Annabi Sulaiman (A.S) ilimi”
Abin da yake dada fito da wannan
fili shi ne Annabi Sulaiman (A.S) ba
shi ne kadai dan Annabi Dauda
(A.S) ba. Yana da wasu ‘ya’yan
bayan shi. Sannan kuma ba
‘ya’yansa ne kawai suke da
gadonsa ba, ragowar matansa ma
zasu gaje shi.
Saboda haka, babu wata hikima
kuma babu abin da mutane za su
fahimta, kamar yadda babu wani
yabo ga mutum, idan aka ce ya
gaji dukiyar mahaifinsa. Domin abu
ne da kowa ya yi tarayya a kan
saninsa cewa ‘ya’ya suna gadar
dukiyar mahaifinsu.
Don haka ba zai zamo wani yabo
ga mutum ba, idan aka ce ya gaji
dukiyar mahaifinsa kuma babu
azanci a cikin fadin hakan.
To ta ya ya za’a ce Ubangiji
(S.W.T) wanda yake kammalalle ta
bangaren ilimi da duk siffofi na
kamala, ya turo Mala’ikan da ya fi
ko wane Mala’ika daraja, izuwa ga
Annabin da ya fi kowane Annabi
ilimi da fasaha, a cikin littafin da ya
fi dukkan littattafan da Allah
(S.W.T) ya saukar da irin wannan
magana mara azanci da hikima?
Ashe kenan duk sanda aka ware
wani mutum guda daga cikin
magada, aka ce ya gaji mahaifinsa
to abin da ake nufi shi ne ya gaje
shi ko dai ta bangaren ilimi ko
mulki ko hali ko halitta. Wannan shi
ne abin da kowa ya sani kuma zai
fahimta kai tsaye. Shi yasa Allah
(S.W.T) ya yabi Annabi Dauda da
Annabi Sulaiman (A.S) da ilimi da
hikima kamar a wannan ayar. Haka
kuma ya sake yabonsu a wani
gurin daban da cewa “Hakika
kowanne daga cikinsu mun bashi
hikima da ilimi.”
Wani abu mai muhimmanci da ya
kamata a sani shi ne lafazin gado
ya kan zo a cikin Alkur’ani da
ma’anoni daban-daban, ta yadda
ake iya gane ma’anarsa idan aka
kalli jerin kalmomin da suka gaba
ce shi ko suka biyo bayansa.
Irin wannan hukunci dai wato na
magana a kan gado na ilimi da
Annabta shi Allah yake nufi a cikin
kissar da ya kawo mana ta addu’ar
Annabi Zakariyya (A.S) ta neman
magaji.
Domin babu yadda za a yi a ce
wani Annabi daga cikin
Annabawan Allah ya na rokon
Allah ya ba shi dan da zai gaje
dukiyarsa? Kari a kan haka, shi
Annabi Zakariyya (A.S) bai
shahara da sarrafa dukiya ba,
ballantana a ce har yana yin
addu’ar Allah ya bashi dan da zai
gaje ta. Domin ya tabbata cewa
Annabi Zakariyya (A.S) kafinta ne.
Kuma malamai basa lissafa shi
cikin Annabawan da Allah ya bawa
dukiya.
Wanda duk ya karanta kissar
Annabi Zakariyya (A.S) kai tsaye
zai fahimci cewa yana rokon Allah
ne ya bashi dan da zai gaji
Annabtar gidan Annabi Ya’akub
(A.S). Shi yasa yake cewa a cikin
addu’ar “Allah ya ba ni wanda zai
gaje ni ya kuma gaji Annabtar
gidan Annabi Ya’akub (A.S)”
Domin iyalan Annabi Ya’akub (A.S)
sun yi gado ne na Annabta.
Shi yasa don Allah Ya nuna mana
cewa ya amsa rokon bawansa
Annabi Zakariyya (A.S) sai Ya
bamu labari cewa ya yi masa
bushara da samun da mai suna
Yahya (A.S), kuma ya bashi
Annabta tun yana karami. Kamar
yadda hakan ya zo a cikin Suratul
Maryam da Suratul Anbiya’i da Al-
Imran .
Kari ma a kan abin da ya gabata
shi ne Annabi Yahya (AS) bai
shahara da dukiya ba, abin da ya
shahara da shi, shi ne Zuhudu da
tsantseni da kamewa.
Sannan koda wani gama garin
mutane ba zai zamo abin yabo ba,
idan ya kasance yana addu’ar
Allah ya bashi da don kawai ya
gaje dukiyarsa. Saboda wannan
wani abu ne dake nuni da
siffantuwar mutum da tsabagen
rowa da son kai. Ta ya ya za’a ce
Annabi daga cikin Annabawan
Allah ya siffantu da irin wannan
siffa ta marowata?
Idan ‘Yan Shi’a suka yi da’awar
cewa: Nana Fadima (RA) ba gado
ta nema daga Sayyadina Abubakar
ba. Ta nemi ya bata gonar Fadak
ne wacce Manzon Allah (SAW) ya
bata kyauta.
Sai mu ce, jawabi a kan wannan
da’awar shi ne kamar haka: –
1) Da’awar cewa tana neman gado
ya ci karo da da’awar neman
kyautar da aka bata.
2) Akwai bambanci tsakanin gado
da kyauta da hanyoyin
tabbatuwarsu a shari’ance.
3) Shin Manzon Allah (SAW) ya
bata wannan kyauta ne a rashin
lafiyarsa ta ajali ko ya bata ne tun
da lafiyarsa. Idan ya bata kyautar
ne tun da lafiyarsa, to wannan wani
lamari da ya kamata ya zamo sa
nanne a bayyane ga iyalan
gidansa. Sannan a ka’ida ta shari’a
kyauta bata tabbata sai da shedu
da kuma Hauzi (Wato ya zamo
wanda aka bawa kyautar ya karbe
ta). duk sanda aka rasa daya daga
wadannan har mai kyautar ya rasu,
to wannan dukiya ta zamo gado.
Don haka da’awar cewa Nana
Fadima ta nemi kyautar da aka
bata ne, ya nuna cewa ba’a samu
Hauzi ba.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce: Nana
Fadima ta kawo sheda kan abin da
ta nema.
Sai mu ce Malamai baki daya sun
karyata wannan riwayar, domin
babu wanda ya rawaito ta sai
Buhtari dan Hassan daga Zaid dan
Ali (RA). Shi kuwa ba sa nanne a
gurin malamai ba.
Idan kuwa Manzon Allah (SAW) ya
bata wannan kyauta a rashin
lafiyarsa ta ajali. To sai mu ce
wannan ya ci karo da abin da yake
sa nanne a shari’a cewa: ba’a
zartar da wasiyya ko kyauta ta
mara lafiya ga wani daga cikin
magadansa. Har wasu Malaman
ma suna kirga hakan a matsayin
babban laifi.
Allah (SWT) kuwa ya kare janibin
Manzon Allah (SAW) da iyalan
gidansa su fada cikin irin wannan
aikin.
4) Abin da yake tabbatacce kuma
sa nanne a gurin Malamai shi ne
Nana Fadima (RA) ta nemi
gadonta ne a gurin Sayyadina
Abubakar (RA) da’awar cewa ta
nemi kyautar da Manzon Allah ya
bata ne, bashi da tushe balle asali,
kuma riwayar da tazo da hakan ta
karya ce.
5) Manzon Allah (SAW) ya hana
kebance magaji da wasiyya a cikin
fadinsa “Babu wasiyya ga magaji
sai idan ragowar magada sun
yarda”
Irin yadda ya hana a ware da daga
cikin ‘ya’ya da wata kyauta ta
daban.
6) Shaikhul Islam ya hakaito daga
Abul Abbas bn Suraiji cikin raddin
da ya yiwa Isa dan Abban a kan
mas’alar rantsuwa da sheda….
“Amma Hadisin Buhtari dan
Hassan daga Zaid dan Aliyu cewa
Nana Fadima ta fadawa Sayyadina
Abubakar cewa: Manzon Allah
(SAW) ya bata gonar ‘Fadak’ kuma
wai har ta kawo shedar mutum
daya da ma ce daya wato
Sayyadina Ali da Ummu Aiman….”
Subhanallah mamakin wannan
riwayar ya isa. Abin da Nana
Faima ta nema daga gurin
Sayyadina Abubakar shi ne
gadonta, shi kuma ya fada mata
abin da ya ji daga ma’aikin Allah
(SAW) cewa: “Annabawa ba’a
gadonsu” ba a hakaito cikin wani
Hadisi ba cewa Nana Fadima ta
nemi kyautar da aka ba ta ba. Ko a
rawaito cewa wani ya yiwa mata
sheda a kan haka.
Hakika an rawaito daga Umar dan
Abdul’aziz cewa “Nana Fadima ta
nemi Manzon Allah (SAW) ya bata
“Gonar Fadak” amma bai bata ba”
Kuma Manzon Allah (SAW) ya
kasance yana ciyar da iyalinsa da
marasa karfi cikin Bani Hashim
yana kuma aurar da marasa Aure
cikinsu daga wannan dukiyar,
iyaka rayuwarsa” har inda yake
cewa: Na sa ku zamo sheda na
mayar da ita a kan tsarin da take a
lokacin Manzon Allah (SAW).”
Babu wani Hadisi tabbatacce
ingantacce da aka samu cewa
Nana Fadima ta yi da’awar an bata
Fadak ko wani ya yi mata sheda a
kan haka. Da kuwa da Hadisin to
da malamai sun hakaito shi.
Domin abin ya shafi neman hakki,
kuma abu ne a bayyane da al-
umma suka tattauna a kansa. Babu
wani cikin al’ummar musulmi da ya
yi da’awar cewa ya ji Manzon Allah
(SAW) ya bawa Nana Fadima
gonar Fadak, kuma babu wani
wanda ya ce ya ji Nana Fadima ta
yi da’awar hakan.
Sai wani wai shi Buhtari dan
Hassan ya zo rana tsaka yana
hakaito hakan daga Zaidu dan Ali.
Wannan maganar ba mu san
asalinta ba, kuma ba mu san daga
inda take ba. Isnadin Fadlu dan
Marzuk daga Buhtari daga Zaid
dan Ali ba ya daga hanyar da
Malamai suka sani. Abin da ya
kamaci mai kawo irin wannan
maganar shi ne ya kame
alkalaminsa daga rubuta ta a cikin
littafi (ko hakaito ta a cikin
maganganun ilimi…”)
Leave a Reply