Da Sunan Allah Mai Rahama mai jin Kai.
Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zhul Hijja
Watan Zhul Hijja yana daga cikin watanni masu girma acikin Musulunci wanda ake kiransu “Ash-Hurul Hurum“. Hakanan kwanaki goma na farkon zhul Hijja sune mafi girman kwanaki a shekara kamar yadda aka rawaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yace:
Babu wasu ranaku da ayyukan alheri acikinsu suka fi soyuwa awurin Allah fiye da wa’innan kwanaki, sai Sahabbai suka tambayi Annabi, Koda Jihadi ne don Daukaka kalmar Allah? sai Annabi yace: koda Jihadi ne don daukaka kalmar Allah, sai dai mutumin da ya fita da dukiyansa, da iyalansa [zuwa Jihadi] kuma bai dawo da komi ba
Bukhari: 969
Wannan Hadisi yana nuna cewa babu wasu ranaku a duniya da Mutum zaiyi aikin alheri acikinsu wanda sukafi soyuwa zuwa ga Allah fiye da wa’innan ranaku. koda Jihadi ne Mutum ya fita a wani rana wanda ba wa’innan ba ladan sa bazai kai wanda yayi aikin alheri acikin wa’innan ranaku ba, sai dai wanda ya fita Jihadi da dukiyarsa, da iyalansa Amma bai dawo da komai ba.
Azumin Ranan Arafa:
Azumin Ranar Arafa yana daga cikin Aikin lada mai girma da Mutum zai aikata acikin wa’innan Ranaku.
Ranar Arafa itace rana ta tara ta watar Zhul Hijja.
Azumin Ranar Sunnah ce mai karfi ga wanda baije aikin Hajji ba, amma wanda yaje aikin hajji bazaiyi ba.
Falalar Azumin Ranar Arafa:
Duk wanda ya Azumci Ranar Arafa Allah zai kankare masa zunubansa na Shekarar da ya wuce da Shekarar da ake ciki. kamar yadda aka rawaito lokacin da aka tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi game da Azumin Ranan Arafa sai yace:
Yana kankare zunuban shekarar da ta wuce da wacce tayi ragowa
Sahih Muslim” 1162
Shin Duk Girman Laifin da Mutum ya aikata idan Mutum yayi Azumin Ranar Arafa Allah zai yafe masa?
Zunuban da ake kankare wa kamar yadda Maluma sukayi bayani sune Kananan Zunubai banda manya. manyan zunubai suna bukatan Tuba kafin Allah ya yafe su.
Allah yasa mudace ya bamu daman Ribatar wannan Rana.
Leave a Reply