Mai rubutu: Hamza Diso
Adadin wadanda sukayi imani da Annabi suka hadu dashi suka kuma ji maganar sa sun fi mutum dubu dari (100,000) kuma Babu wani guri ko gari daya hadasu dukkan Su a lokaci guda, sannan babu wani sahabbi da ya san dukkanin maganganun Annabi kasan cewar suma suna da iyali da kasuwanci ko Noma ko tafiye-tafiye, Kenan bazai yiwu ko yaushe su kasance tare da Annabi ba.
A duk inda Annabi Zai je akwai wani bangare na sahabbai tare dashi wadanda suke jin maganganun sa suke kuma haddacewa ko rubutawa, ta yadda abinda wane bai ji ba to wane yaji, Allah da kansa shi yayiwa sahabbai umarnin Yin haka sanda yace:
وَمَا كَانَ الْمُؤْمِنُونَ لِيَنفِرُوا كَافَّةً ۚ فَلَوْلَا نَفَرَ مِن كُلِّ فِرْقَةٍ مِّنْهُمْ طَائِفَةٌ لِّlيَتَفَقَّهُوا فِي الدِّينِ وَلِيُنذِرُوا قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُوا إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ
Bai kamata ga muminai su fita gaba dayan Su ba, me zai hana baza a samu wani yanki daga cikin kowanne bangare ba su fita, don su (sami karin) fahimta a addini kuma suyiwa mutanan su wa’azi idan sun dawo ko sa kiyayi (dokokin Allah)
Kenan ana bukatar sahabbai su dinga kasuwa gida biyu, idan Annabi zai aika wasu yaki ko wani abun daban to wasu su zauna tare dashi don susan abubuwan da suka sauka na wahayi sannan su sanar da yan uwansu idan sun dawo.
Sanda Annabi zai tafi wani waje, yaki ko wanin sa, to asamu wadanda zasu fita tare dashi su dinga rike abubuwan da yake fada ta yadda zasu sanar da wadanda suke gida idan an dawo.
Kenan sahabbai basa rabuwa da Annabi, sai dai kuma bazai Yiwu ace wani sahabi daya koma biyu ko 20 sun San komai game da maganganun Annabi ba.
Wannan yana daga cikin hikimar bawa Annabi damar auran mata dayawa, ta yadda dukkan Su zasu zamo masu ruwaito ayyukan sa da maganganun sa na cikin gida, don shi Annabi abin koyi ne a komai nasa kuma ga kowa, a wajensa za a fahimci Alkur’ani a kuma koyi yadda ake jagorantar Al’umma.
Shine misalin miji na gari soja a filin yaki dan kasuwa mai amana, makoci dan uwa, kai koma me kake bukata to shine madubin da zai zama maka jagora, to kaga Kenan dole rayuwarsa baza ta zama sirri ba, dole a ruwaito komai da komai.
لَّقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِّمَن كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا
Kyakykyawan abun koyi ya tabbatar gare ku a cikin (rayuwar) Ma’aikin Allah ga duk Wanda yake fatan (haduwa mai kyau) da Allah da kuma (samun sakamako mai kyau) a ranar karshe, sannan kuma ya ambaci Allah dayawa.
Duk da cewa ba dukkanin sahabbai ne suke rubuta hadisi ba, to amma dukkanin Su suna kokarin tabbatar da magana kafin su jinginawa Annabi, zaka ga haka a fili a kissar da imamu Ahmad da wanin sa suka ruwaito cewar wata kaka tazo wajen Sayyidina Abubakar tana neman a bata gado, sai ya tambayi sahabbai ” Shin cikin ku akwai Wanda yasan hukuncin Annabi akan wannan?” Daya daga cikin sahabbai ya tashi yace: “kwarai Annabi ya bawa kaka sudusi”( daya bisa shida na abinda mamaci ya bari) sai Sayyidina Abubakar yace: wazai Kara tabbatar da haka? Wani sahabin ma ya tashi ya Kara tabbatar wa.
Cikin wannan kissa zaka fahimci cewar Ba komai Sayyidina Abubakar ya sani ba (shi kansa) sannan zaka fahimci yadda sahabbai suke kokarin tabbatar da magana kafin su jinginawa Annabi.
Kamar yadda muka Sani hanyar ruwaito hadisi kodai mai riwaya yaji ya haddace, ko kuma yaji ya rubuta, abubuwan da aka rubuta kuma akwai wadanda suka zo mana kamar Hadisan da abu hurairah yayi wa Hammam shiftar su ya rubuta wadanda har yau sunanan, idan kana so sai ka danna nan domin saukar da littafin ka karanta.
Haka cikin su akwai wadanda basu zo mana su kadai ba sai a cikin wasu litattafan.
A rubutu na gaba zamu tattauna akan su duka.
Allah ya bamu ikon gane gaskiya da kuma aiki da ita.
Leave a Reply