Yana daga cikin ruɗani da mutane suke faɗawa da yawa aciki: Mance wa da Allah lokacin da suke neman wani abu. Sai suyi riƙo da sababi kawai ba tare da sun nemi taimakon Allah ba. Hakan sai ya janyo musu:
- Ko su rasa abinda suke nema ɗin kuma su kasa haƙuri akai, Su shiga tashin hankali.
- Ko kuma su sameshi ya zamto musu musiba. Ta yadda zai janyo musu halaka ko kuma ya janyo musu Rashin kwanciyar hankali.
A duk lokacin da kake da buƙatar wani abu toh ka roƙi Allah ya taimaka maka akai. Ya kuma tabbatar maka shi indai alheri ne. Ya kuma kawar maka dashi in ba alheri bane.
A lokacin da ka lazimci haka toh zaka sami sa’adah a rayuwarka.
Inka rasa abinda kake nema zaka samu Allah zai sa maka haƙuri ta yadda hankalinka ba zai tashi akan rasa wa da kayi ba, sannan kuma Allah ya baka wanda yafi shi wannan ɗin alheri.
Ko kuma idan ka sami shi abinda kake so ɗin da taimakon Allah sai Allah ya taimakeka akai, ya sanya shi ya zamto maka farin ciki da kuma kwanciyar hankali.
Shi yasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance yana koyawa Sahabban sa istikhara(Neman zaɓin Allah). Kuma ya dace ko wani musulmi yasan ya akeyinta. Duk wani abu da kakeso kayi, kasuwanci ne, Aure ne, fara wani aiki ne, Sai ka nemi zaɓin Allah. Allah yafi ka sanin abinda yake alheri a gareka. Kuma bazai taɓa tozarta ka ba.
Kada mu dogara da koƙarinmu, a kullum mu dogara da Allah, sai muyi iya ƙoƙarinmu, sai Allah ya dafa mana. Allah yasa mudace.
Leave a Reply