Falalar Kira zuwa ga shiriya da Hadarin kira zuwa ga Bata

Danna nan domin shiga karatu Online

Yana daga cikin ayyuka masu falala, wanda kuma mutum yake samun ladansu har bayan ransa, kira zuwa ga shiriya.
Abu Huraira(Allah kara masa yarda) ya rawaito hadisi daga Manzon Allah(Allah yayi dadin tsira gareshi). Manzon Allah yace: Wanda yayi kira zuwa Ga Shiriya, yana da lada kwatankwacin ladan wanda suka bishi kan wannan shiriya da yayi kira zuwa gareshi, kuma ba za’a rage wa wa’innan wainda suka amshi kiran komai daga ladansu ba, haka nan wanda yayi kira zuwa ga Tsabon Allah, Shima yana da zunubi kwatankwacin zunubin wa’inda suka bishi kan wannan tsabo,kuma ba za’a rage musu komai ba daga Zunubansu.
Wannan yake nuna Falalar Kira zuwa ga alkhairi da shiriya da Sunnah, yake kuma nuna hadarin kira zuwa ga bata, da tsabon Allah da Bid’ah.

Sannan kuma ya kamata mutum ya sani cewa shi kira zuwa ga shiriya yakan kasancewa da Magana ko da aiki, haka nan shima kira zuwa ga bata.
kada ka fadi wata magana ko ka aikata wata aiki da wanda kasan wani zaiyi koyi dakai a kai sai in ya kasance wannan aiki ne da ya zama ba na tsabo ba. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Falalar Kira zuwa ga shiriya da Hadarin kira zuwa ga Bata”
  1. sani ahmad gumi Avatar

    Allah yasaka da Alheri

Leave a Reply

Categories
Latest updates