Fadin Kyakkyawa(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Danna nan domin shiga karatu Online

Fadin kalma kyakkyawa ga
mutane, tare da ambaton alheri
garesu, da tausasa magana wata
dabi’a ce kyakkyawa da musulunci
ya umarci mabiyansa da ita. Allah
Madaukakin Sarki a cikin Alkur’ani
mai girma yana cewa “ka cewa
bayina su fadi (kalmar) da tafi
kyau” (Suratul Isra’i) a hadisi
ingantacce Manzon Allah (S.A.W)
ya ce “Musulmi (cikakke) shi ne
wanda musulmi suka kubuta daga
hannunsa da bakinsa”.
Lamarin bai tsaya nan ba, sai da
Alkur’ani ya dora mu akan wannan
dabi’a ta fadin kalma mai kyau a
wurare da dama, kamar wajen
iyaye an hana a ce musu tir, haka
nan wajen mai roko (Mabukaci) an
hana a yi masa tsawa,haka kuma
Allah Madaukakin Sarki ya yabi
bayinsa Muminai da cewa idan
jahilai suka yi musu hauka sai su
ce musu aminci da kwanciyar
hankali (Wato Salama).
Idan mun koma sunnar Manzon
Allah (S.A.W) zamu samu misalai
masu yawa kan irin yadda Manzon
Allah (S.A.W) yake mu’amala da
mutane daban daban, yana fada
musu kyakkyawar kalma, a yayin
da su, suke fada masa mummuna,
ko suka aikata mummuna, kissar
Balaraben kauyen nan da ya yi
fitsari a masallaci, da yadda
Manzon Allah (S.A.W) ya yi masa
mu’amala, ya hana sahabbai su yi
masa tsawa, ya sanya aka barshi
ya gama fitsarinsa, sannan ya yi
umarni aka kawo ruwa guga guda
aka zuba akan fitsarin, sannan ya
karantar da shi abin da ya dace,
babban misali ne a wajen da’awa
da mu’amala da mutane, haka nan
kissar sahabin nan Mu’awiya Ibnul
Hakam Assulamiy wadda imamu
Muslim ya rawaito, yayin da ya yi
magana a cikin sallah, don bai san
an hana ba, sahabbai suka yi ta
kallonsa, sai ya sake cewa
“kaicona, me yasa kuke kallona?”
sai suka rika buga hannayensu
akan cinyoyinsu, suna nuna masa
ya yi shiru, ya ce da aka gama
Sallah, ban taba ganin malamin da
ya fi Manzon Allah (S.A.W) ba,
Wallahi, bai kyare ni ba, bai dokeni
ba, bai yi min tsawa ba, kadai abin
da ya ce min, wannan sallah baya
dacewa a yi maganganun mutane
a cikinta”. Allahu Akbar haka
Manzon Allah yake da’awa cikin
hikima da adalci.
Yan uwa, dole ne idan muna so mu
ci nasara a da’awarmu mu yi koyi
da Manzon Allah (S.A.W) da
sahabbansa da sauran magabata,
mu zama masu hakuri, masu
kyakkyawar magana, masu nasiha.
Zafafa magana da cin mutunci da
batanci, musamman ma ga dan
uwa musulmi a koyaushe, ba tsari
ba ne na da’awa. Allah ya sa mu
gane. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Fadin Kyakkyawa(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
  1. musabimam gombe Avatar
    musabimam gombe

    malam allah yamana sakaiya da gidan aljana,
    tambayana itace,
    kyakkyawan dabi a, da kyakkyawan magana anayiwa wadanda ba musulmaiba?

Leave a Reply

Categories
Latest updates