DARASI NA SHIDA (6) SHUBUHOHIN SHI’A A KAN HADISIN MAYAFI DA WARWARE SU A BISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa

Danna nan domin shiga group na karatu Online

DARASI NA SHIDA (6) Bismillahir
Rahmanir Rahim Kafin mu shiga
karatu ga wata yar sanarwa: –
Muna kara tunatar da jama’ar
wannan zaure namu mai albarka
cewa don Allah (S.W.T) mu daure
mu daina aiko tambaya ta wannan
shafin saboda bamu da cikakken
lokaci na amsa muku su, don haka
muka bada lambobin wayarmu
domin tambaya ko Karin bayani,
lambobin zasu zo a karshen
wannan darasinmu nay au Inshaa
Allahu: – SHUBUHOHIN SHI’A A
KAN HADISIN MAYAFI DA
WARWARE SU A BISA
FAHIMTAR MALAMAI NA
KWARAI. Daga cikin shubuhar da
‘Yan Shi’a masu limamai goma sha
biyu da suke yadawa akwai
Hadisin “Mayafi” wato Hadisin da
aka karbo daga Nana Aisha da
Umma Salama (R.A) cewa, lokacin
da Ayar nan dake cikin sura Ali-
Imran ta sauka wato Fadin
Ubangiji (S.W.T) “Duk wanda ya yi
jayayya da kai dangane da abin da
aka yi maka waha yi bayan dalilai
bayya nannu sun zo maka, to ka
ce: – ku zo mu kirawo ‘ya’yan mu
da ‘ya’yanku, da matayenmu, da
matayenku, da mu kanmu da ku
kanku sannan mu yi addu’a ta
la’anta a kan masu karya”. Sai
Manzon Allah (S.A.W) ya kirawo
Sayyadina Ali da Nana Fadima da
Hasan da Husaini (R.A), ya Lulluba
da mayafi tare da su, sannan ya
ce: “ya Ubangijiwadannan iyalan
gida na ne ka kawar da datti, daga
gare su ka kuma tsarkakesu iyaka
tsarkakewa” . ‘Yan Shi’a masu
Limamai goma sha biyu sukan kafa
hujja da wannan Hadisin cewa,
Sayyadina Aliyu da Nana Fadima
da Hasan da Husaini (R.A), su ne
kadai Ahlu Al-baiti kuma
Ma’asumai ne basa kuskure.
Hujjarsu a nan kamar yadda suke
riyawa ita ce, Allah ya tafi da datti
daga barinsu ya kuma tsarkakesu.
Don haka sun zama Ma’asumai a
riyawar su. Jawabi a kan wannan
Hadisi shi ne , ta fuskoki kamar
haka. 1) Tabbas Sayyadina Aliyu,
Nana Fadima, Hasan da Husaini
Allah ya kara musu yarda, suna
daga cikin mafiya kusanci da
Manzon Allah (S.A.W). Amma ba
su ne kadai Ahlu-Al-Baiti ba a
haduwar Malaman Sunna da Shi’a.
2) Hakika wannan Hadisi ya
inganta in banda wata riwaya da
Imamu Al-Tirmizi ya fitar daga
Umma-Salama (R.A) ta ce:
“Lokacin da Manzon Allah (S.A.W.)
ya Lullube Sayyadina Aliyu da
Fadima da Hasan da Husaini (R.A)
ya karanta wannan ayar ta cikin
suratu Al-Ahzab, sai ni ma (Ummu-
Salama) na ce ya ma’aikin Allah ni
ma ina cikin Ahlu-Al-Baiti? Sai
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “ke
dai ki na cikin Alkhairi. ” Malaman
Hadisi sun tabbatar da cewa
wannan riwaya bata inganta ba.
Saboda a cikin Isnadinsa Hadisin
akwai gibi kamar yadda Ibn Kathir
ya Fada. Riwayar data inganta
daga Umma-Salama ita ce lokacin
da ta tamba yi Manzon Allah
(S.A.W) cewa shin ni ma ina cikin
Ahlu-Al-Baiti? Sai ya ce: “Tabbas
kema ki na cikinsu” . 3) Wa nanan
aya ta cikin Suratu Al-Imran ba
cewa ta yi Manzon Allah (S.A.W.)
ya kira yi dukkan Ahlu Al-Baiti ba.
A, a an umarce shi ne da ya kirawo
wadanda suka samu daga
danginsa. Sai aka da ce a daidai
wannan lokaci Sayyadina Aliyu da
Nana Fadima da Hasan da Husaini
(R.A) su ne iyaka wadanda zai iya
kira. Ba wai don su ne kadai Ahlu-
Al-Baiti ba. Dalili kuwa shi ne
sanannen abu ne cewa bayansu,
akwai wadanda suke da matsayi iri
daya da su ta bangaren nasaba a
gurin Manzon Allah (S.A.W) a
haduwar malamai. Amma a dai-dai
wannan lokacin basa wannan
gurin saboda wasu dalilai. Misali
akwai Ja’afar dan Abu Dalib da
Akilu dan Abi Dalib (R.A) ‘yan
uwan Sayyadina Ali (R.A),
wadanda matsayinsu iri daya ne
da na Sayyadina Ali (R.A) ta
bangaren nasaba a gurin Manzon
Allah (S.A.W). Ita kuwa Nana
Fadima (R.A) akwai ‘yan uwanta
da suke da nasaba iri daya, amma
a dai dai wannan lokacin
dukkanninsu sun rasu ita kadai ce
kawai tai saura. Domin ya tabbata
cewa ‘ya’yan Manzon Allah
(S.A.W.) guda bakwai ne maza uku
wato Alkasim, Abdullahi da Ibrahim
(R.A). Sai kuma mata hudu wato
Zainab, Rukayya, Ummu-Khulsum
da Fadima ‘yar autarsu, Allah ya
kara musu yarda. Hasan da
Husaini (R.A) kuwa suna da ‘yan
uwa da suke ciki daya, wato
Zainab, Ummukulthum wacce
Sayyadina Umar (R.A) ya aura, sai
kuma Muhsin wanda ya rasu yana
karami. Sannan kuma Manzon
Allah (S.A.W) yana da wasu jikokin
ta bangaren ‘ya’yansa Zainab da
Rukayya (R.A) da suka Haifa tare
da Sayyadina Usman (R.A) da Ibn
Abul As (R.A). Kari a kan haka,
akwai Abbas dan Abdu Al-
Muddalib (R.A) wanda shi ya fi
kowa kusanci da Manzon Allah
(S.A.W) bayan ‘ya’yansa amma a
lokacin baya nan. Abin dai da
muke so a gane shi ne – Manzon
Allah (S.A.W.) ya kira yi Sayyadina
Aliyu da Nana Fadima da Hasan
da Husaini (R.A) ne a wannan
lokaci, don su ne kawai wadanda
zai iya kira, ba wai don su ne kadai
Ahlu Al-Baiti ba. Idan ‘yan Shi’a
suka ce to me yasa Manzon Allah
(S.A.W) bai kira yi matansa ba a
halin yana da damar da zai kiraye
su? Sai mu ce jawabi ya gabata a
hadisin Ummu Salma cewa lallai
matansa suna daga cikin Ahlu Al-
Baiti. Amma bai kiraye su bane
saboda ba su da alaka da shi ta
nasaba da jinni, sai ta bangare
auratayya kamar yadda bayani zai
zo nan gaba. Kari a kan haka a
cikin ayar ba’a ce Manzon Allah
(S.A.W) ya kira yi matansa na aure
ba. Kuma Manzon Allah (S.A.W)
ba zai yiwu ya lulluba tare da
Matansa ba a cikin wannan bargo
a halin akwai wadanda ba
muharramansu ba ne a ciki. 4) Ga
wata tambaya ga ‘yan Shi’a:
Menene hukuncin ragowar ‘ya’yan
Manzon Allah (S.A.W) da jikokinsa,
shin su ba AhluAl-baiti ba ne?
Mene ne hukuncin ragowar ‘yan
uwan Sayyadina Ali Ja’afar da
Akilu (R.A)? Menene hukuncin
Nana Khadija (R.A) su ma duk ba
Ahlu Al-baiti ba ne? Idan ‘Yan
Shi’a suka ce suma Ahlu Al-baiti
ne. Sai mu ce to ai suma ba sa
cikin wadanda Manzon Allah
(S.A.W) ya lullube da mayafin, ta
ya ya suka zama Ahlu Al-baiti?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Manzon
Allah (S.A.W) bai kiraye su ba ne.
Saboda galibin su basa nan. Sai
mu ce wannan ya zama martani ga
‘yan Shi’a da suke iya kance
Hasan da Husaini da Sayyadina
Aliyu da Nana Fadima (R.A) a
matsayin Ahlu Al-baiti, ya kuma
nuna tabbacin abin da muka
gabatar cewa Manzon Allah
(S.A.W.) ya kira yi iyaka wadanda
ya samu damar ya kiraya ne a
wannan lokacin, ba wai don su ne
kadai Ahlu Al-baiti ba. Idan ‘Yan
Shi a suka dage kan cewa lallai
iyaka wadanda Manzon Allah
(S.A.W) ya lullube da wannan
mayafin su ne kadai Ahlu Al-baiti.
Sai mu ce me yasa suke kawo
sunayen wasu limamai guda tara
bayan basa daga cikin wadanda
Manzon Allah (S.A.W.) ya lullube
da wannan mayafin? Idan ‘Yan Shi
a suka ce su ragowar limamai
guda tara an ba su hukunci ne irin
na iyayensu, saboda jikokin
Husaini (R.A) ne. Sai mu ce, ai ba
suke nan jikokin Husaini (R.A) ba,
akwai jikokinsa da yawa wadanda
‘Yan Shi’a mai limamai goma sha
biyu ba su yarda da su ba, kamar
Zaidu dan Aliyu dan Hussain da
Ismail dan Muhammad dan Aliyu
dan Husaini Allah ya kara yarda a
garesu. Me yasa ‘Yan Shi’a basa
kawo sunayensu a matsayin
limamai? Kari a kan haka me yasa
‘Yan Shi’a suka dauki wasu daga
cikin jikokin Sayyadina Husaini
(RA), suka yiwatsi da jikokin
Sayyadina Hasan (RA) gaba
daya? Kuma me yasa ‘Yan Shi’a
suka zabi Hasan da Husaini (R.A)
kadai daga cikin ‘ya’yan Sayyadina
Ali (R.A), suka yiwatsi da ragowar,
a halin Sayyadina Ali (R.A) yana
da ‘ya’ya sama da talatin? Shin
ragowar ‘ya’yan nasa ba Ahlu Al-
baiti ba ne? Me yasa ba za‘a ba su
hukunci iri daya dana ‘yan uwansu
ba? Kuma me yasa ‘Yan Shi’a
suke kirga Nana Khadija (R.A)
daga cikin Ahlu Al-baiti bayan ita
ma bata cikin wadanda Manzon
Allah (S.A.W) ya lullube da mayafin
amma basa sanya ragowar matan
Manzon Allah (SAW) a cikin Ahlu-
Albaiti? Idan ‘Yan Shi’a suka ce
saboda ita Nana Khadija (R.A) ta
riga ta rasu ne a wannan lokacin,
kuma dalilai sun tabbatar da
kasantuwar ta cikin Ahlu Al-Baiti.
Sai mu ce kamar yadda dalilai
suka tabbatar da kasantuwar Nana
Khadija (R.A) cikin Ahlu Al-Baiti,
hakama akwai dalilai da suka
tabbatar da sauran Matayen
Manzon Allah (S.A.W) a cikin Ahlu-
Al-Baiti. Wani karin haske ma shi
ne ita wannan ayar ta cikin Suratu
Al-Ahzab wato Fadin Ubangiji
(S.W.T) “kuma ku matayen Manzon
Allah (S.A.W) ku zauna a
gidajenku, idan kuma kun tashi fita
to kada kuyi fita irin ta Jahiliyyar
farko. Ku zamo masu tsayar da
Sallah da bayar da zakka, ku zamo
masu biyayya ga Allah da
Manzonsa. Hakika Ubangiji yana
nufin ya tafiyar muku da datti ne ya
ku Ahlu Al-Baiti ya kuma tsarkake
ku iyaka tsarkakewa” Tana
magana ne baki daya a kan
matayen Manzon Allah (S.A.W),
domin duk inda kalmar Ahlu Al-
baiti ta zo cikin Alkur’ani tana
magana ne a kan mata. Misali
Fadin Mala’iku ga Saratu matar
Annabi Ibrahim (A.S) lokacin da ta
yi mamakin busharar da suka yi
mata ta samun haihuwa. Sai suka
ce da ita “yanzu kya dinga mamaki
da lamarin Ubangiji? Rahamar
Allah da Albarkarsa su tabbata a
gareku ya ku Ahlu Al-Baiti. Hakika
shi Ubangiji abin godewa ne kuma
abin girmamawa” Sannan wanda
ya karanta jerin ayoyin da tsarin su
zai tabbatar da abinda muka fada.
Dadin dadawa malamamai suna
kawo maganganu guda hudu a kan
su waye Ahlu Al-baiti. Amma duk
cikin wadannan maganganun na
malamai babu inda aka takaita
Ahlu Al-baiti da iyaka wadanda
Manzon Allah (S.A.W.) ya lullube
su da mayafi. Ga maganganun
kamar haka: – Ta daya -Wasu
Malamai sun ce Ahlu Al-baiti su ne
wadanda aka haramta musu cin
zakka. Sannan a kai maganganu
uku dangane da ko su waye
wadanda aka haramtawa cin
zakkar. Magana ta daya: –
Wadanda suka ce su ne Banu
Hashim da Banu Al-Muddlib
Magana ta biyu: – Wadanda suka
ce su ne Banu Hashim kawai
Magana ta uku: – Wadanda suka
ce su ne Banu Hashim da abin da
ya yi samansu izuwa Muddalib ka
kan Manzon Allah (S.A.W.),
wannan ya hada da Banu Umayya
da Banu Muddalibi da Banu Naufal
domin su ukun nan mahaifinsu
daya da Hashim ka kan Manzon
Allah (S.A.W.) Ta biyu -Wasu
malaman suka ce: – Ahlu Al- baiti
su ne matayen Manzon Allah
(S.A.W.) da zuriyarsa. Ta uku –
Wasu Malaman suka ce Ahlu Al-
baiti su ne mabiyansa. Ta hudu –
Wasu malaman suke ce Ahlu Al-
baiti su ne masu tsoron Allah cikin
al’ummarsa . A duk cikin
maganganun nan da suka gabata,
magana ta farko da ta biyu su ne
suke da inganci ta bangaren dalili
na Alkur’ani da Hadisai. Wato
masu cewa Ahlu Al-baiti su ne,
Banu Hashim da Banu-Muddalib
da matayen Manzon Allah (S.A.W.)
da zuriyarsa. Amma ‘Yan Shi’a
masu limamai goma sha biyu sai
su kai watsi da dukkan dangin
Manzon Allah (S.A.W.) da
matayensa da zuriyarsa, suka
ware wasu ‘yan tsirari suka ce su
ne kadai Ahlu Al-baiti, tsarkakku
daga datti amma banda ragowar. A
cikin matansa sai suka dauki Nana
Khadija (R.A), suka yiwatsi da
ragowar. A cikin ‘ya’yansa kuma
suka dauki Nana Fadima (R.A),
suka yiwatsi da ragowar. A cikin
‘ya’yan Nana Fadima (R.A) suka
dauki Hasan da Husaini (R.A) suka
yi, watsi da ragowar. A cikin
‘ya’yan Hasan da Husaini (R.A),
sai suka dauki wasu daga ‘ya’yan
Husaini (R.A), suka yiwatsi da
‘ya’yan Hasan (R.A) baki daya A
cikin ‘yan uwan Manzon Allah
(S.A.W) da danginsa kuwa sai
suka dauki Sayyadina Ali (R.A) shi
kadai, suka yiwatsi da ragowar.
Sabanin Ahlu Al-Sunna, da suke
girmama dukkan dangin Manzon
Allah (S.A.W) da matansa da ‘ya
‘yansa da jikokinsa da dukkan
zuriyarsa baki daya, Allah ya kara
musu yarda ba tare da wariya ko
yin watsi da wani daga cikinsu ba.
5) Manzon Allah (SAW) ba cewa
ya yi: “Ya Allah wadannan ne kadai
Ahlu Al-baiti ba. A’a cewa ya yi “Ya
Allah wadannan ma Ahlu Al-baiti
ne” wato abin da yake nuni da shi
shi ne , Sayyadina Aliyu da Nana
Fadima da Hasan da Husaini (R.A)
suma sun shiga fadin ma’anar ayar
nan ta cikin sura Al-Ahzab, don
kada wani yakebance Ahlu Al-Baiti
da iyaka matan Manzon Allah
(S.A.W.). Abin da yake nuna hakan
shi ne Hadisin Zaidu dan Arkam
(R.A) wanda yana daga cikin
hadisan da ‘Yan Shi’a suke takama
da shi, amma sun yi masa
mummunar fahimta. Imamu Muslim
ya rawaito Hadisi daga Zaidu-dan-
Arkam (R.A) ya ce: “Wata rana
Manzon Allah (S.A.W.) ya tashi
yana mai huduba a gindin wani
ruwa da ake kira da suna “Gadir
Khum” tsakanin Makka da Madina.
Sai ya yi godiya ga Allah ya yi yabo
a gare shi. Ya yiwa’azi ya tunasar
da jama’a sannan ya ce: – “Bayan
haka ku saurara ya ku mutane,
hakika ni ma mutun ne ya kusata
dan aiken Ubangiji ya zo min.
Amma ni zan bar muku abubuwa
guda biyu masu matukar
muhimmanci. Na farkonsu shi ne ,
littafin Allah a cikinsa akwai haske
da shiriya, ku yi riko da littafin Allah
kuma ku yi aiki da shi. Ya ja
hankali kan aiki da littafin Allah ya
kuma kwadaitar da mutane,
sannan ya ce: “Da kuma iyalan
gida na. Ina tunasar da ku Allah
Dangane da iyalan gida na”. Sai
Husaini dan Saburata ya ce da
Zaid dan Arkam: “Su waye Ahlu Al-
baitin Manzon Allah (S.A.W.) ya kai
Zaid dan Arkam, shin matayensa
ba su ne kawai Ahlu Al-baiti ba?
Sai Zaid dan Arkam ya ce: –lallai
matayensa Ahlu Al- baiti ne. Amma
bayan su akwai Ahlu Al-baiti da
aka haramta musu cin Zakka. Sai
ya ce su waye? Sai Zaid dan
Arkam ya ce: su ne iyalan
Sayyadina Ali, da iyalan Akilu da
iyalan Ja’afar da iyalan Abbas. Sai
ya ce: – duk wadannan an haramta
musu cin zakka? Sai Zaid ya ce:
na’am” . Don haka wannan Hadisin
ya tabbatar da abin da muka
gabatar cewa, Ahlu Al-baiti su ne
Matan Manzon Allah (S.A.W.) da
‘ya’yansa da danginsa da
zuriyarsu. Dangane da wata
riwayar daga Zaidu dan Arkam
(R.A) dake nuni da cewa matayen
Manzon Allah (S.A.W.) basa cikin
Ahlu-Al-Baiti. Malamai sun bayar
da amsa da cewa Zaidu dan
Arkam Allah ya kara masa yarda
ya bayar da amsa ne gwargwadon
irin tambayar da aka yi masa. A
karon farko an tambaye shi ne
“Shin matayen Manzon Allah
(S.A.W) Suna daga cikin Ahlu Al-
Baiti?” Sai ya bada amsa da cewa
suna cikin Ahlu Al-Baiti. A wani
karon kuma an tambaye shi ne
cewa “Shin matayen Manzon Allah
(S.A.W.) ne kadai Ahlu Al-Baiti?”
Sai ya bayar da amsa da cewa ba
su kadai ne Ahlu Al-Baiti ba. Idan
‘Yan Shi’a suka ce wannan hadisi
na Zaid dan Arkam yana nuni da
cewa matayen Manzon Allah
(S.A.W) ba a haramta musu cin
zakka ba, ashe kenan basa daga
cikin Ahlu Al-Baiti. Sai mu ce
wannan magana ba haka take
ba.Tun da a cikin hadisin akwai
bayani karara dake tabbatar da
cewa matayen Manzon Allah
(S.A.W) suna daga cikin Ahlu Al-
Baiti. Sannan magana mafi inganci
daga cikin maganganun malamai
shi ne , matayen Manzon Allah
(S.A.W.) ma an haramta musu cin
zakka. Idan wani ya ce: to me yasa
ba’a haramtawa barorin
matayensa cin zakka ba, kamar
yadda aka haramtawa barorin
ragowar Ahlu al-baiti? Sai mu ce
an haramtawa barorin ragowar
Ahlu Al-Baiti cin zakka ne, saboda
alakarsu da Manzon Allah (S.A.W.)
ta jini ce da asali. Amma matayen
Manzon Allah (S.A.W.) ba’a
haramtawa barorinsu cin zakka ba,
saboda alakarsu da Manzon Allah
(S.A.W.) ta auratayya ce da reshe.
Kuma bisa ka’ida ana gina reshe
ne a kan asali, ba’a gina reshe a
kan reshe dan uwansa. Wani karin
haske a kan abin da ya gabata shi
ne Manzon Allah (S.A.W.) ya
yiwasiyya ne da a kula masa da
Ahlu Al-baiti, kada a wulakantasu
ko a ci zarafinsu, kamar yadda a
wasu Hadisai ya yi magiya da a
kula masa da Sahabbansa kada a
wulakantasu ko a ci zarafinsu .
Amma ‘Yan Shi’a, ba su da aiki
dare da rana sai cin zarafin
Sahabbai da matayen Manzon
Allah (S.A.W). Har ta kai saboda
tsa nanin gabarsu da kiyayyarsu
ga Sahabbai, har ma wani Lazimi
suke da shi safe da yamma na
la’antar manyan Sahabban
Manzon Allah (S.A.W) wato
Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) da ‘ya’yansu guda biyu wato
Nana Aisha da Hafsa (R.A) da duk
wanda ya goya musu baya a
sha’anin Khalifancinsu . Idan kuwa
haka ne, wannan la’antar da ‘Yan
Shi’a suke yi zata shafi dukkan
Ahlu Al-baiti don kuwa duk cikinsu
babu wanda bai goyawa
Sayyadina Abubakar da Umar
baya ba. Saboda Tarihi cike yake
da bayyana irin gudunmawa da
taimako da shawarwari da
Sayyadina Ali (R.A) ya dinga
bayarwa ga Halifofin nan guda
biyu. Musamman Sayyadina Umar
(R.A). kuma alaka dake tsakaninsu
tasa Sayyadina Ali (R.A) ya
aurawa Sayyadina Umar (R.A)
‘yarsa ta cikinsa: wacce suka haifa
tare da Nana Fadima (R.A) ‘yar
Manzon Allah (S.A.W), wato Ummu
Kulthum. Sannan saboda
kyakykyawan zumunci dake
tsakaninsu sai da Sayyadina Ali
(R.A) ya sanyawa wasu daga cikin
‘ya’yansa suna Abubakar da Umar
da Usman. Bayan wannan kuma
Sayyadina Umar (R.A) ya nada
Sayyadina Ali (R.A) Alkali. Ya
kuma bar masa rikon Halifanci a
Madina lokacin da zai yi tafiyar nan
mai cike da tarihi da abin koyi
izuwa kasar Sham. Saboda yadda
Sayyadina Ali (R.A) yake ganin
girman Sayyadina Umar (R.A) har
sai da ta kai yana cewa “Babu wani
mutum da nake fatan na tsaya a
gaban Allah da irin aikinsa sai
Sayyadina Umar (R.A)” . Shin
Sayyadina Ali (RA) zai yi burin
tsayuwa gaban Allah da aikin
kafiri? Dangane da maganar
ma’asumanci da ‘yan Shi’a suke
ambata karkashin wannan Hadisin
saboda Addu’ar da Manzon Allah
(S.A.W.) ya yi cewa: “Allah ya tafi
da datti ga barin Ahlu Al-baiti ya
kuma tsarkake su” Sai mu tamba yi
‘Yan Shi’a, shin yaushe ne
Limaman Shi’a suka zamo
Ma’asumai , bayan saukar wa
nannan ayar ne ko kafin saukarta?
Idan bayan saukarta ne, ina
da‘awar cewa limamai Ma’asumai
tun suna yara? Idan kuma kafin
saukarta ne, to wannan ayar ba ita
ce ta mayar da su Ma’asumai ba.
Don haka babu hujja a cikin ta.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Allah ya
tsarkake Ahlu-Albaiti kamar yadda
Manzon Allah ya roka musu don
haka Ma’asumai ne. ¬¬¬¬¬ Jawabi
a kan wannan da’awar shi ne ta
fuskoki kamar haka: – 1- Babu wani
guri a cikin wannan Hadisi da ya
nuna cewa Sayyadina Ali da Nana
Fadima da Hasan da Husaini (R.A)
tare da sauran limaman Shi’a
Ma’asumai ne. Saboda ita kalmar
tsarkakewa da kawar da datti basa
nufin ma’asumanci kamar yadda
bayani zai zo nan gaba. 2- Manzon
Allah (S.A.W.) ya yi addu’a ne ta
Allah ya kiyaye masa iyalansa ya
tsare su daga aiki irin na jahiliyya
kamar fita cikin tsaraici, ya sanya
su masu tsayar da Sallah da bayar
da zakka masu yin da’a ga Allah
da Manzonsa. Wanda duk ya
karanta jerin ayoyin zai fahimci
haka. Allah (S.W.T) cewa ya yi “Ya
ku matayen Manzon Allah (S.A.W)
hakika ku ba dai-dai kuke ba da
ragowar mataye, matukar kun ji
tsoron Allah. Don haka kada ku
dinga karairaya sauti don gudun
kada wanda yake da cuta a zuciya
ya yi kwada yinku. Ku dinga fadar
magana sa nanniyya a shari’a,
kuma ku zauna a gidajenku, idan
kun tashi fita kada ku yi fita ta
tsaraici irin ta jahiliyyar farko, ku
tsayar da Sallah, ku bayar da
Zakka ku zamo masu da’a ga Allah
da ManzonSa, Allah ya na nufin ya
tafiyar muku da datti ne, ku iyalan
wannan gida ya kuma tsarkake ku
tsarkakewa” A nan kawar da datti
da tsarkakewa abin da yake nufi a
shi ne abin da ayoyin suka kunsa
na ayyukan jahiliyya, kamar fita a
cikin tsaraici da rashin kamun kai
da kwada yin abin duniya da kawa
ce-kawa centa. 3- Kungiyoyin Shi’a
ba su hadu a kan wani mutum ba,
wanda kowa ya yarda cewa shi
ma’asumi ne. Tun daga kan
Sayyadina Ali (R.A) har izuwa kan
duk wani daga cikin Ahlu Al-Baiti
da ake da’awar cewa shi ma’asumi
ne. 4- Babu wata ingantacciyar
riwaya daga Sayyadina Ali (R.A) ko
wani daga cikin Ahlu Al-baiti da ya
yi da’awar cewa shi ma’asumi ne.
Bari ma dai ayyukansu da
maganganinsu duk suna tabbatar
da cewa su ba Ma’asumai ba ne.
5- An samu riwayoyi da fatawoyi
mabambanta juna daga Ahlu Al-
baiti. Kamar yadda kuma aka samu
cewa suna yin raddi ga juna a kan
mas’aloli masu yawa. Misali: Akwai
Sabanin ra’a yi tsakanin Sayyadina
Hasan da Husaini (R.A) kan da
cewar sallama halifanci ga
Sayyadina Mu’awiya da abu
Sufyan (R.A). Sannan akwai
Sabanin ra’a yi tsakanin Abdullahi
dan Abbas da Sayyadina Ali (R.A)
a kan matsaloli masu yawa. Kamar
lokacin da Sayyadina Ali (R.A) ya
kona wasu mutane da suke
da’awar cewa shi Allah ne. Da
labari ya je kunnen Abdullahi dan
Abbas (R.A) sai ya ce: “Idan ni ne
kashe su zan yi saboda Manzon
Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya bar
addininsa (Muslunci) ku kashe shi.
Kuma ba zan konasu ba saboda
Manzon Allah (S.A.W) ya hana yin
azaba da wuta” . Badan kada
wannan littafi ya tsawaita ba, da
mun kawo misalai masu yawa na
irin wadannan matsaloli. Amma ya
ishi mai karatu ya fahimci cewa
babu wani Ma’asumi bayan
Manzon Allah (S.A.W), idan ya kalli
sabanin dake tsakanin Ahlu Al-baiti
a kan matsaloli daban-daban na
akida da Fikhu da sabanin dake
tsakanin Kungiyoyin Shi’a kan
wanene Ma’sumi, ta yadda kowa
ce Kungiya take da’awar nata
limamin ne Ma’asumi. Ragowar
limaman wata kungiyar ba
Ma’asumai ba ne. 6- Mabiya Shi’a
masu limamai goma sha biyu suna zuzuta
limamansu suna ma ba su
matsayin da yafi na Annabawa
kamar yadda Khomeni yake Fada
a littafinsa Hukuma Islamiyya
cewa: “Dole ne ga mai bin tafarkin
Shi’a ya yarda cewa limamanmu
suna da matsayin da babu wani
Annabi Mursali, ko Mala’ika
makusanci da yake da shi”. Ya
kuma nuna cewa Mahadi shi ne zai
zo, ya tabbatar da adalci da
gaskiya, wanda Annabawan Allah
baki daya, har Manzon Allah
(SAW) suka kasa tabbatarwa.
Tirkashi ashe akidar ‘Yan Shi’a
bata tsaya a kan yarda da limamai
sha biyu Ma’asumai ba kawai, bari
dai har sai mutum ya yarda cewa
wadannan limaman sun fi dukkan
Annabawa da Mala’iku matsayi a
gurin Allah . Sanannen abu ne
kuwa babu wani matsayi da ya fi
na Annabawa a cikin dukkan
halittun Allah. Wata kila yarda da
wannan akidar, yake sa ‘Yan Shi’a
suke siffanta Limamansu da suffofi
irin na Allah. Kai a wani lokacin
ma, su kan nuna cewa limamansu
sun fi Allah. Saboda sukan
danganta kuskure ko jahilci da
rashin sanin ya kamata ko rashin
hikima zuwa ga Allah. Amma ba su
taba danganta wata siffa ta tawaya
ga limamansu ba, dai-dai da
kwayar zarra. Ko a nan mai karatu
zai fahimci cewa ‘Yan Shi’a masu
limamai goma sha biyu, suna kira
ne kawai izuwa imani da Alloli
goma sha biyu, ba wai limamai
goma sha biyu ba. Shi yasa zaka
ga mabiya Shi’a mai limamai goma
sha biyu, da duk wata kungiya da
suka allantar da wani ba Allah ba
daga mabiya Sufanci da Kiristanci
da makamantansu, suna jin farin
ciki da shauki da annushuwa duk
sanda aka ambaci wannan
mutunin, amma basa jin komai
idan an ambaci sunan Allah. Idan
da zaka ce kowa ya kama
limamansu da shehunansu, sai ka
ji sun yi shiru, zuciyarsu na cike da
murna. Amma idan ka ce kowa ya
kama Allah shi kadai, ba tare da
wani ba. Sai kaga sun harzuka sun
cika da fushi hankalinsu ya tashi.
Sai ka ji suna cewa don me za’a ce
a kama Allah shi kadai, ba tare da
an kama kafa da wani ba! Allah
(S.W.T) yana cewa: dangane da
ma’abota irin wannan akidar wato
masu fifita soyayyar wanin Allah a
kan son Allah (S.W.T) “Daga cikin
mutane akwai masu rikon wasu
kishiyoyi koma bayan Allah, suna
kaunarsu kamar yadda suke son
Allah” Ya kuma bamu labarin irin
inkarin da kafirai suke yi ga
Manzon Allah (S.A.W) lokacin da
ya ce: da su. Su kira yi Allah shi
kadai a matsayin abin bauta. Sai
kafirai suka ce: – ‘yanzu ya za a ce
a kama Allah shi kadai, lallai
wannan abu ne mai ban mamaki” .
Hakan ne yasa suka dinga
tuhumar Manzon Allah (S.A.W) da
rashin ganin girman iyayen gijinsu.
Kamar yadda yanzu ake tuhumar
Ahlu Al-sunna da cewa wai basa
son Annabi (S.A.W) ko a ce basa
kaunar Waliyyai da Shehunnai. Ba
don komai ba sai don sun ce a
bautawa Allah (S.W.T) shi kadai,
ba tare da an hadashi da wani ba.
Kuma a yi biyayya ga Manzon
Allah (S.A.W) ba tare da an yi
masa kishiya ba. Abin tambaya a
nan shi ne menene aibi cikin
wannan? Shin Allah (S.W.T) bai
cancanta da a bauta masa ba ne
shi kadai? Ko kuwa mutane suna
so ne ayar dake cikin Suratul-
Zumar ta yi aiki a kansu ne wato
fadin Ubangiji (S.W.T) “Kuma idan
aka ambaci Allah shi kadai sai
kaga zukatan wadanda ba su yi
imani da ranar lahira ba cike da
kunci da rashin jin dadi, amma
idan aka ambaci wani ba Allah ba,
sai ka gansu cikin farin ciki da
annushuwa da murna” . Menene
aibi cikin cewa a yiwa Manzon
Allah (S.A.W) biyayya shi kadai ?
Ashe bautar Allah shi kadai da
biyayya ga AnnabawanSa, ba shi
ne tushen sakon da Annabawa
suka zo da shi ba? 7) Idan addu’ar
da Manzon Allah (S.A.W) ya yi ta
tafiyar da datti ga barin Ahlu Al-
baiti ya kuma tsarkakesu, shi ne
dalilin da yasa ‘Yan Shi’a suke
da’awar cewa limamansu sun
zama Ma’asumai . To me ‘Yan
Shi’a za su ce dangane da tafiyar
da datti da kuma tsarkakewar da
Allah (S.W.T) ya ce: ya yiwa
Sahabbabai a cikin fadinSa “Ku
tuna lokacin da Ubangiji ya lullube
ku da wani irin gyangyadi don ya
sanya muku aminci daga gurinsa
kuma ya saukar da ruwan sama a
gareku, domin ya tsarkake ku da
shi, ya tafiyar muku da dattin
shaidan, sannan ya mamaye
zuciyarku da imani, ya kuma
tabbatar da dugaduganku a kan
imani sakamakon hakan” . A cikin
wannan ayar Allah (S.W.T) ya
tabbatar da cewa ya yiwa
Sahabbabai abubuwa guda hudu
kamar haka: – Na daya Ya ce: ya
tsarkake su. Na biyu Ya tafiyar
musu da dattin shaidan. Na uku Ya
mamaye zuciyarsu da imani. Na
hudu Ya tabbatar da duga-
dugansu a kan musulunci. To me
yasa ‘Yan Shi’a basa cewa da
Sahabbai Ma’asumai ? A
maimakon hakan sai suke
kafirtasu, suke siffantasu da
zalunci da cin amana! Idan ‘Yan
Shi’a suka ce tsarkakewar da Allah
(S.W.T) ya ce: ya yiwa Sahabbai
da dattin da ya ce: ya tafiyar musu
da shi na Zahiri ne. wanda ya yiwa
Ahlu Al-baiti kuwa na ma’ana ne,
shi yasa suka zamo Ma’asumai
sabanin Sahabbai. Sai mu ce ko
alama abin ba haka yake ba.
Saboda abin da ayar ta kunsa ya
karyata wannan fahimtar. Domin a
cikin ayar akwai maganar saukar
da aminci daga Allah da maganar
cika zuciya da imani da maganar
tabbatuwa a kan imani da tafiyar
da dattin shaidan. Wadannan
abubuwa kuwa ba su da alaka da
tsarki na zahiri bari ma dai su ne
hakikanin tsarki na badini. Idan har
ayar dake cikin suratul-Ahzab hujja
ce a kan cewa Ahlu- Albaiti
Ma’asumai ne. To wannan ayar
dake cikin surutu-Al’imran, ya
kamata ta zamo hujja a kan cewa
sahabbai ma Ma’asumai ne. Idan
kuwa wannan ayar ba hujja ba ce.
To waccan ayar ma ba hujja ba ce.
Ko ta ina aka kalli ayoyin guda
biyu, sun ci karo da tushen akidar
Shi’a. Muhammad Aminu Ibrahim
Daurawa 08023742857 Abu
Abdullah Hamza Uba Abubakar
Kabawa. 08028751610
08059517410 08093632636

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “DARASI NA SHIDA (6) SHUBUHOHIN SHI’A A KAN HADISIN MAYAFI DA WARWARE SU A BISA FAHIMTAR MALAMAI NA KWARAI(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa”
  1. muhammad sagir Avatar
    muhammad sagir

    Assalam,idan na fahimci malam kana nufin Abbas Ibn Abi Talib ya fi kusanci da Annabi fiye da Ali Ibn Abi Talib?A kokarin kare sunna bai kamata rage darajar wadanda Allah da manzonsa suka fifita.Sannan hadisan Annabi duk sun fifita wadanda ka yi musu kudin goro da sauran sahabbai ba.Allah Ya sa mu gane.

  2. BILYA TUKUR BAKORI Avatar

    Allah yasaka da Alkhairi

  3. […] Source: DARASI NA SHIDA (6) SHUBUHOHIN SHI’A AKAN HADISIN MAYAFI DAWARWARE SU A BISAFAHIMTAR MALAMAI NAKWA… […]

Leave a Reply to BILYA TUKUR BAKORICancel reply

Latest updates
Categories