kame Bakinka(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Hattara Dai! Kar Ka Zama Cikin
Wadannan!!!
Imam Ibnul Kayyim (Allah Ya
Jikansa Da Rahama) Yana cewa
“Abin mamaki, sai ka ga mutum
yana yi masa sauki ya kiyayi cin
haramun, da zalunci, da zina, da
sata da shan giya da kallon
haramun da makamantansu,
amma kiyaye harshensa yana
masa wahala, har sai ka ga
mutumin da ake nuna shi wajen
addini da gudun duniya da ibada,
amma yana fadin kalmar dake
jawo fushin Allah, ba tare da ya
damu ba, kalmar da zata sauko da
shi kasa fiye da nisan da yake
tsakanin gabas da yamma.
Sau da yawa zaka ga mutum mai
tsantseni wajen barin alfasha da
zalunci amma harshensa yana
cikin kage a cikin mutuncin rayayyu
da matattu amma bai damu da
abin da yake fada ba” (Aljawabul
Kafi 203). Don haka dan uwa
musulmi ka rika lura da abin da
zaka furta da wanda zaka rubuta,
Allah YaSa Mu Dace.

4 responses to “kame Bakinka(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
 1. Salisu Avatar
  Salisu

  Allah yasa mu’iya kame bakinmu

 2. usman isa el-yazaki, kwandare Avatar
  usman isa el-yazaki, kwandare

  Allah ya mamu ikon kame bakin mu ya kuma shiryar damu hanyar madaidaiciya

 3. Ubaidullah Muhammad Avatar
  Ubaidullah Muhammad

  Amin. Malam Allah yasaka da Alkhairi. Allah kabamu ikon ampani da abun da mukaji.

 4. Allah ya saka da alkhari amin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: