HAKIKA HADITHAN AZUMIN AA'SHUU'RAA SUN TABBATA HATTAA A CIKIN LITTATTAFAN SHI'AH MA, AMMA DA YAKE YAWANCIN YAN SHI'AH BA SA YIN KARATU SAI WAKE-WAKE BA SU SAN HAKAN BA

Danna nan domin shiga group na karatu Online

HAKIKA HADITHAN AZUMIN
AA’SHUU’RAA SUN TABBATA
HATTAA A CIKIN LITTATTAFAN
SHI’AH MA, AMMA DA YAKE
YAWANCIN YAN SHI’AH BA SA
YIN KARATU SAI WAKE-WAKE
BA SU SAN HAKAN BA!!
‘Yan’uwa Musulmi! Lalle mun
rubuta a shafukan Facebook a ran
5/1/1434 H 19/11/2012 M cewa:
((BANDA BIDI’AR ‘YAN SHI’AH,
BANDA KUMA BIDI’AR
NAWAASIB A RANAR
AA’SHUU’RAA, ABIN DA KE
WAJIBI SHI NE LAZIMTAR
SUNNAH WATAU AZUMCE
WANNAN RANA TA GOMA GA
WATAN MUHARRAM)).
Bayan wannan rubutu namu sai
muka ga wasu masu addinin
Shi’ah suna ta karyata halaccin yin
azumin Aa’shuu’raa suna cewa
wannan azumin kiren karya ne
kawai daga mu Ahlus-Sunnah Wal
Jama’ah!!
Wannan shi ya sa a wannan rana
ta litinin 19/1/1434 H 3/12/2012 M
muka ga ya dace mu kawo hujjojin
da za su tabbatar da cewa lalle
azumin ranar Aa’shuu’raa azumi
ne ya tabbata a cikin littattafan
‘Yan Shi’ah ma, kamar yadda ya
tabbata a cikin littattafan Ahlus
Sunnah Wal Jama’ah, koda yake
dai jahilan ‘yan Shi’ah ba su san
da hakan ba!!!
Hakika, yana daga cikin al’adar
‘yan bidi’ah da bin son zuciya a
zamanin da da kuma yanzu cewa
su ba sa jin kunyar kiren karya, da
yin kage ga abokan husumarsu,
haka nan ba sa jin kunyar boye wa
mabiyansu yadda gaskiyar al’amari
yake’ saboda tsoron da suke yi na
cewa idan har sun gaya musu
gaskiyar to wannan zai zama
sanadiyyar yadda su mabiyan
nasu za su kauracewa bidi’ar tasu
su koma yin riko da gaskiyar da
tabbata cikin sunnar Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah.
‘Yan’uwa Musulmi! Akwai wani
Dan Shi’ah mai suna
Muhammadus Samaawii mai
yawan nuna wa Sahabban Manzon
Allah da Jama’ar Ahlus Sunnah
kiyayya ya yi wani littafi da ya
sanya wa suna: “Ash-Shii’atu Hum
Ahlus Sunnah” a cikin wannan
littafi nasa lalle ya ambaci abin da
yake nuna cewa lalle shi jahili ne,
kuma lalle shi mutum ne da ba ya
karanta littattafan ilmi, hatta
littattafansu na Shi’ah ma ba ya
karanta su!! Ya rubuta cikin
wannan littafi nasa Ash-Shii’ah
Hum Ahlus-Sunnah a shafi na
301-302 kamar haka:-
(( ﻭﻳﺘﺒﻴﻦ ﻟﻨﺎ ﺃﻳﻀﺎ ﺑﺎﻥ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ
ﻳﺤﺘﻔﻠﻮﻥ ﺑﻴﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻷﻧﻬﻢ ﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﺳﻨﺔ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦ
ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻭﺑﻨﻲ ﺃﻣﻴﺔ ﻓﻲ ﺍﺣﺘﻔﺎﻟﻬﻢ ﺑﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻷﻧﻬﻢ
ﺍﻧﺘﺼﺮﻭﺍ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻭﺍﺧﻤﺪﻭﺍ ﺛﻮﺭﺗﻪ ﺍﻟﺘﻲ
ﻛﺎﻧﺖ ﺗﻬﺪﺩ ﻛﻴﺎﻧﻬﻢ، ﻭﻗﻄﻌﻮﺍ ﺑﺬﻟﻚ ﺩﺍﺑﺮ ﺍﻟﺸﻐﺐ
ﻋﻠﻰ ﺣﺪ ﺯﻋﻤﻬﻢ… ﻭﺗﻘﺮﺏ ﺍﻟﻴﻬﻢ ﻋﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﺴﻮﺀ ﻣﻦ
ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻓﻮﺿﻌﻮﺍ ﻟﻬﻢ ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ ﻓﻲ
ﻓﻀﻞ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻭﺍﻥ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﺗﺎﺏ
ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻪ ﺍﺩﻡ، ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﺭﺳﺖ ﻓﻴﻪ ﺳﻔﻴﻨﺔ ﻧﻮﺡ
ﻋﻠﻰ ﺟﺒﻞ ﺍﻟﺠﻮﺩﻱ، ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﻛﺎﻧﺖ ﻓﻴﻪ
ﺍﻟﻨﺎﺭ ﺑﺮﺩﺍ ﻭﺳﻼﻣﺎ ﻋﻠﻰ ﺍﺑﺮﺍﻫﻴﻢ، ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ
ﺧﺮﺝ ﻓﻴﻪ ﻳﻮﺳﻒ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﺠﻦ ﻭﺭﺩ ﻓﻴﻪ ﺑﺼﺮ
ﻳﻌﻘﻮﺏ، ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﺍﻧﺘﺼﺮ ﻓﻴﻪ ﻣﻮﺳﻰ ﻋﻠﻰ
ﻓﺮﻋﻮﻥ، ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﻧﺰﻟﺖ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﻋﻴﺴﻰ
ﻣﺎﺋﺪﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ… ﻭﻗﺪ ﺃﻣﻌﻨﻮﺍ ﻓﻲ ﺍﻟﻜﺬﺏ ﻋﻨﺪﻣﺎ
ﺭﻭﻭﺍ ﺑﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻫﺎﺟﺮ
ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺼﺎﺩﻑ ﺩﺧﻮﻟﻪ ﺍﻟﻴﻬﺎ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ
ﻓﻮﺟﺪ ﻳﻬﻮﺩ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﺻﻴﺎﻣﺎ ﻓﺴﺄﻟﻬﻢ ﻋﻦ ﺍﻟﺴﺒﺐ
ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ: ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﺍﻧﺘﺼﺮ ﻓﻴﻪ ﻣﻮﺳﻰ ﻋﻠﻰ
ﻓﺮﻋﻮﻥ ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ :
ﻧﺤﻦ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﻤﻮﺳﻰ ﻣﻨﻜﻢ، ﺛﻢ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺑﺼﻮﻡ
ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻭﺗﺎﺳﻮﻋﺎﺀ ﻟﻤﺨﺎﻟﻔﺔ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ. ﻭﻫﺬﺍ ﻛﺬﺏ
ﻣﻔﻀﻮﺡ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Yana bayyana a gare mu
har yanzu cewa: lalle Ahlus-
Sunnah Wal Jamaa’ah suna yin
buki saboda zuwan ranar
Aa’shuu’raa saboda su sun bi
sunnar Yaziidu Dan Mu’aawiyah
ne da kuma Banuu Umayyah cikin
bukin da suke yi saboda zuwan
wannan ranar, saboda su a cikinsa
ne suka samu nasara a kan
Husaini, suka kuma dankofar da
tada kayar baya da ya yi, wacce
take barazana ga kasancewarsu a
kan mulki, saboda haka suka
yanke dukkan wani tada hargitsi
kamar yadda suke riyawa…Sannan
miyagun maluma daga cikin Ahlus-
Sunnah Wal Jamaa’ah suka nemi
shiga fada ta hanyar kirkiro musu
hadithan karya da suke nuna
falalar wannan rana, da kuma
cewa Aa’shuu’raa ita ce ranan nan
da Allah ya karbi tuban Annabi
Adamu a cikinta, kuma ita ce ranan
nan da jirgin Annabi Nuhu ya
sauka a kan dutsen Juudii a
cikinta, kuma ita ce ranan nan da
Wuta ta kasance wani irin sanyi da
aminci ga Annabi Ibrahim a cikinta,
kuma ita ce ranan nan da Annabi
Yusuf ya fita daga cikin kurkuku a
cikinta, kuma aka mayar da ganin
Annabi Yakubu a cikinta, kuma ita
ce ranan nan da Annabi Musa ya
samu nasara a kan Fir’auna a
cikinta, kuma ita ce ranan nan da
teburin abinci daga sama ya sauko
wa Annabi Isa a cikinta… Hakika
suka yi zurfi a cikin yin karya a
lokacin da suka ruwaito cewa:
Annabi mai tsira da amincin Allah
shi da iyalansa a lokacin da ya yi
hijira zuwa Madinah, shigarsa
Madinan ya dace da ranar
Aa’shuu’raa saboda haka sai ya
tarar da Yahudawan Madinah suna
yin azumi, sai ya tambaye su dalilin
yin hakan, sai suka ce: wannan
rana ce da Musa ya ci nasara a
kan Fir’auna a cikinta, to sai
Annabi mai tsira da amincin Allah
shi da iyalansa ya ce: ai mu ne
muka fi dacewa da Annabi Musa a
kanku, daga nan sai ya umurci
Musulmi da yin azumin
Aa’shuu’raa da kuma Taa’suu’aa
saboda saba wa Yahudawa. Lalle
wannan karya ce mai cike da abin
kunya)). Intaha.
‘Yan’uwa Musulmi! Haka wannan
Dan Shi’ah mai yawan nuna
kiyayya ga Sahabban Manzon
Allah da kuma Ahlus Sunnah Wal
Jamaa’ah ya rubuta cikin littafinsa,
duk kuwa da cewa ruwayoyi da
yawa masu kyakkyawan isnadi a
cikin littattafan ‘Yan Shi’ah sun zo
da maganar falalar yin azumi a
ranar Aa’shuu’raa, a lokacin da
ruwayoyin da suka hana yin
azumin ranar Aa’shuu’raa cikin
littattafan nasu dukkansu masu
rauni ne!! Kuma duk da yake daya
daga cikin manyan maluman ‘Yan
Shi’ah ya amince da wannan
kakikar, wannan malamin kuwa shi
ne: Muhammadur Ridhaa Al-
Husain Al-Haa’irii a cikin littafinsa
mai suna: Najaatul Ummah Fii
Iqaamatil Azaai Alal Husaini Wal
A’immah shafi na 145,146,148,
littafin da aka buga a garin Qum a
can Iran, a shekarar hijirah ta
1413.
Mu a nan muna gaya wa wannan
Dan Shi’ah mai bayyana
kiyayyarsa ga Sahabban Manzon
Allah da kuma Ahlus Sunah: Cewa
su wadannan Ahlus Sunnah da
kake zagi kuma kake yi musu kage
da yarfe, za su kure ka, kuma za su
bayyana jahilcinka ta hanyar kawo
maka abin da zai karyata ka ya
kuma kunyata ka daga cikin abin
da yake rubuce a cikin yardaddun
littattafai a wurin ‘Yan Shi’ah.
Ga dai Muhammadut Tuusii wanda
yake babban malami ne a wurin
‘Yan Shi’ah yana ruwaitowa a cikin
littattafansan nan guda biyu watau:
Tahziibul Ahkam, da kuma
Alistibsar, kuma wadannan
littattafai guda biyu suna daga cikin
manyan littattafan Shi’ah guda
hudu da ake gadara da su,
wadanda Sharafud Diinil Aa’milii ya
yi magana a kansu cikin littafin:
Almuraa’ja’at 110/311 a inda ya
ce:-
(( ﺍﻟﻜﺎﻓﻲ، ﻭﺍﻟﺘﻬﺬﻳﺐ، ﻭﺍﻻﺳﺘﺒﺼﺎﺭ، ﻭﻣﻦ ﻻ
ﻳﺤﻀﺮﻩ ﺍﻟﻔﻘﻴﻪ، ﻭﻫﻲ ﻣﺘﻮﺍﺗﺮﺓ ﻭﻣﻀﺎﻣﻴﻨﻬﺎ ﻣﻘﻄﻮﻉ
ﺑﺼﺤﺘﻬﺎ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Al-Kaafii, da At-Tahziib,
da Alistibsar, da Man Laa
Yahdhuruhul Faqiih, wadannan
mutawaatirai ne, kuma abin da
suka kunsa an tabbatar da
ingancinsa)). Intaha.
HADITHAN DA SUKE NUNA
FALALAR YIN AZUMIN
AA’SHUU’RAA DAGA
LITTATTAFAN ‘YAN SHI’AH:
‘Yan’uwa Musulmi! Saboda
bayyana wa jama’a hakikanin
gaskiya cikin wannan mas’ala za
mu kawo hadithai dai-dai har tara
daga muhimman littattafan Shi’ah
wadanda suke yin umurni da yin
azumin Aa’shuu’raa da kuma nuna
falalarsa, sabanin abin da shi
wannan Dan Shi’ah mai cike da
nunawa Sahabbai kiyayya:-
Hadithi na farko: Tuu’sii ya ruwaito
cikin Tahzii’bul Ahkam 4/299, da
kuma cikin Alistibsar 2/134, shi ma
Al-Faidhul Kaa’shaa’nii ya ruwaito
cikin Waa’fii 7/13, shi ma Al-Hurrul
Aa’milii ya ruwaito cikin
Wasaa’ilush Shi’ah 7/337, shi ma
Al-Barwajurdii ya ruwaito cikin
Jaami’u Ahaa’dithush Shi’ah
9/474-475, dukkansu wadannan
sun ruwaito daga Ja’afarus Saa’diq
daga mahaifinsa Muhammadul
Baa’qir cewa Aliyyu Dan Abii
Taa’lib ya ce:-
(( ﺻﻮﻣﻮﺍ ﺍﻟﻌﺎﺷﻮﺭﺍﺀ: ﺍﻟﺘﺎﺳﻊ ﻭﺍﻟﻌﺎﺷﺮ؛ ﻓﺎﻧﻪ ﻳﻜﻔﺮ
ﺫﻧﻮﺏ ﺳﻨﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ku yi azumin
Aa’shuu’raa: Ranar tara, da goma,
lalle shi yana kankare zunuban
shekara)). Intaha.
Hadithi na biyu: Tuu’sii ya ruwaito
cikin Tahzii’bul Ahkam 4/299, da
kuma cikin Alistibsar 2/134, shi ma
Al-Faidhul Kaa’shaa’nii ya ruwaito
cikin Waa’fii 7/13, shi ma Al-Hurrul
Aa’milii ya ruwaito cikin
Wasaa’ilush Shi’ah 7/337, shi ma
Al-Barwajurdii ya ruwaito cikin
Jaami’u Ahaa’dithush Shi’ah 9/475,
shi ma Yusuful Bahraa’nii ya
ruwaito cikin Al-Hadaa’iqul
Nas’dhirah 13/370-371, dukkansu
wadannan sun ruwaito daga Aliyyu
Dan Abii ya ce:-
(( ﺻﺎﻡ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻪ ﻳﻮﻡ
ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira
da aminci shi da iyalinsa, ya yi
azumin ranar Aa’shuu’raa)). Intaha.
Hadithi na uku: Tuu’sii ya ruwaito
cikin Tahzii’bul Ahkam 4/300, da
kuma cikin Alistibsar 2/134, shi ma
Al-Faidhul Kaa’shaa’nii ya ruwaito
cikin Waa’fii 7/13, shi ma Al-Hurrul
Aa’milii ya ruwaito cikin
Wasaa’ilush Shi’ah 7/337, shi ma
Al-Barwajurdii ya ruwaito cikin
Jaami’u Ahaa’dithush Shi’ah 9/475,
shi ma Yusuful Bahraa’nii ya
ruwaito cikin Al-Hadaa’iqun
Naa’dhirah 13/370-371, dukkansu
wadannan sun ruwaito daga
Ja’afarus Saa’diq daga mahaifinsa
Muhammadul Baa’qir cewa ya ce:-
(( ﺻﻴﺎﻡ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻛﻔﺎﺭﺓ ﺳﻨﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Azumin ranar
Aa’shuu’raa kaffarar shekara ne)).
Intaha.
Hadithi na hudu: Al-Hurrul Aa’milii
ya ruwaito cikin Wasaa’ilush Shi’ah
7/347, shi ma Al-Barwajurdii ya
ruwaito cikin Jaami’u Ahaa’dithush
Shi’ah 9/474, shi ma Yusuful
Bahraa’nii ya ruwaito cikin Al-
Hadaa’iqun Naa’dhirah 13/377,
dukkansu wadannan sun ruwaito
daga Ja’afarus Saa’diq cewa ya
ce:-
(( ﻣﻦ ﺃﻣﻜﻨﻪ ﺻﻮﻡ ﺍﻟﻤﺤﺮﻡ ﻓﺎﻧﻪ ﻳﻌﺼﻢ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻣﻦ
ﻛﻞ ﺳﻴﺌﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Wanda duk ya samu
damar yin azumin Al-Muharram to
lalle shi zai tsare mai yin sa daga
dukkan wani mummuna)). Intaha.
Hadithi na biyar: Al-Hurrul Aa’milii
ya ruwaito cikin Wasaa’ilush Shi’ah
7/347, shi ma Al-Barwajurdii ya
ruwaito cikin Jaami’u Ahaa’dithush
Shi’ah 9/474, shi ma Yusuful
Bahraa’nii ya ruwaito cikin Al-
Hadaa’iqun Naa’dhirah 13/377,
dukkansu wadannan sun ruwaito
daga Annabi mai tsira da amincin
Allah shi da iyalinsa cewa ya ce:-
(( ﺍﻥ ﺍﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﻔﺮﻳﻀﺔ ﺍﻟﺼﻼﺓ
ﻓﻲ ﺟﻮﻑ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﺍﻥ ﺍﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﺷﻬﺮ
ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺻﻮﻡ ﺷﻬﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺪﻋﻮﻧﻪ ﺍﻟﻤﺤﺮﻡ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Na’ana: ((Lalle mafi falalar salla
bayan sallar farilla ita ce sallar
cikin dare, kuma lalle mafi falalar
azumi bayan watan Ramadhan, shi
ne azumin watan Allah da suke
kiran sa Al-Muharram)). Intaha.
Hadithi na Shida: Husainun Nuu’rit
Tabrisii ya ruwaito cikin
Mustadrakul Wasaa’il 1/594, shi
ma Al-Barwajurdii ya ruwaito cikin
Jaami’u Ahaa’dithush Shi’ah 9/475,
dukkansu wadannan sun ruwaito
daga Aliyyu Dan Abii Taa’lib cewa
ya ce:-
(( ﺻﻮﻣﻮﺍ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﺍﻟﺘﺎﺳﻊ ﻭﺍﻟﻌﺎﺷﺮ ﺍﺣﺘﻴﺎﻃﺎ؛
ﻓﺎﻧﻪ ﻛﻔﺎﺭﺓ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺘﻲ ﻗﺒﻠﻪ، ﻭﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﻌﻠﻢ ﺑﻪ ﺃﺣﺪﻛﻢ
ﺣﺘﻰ ﻳﺄﻛﻞ ﻓﻠﻴﺘﻢ ﺻﻮﻣﻪ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ku yi azumin ranar
Aa’shuu’raa: ranar tara da goma
saboda ihtiyaa’tii, domin shi
kaffarar shekarar da ta gabace shi
ne, idan dayanku bai san da shi ba
har ya ci abinci, to ya cika azumin
sa)). Intaha.
Hadithi na bakwai: Husainun
Nuu’rut Tabrasii ya ruwaito cikin
Mustadrakul Wasaa’il 1/594, shi
ma Al-Hurrul Aa’milii ya ruwaito
cikin Wasaa’ilush Shi’ah 7/347, shi
ma Al-Barwajurdii ya ruwaito cikin
Jaami’u Ahaa’dithush Shi’ah 9/475,
shi ma Radhiyyud Diin Aliyyub
Musa ya ruwaito cikin Iqbaa’lul
A’amal shafi na 554, dukkansu
wadannan sun ruwaito daga
Abdullahi Dan Abbas cewa ya ce:-
((ﺍﺫﺍ ﺭﺃﻳﺖ ﻫﻼﻝ ﺍﻟﻤﺤﺮﻡ ﻓﺎﻋﺪﺩ ﻓﺈﺫﺍ ﺍﺻﺒﺤﺖ ﻣﻦ
ﺗﺎﺳﻌﻪ ﻓﺎﺻﺒﺢ ﺻﺎﺋﻤﺎ. ﻗﻠﺖ: ﻛﺬﻟﻚ ﻛﺎﻥ ﻳﺼﻮﻡ
ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻪ؟ ﻗﺎﻝ: ﻧﻌﻢ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Idan ka ga jinjirin watan
Al-Muharram to ka kirga, idan ka
wayi gari a ran taransa to sai ka
tashi da azumi. Sai na ce: haka ne
Muhammad mai tsira da amincin
Allah shi da iyalansa yake yin
azumin? Sai ya ce: haka ne)).
Intaha.
Hadithi na takwas: Husainun
Nuurut Tabrasii ya ruwaito cikin
Mustadrakul Wasaa’il 1/594 daga
Ja’afarus Saa’diq cewa ya ce:-
(( ﺃﻭﻓﺖ ﺍﻟﺴﻔﻴﻨﺔ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺠﻮﺩﻱ ﻓﺄﻣﺮ
ﻧﻮﺡ ﻣﻦ ﻣﻌﻪ ﻣﻦ ﺍﻹﻧﺲ ﻭﺍﻟﺠﻦ ﺑﺼﻮﻣﻪ ﻭﻫﻮ ﺍﻟﻴﻮﻡ
ﺍﻟﺬﻱ ﺗﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻪ ﺍﺩﻡ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Jirgi ya sauka a kan
Juu’dii a ranar Aa’shuu’raa sai
Nuhu ya umurci wadanda ke tare
da shi daga cikin mutane da
aljannu da su yi azuminsa, kuma
shi ne ranan nan da Allah Ya karbi
tubar Adamu alaihis Salam a
cikinsa)). Intaha.
Hadithi na tara: Abuu Ja’afar
Muhammad Dan Baa’bawaihi
Wanda ake masa lakabi da As-
Saduuq ya ruwaito cikin littafinsa
Al-Muqnii shafi na 101 cewa:-
(( ﺍﻧﻪ ﻓﻲ ﻋﺸﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺤﺮﻡ ﻭﻫﻮ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ
ﺍﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻮﺑﺔ ﺍﺩﻡ ﻭﻓﻴﻪ ﺍﺳﺘﻮﺕ ﺳﻔﻴﻨﺔ ﻧﻮﺡ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﺠﻮﺩﻱ ﻭﻓﻴﻪ ﻋﺒﺮ ﻣﻮﺳﻰ ﺍﻟﺒﺤﺮ ﻭﻓﻴﻪ ﻭﻟﺪ ﻋﻴﺴﻰ
ﺍﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﻓﻴﻪ ﺍﺧﺮﺝ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻧﺲ ﻣﻦ
ﺑﻄﻦ ﺍﻟﺤﻮﺕ ﻭﻓﻴﻪ ﺍﺧﺮﺝ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﺳﻒ ﻣﻦ ﺑﻄﻦ
ﺍﻟﺠﺐ ﻭﻓﻴﻪ ﺗﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻡ ﻳﻮﻧﺲ ﻭﻓﻴﻪ ﻗﺘﻞ ﺩﺍﻭﺩ
ﺟﺎﻟﻮﺕ ﻓﻤﻦ ﺻﺎﻡ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﺫﻧﻮﺏ ﺳﺒﻌﻴﻦ
ﺳﻨﺔ ﻭﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻣﻜﺎﺗﻢ ﻋﻠﻤﻪ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((A ranar goma ga Al-
Muharram ne, wanda shi ne ranar
Aa’shuu’raa da Allah Ya saukar da
tubar Adam a cikinsa, kuma jirgin
Nuhu ya sauka a kan Juu’dii a
cikinsa, kuma Musa ya ketare teku
a cikinsa, sannan aka haifi Isa Dan
Maryam a cikinsa, sannan Allah Ya
fitar da Yunus daga cikin kifi a
cikinsa, kuma a cikinsa ne Allah Ya
fitar da Yusuf daga cikin rijiya,
kuma a cikinsa ne Allah Ya karbi
tubar mutanen Yunus, sannan a
cikinsa ne Dawuda ya kashe
Jaluta, wanda duk ya yi azumin
wannan rana za a gafarta masa
zunubban shekaru saba’in, kuma
za a gafarta masa maboyace-
maboyacen ilminsa)). Intaha.
‘Yan’uwan Musulmi! Idan ‘Yan
Shi’ah Raa’fidah sun ce suna jin
haushi Ahlus Sunnah ne saboda
su ba sa yin bidi’o’in da suke yi a
ranar Aa’shuu’raa da wasu
kwanukan watan Al-Muharram na
makoki irin na siyasa, da kururuwa,
da marin kumatu, da yayyaga
tufafi, da yi wa jiki rauni, sai a ba
su amsa ta fiskoki biyu:-
Fiska ta farko: Sai a ce da su:
Annabi Muhammad mai tsira da
amincin Allah bai yi umurni da a
rika yin haka ba a wannan rana ta
Aa’shuu’raa, a’a abin da shi Annabi
ya ce shi ne: Kururuwa saboda
mutuwar wani yana daga cikin
aikin Jahiliyyah. Wannan kuwa
hadithi ne ingantacce da yake
rubuce a cikin littattafan Ahlus
Sunnah da kuma littattafan Shi’ah.
A cikin littattafan Ahlus Sunnah
Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi
na 1294 daga Abdullahi Dan
Mas’ud cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah ya:-
(( ﻟﻴﺲ ﻣﻨﺎ ﻣﻦ ﻟﻄﻢ ﺍﻟﺨﺪﻭﺩ ﻭﺷﻖ ﺍﻟﺠﻴﻮﺏ ﻭﺩﻋﺎ
ﺑﺪﻋﻮﻯ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ba ya daga cikinmu,
mutumin nan da ya mari kumatu’
sannan ya kyakkece tufafi’ kuma
ya yi kira irin na jahiliyyah)). Intaha.
Sannan Imamu Muslim ya ruwaito
hadithi na 934 daga Abu Malik Al-
Ash’arii cewa Annabi mai tsira da
amincin Allah ya ce:-
(( ﺍﺭﺑﻊ ﻓﻲ ﺃﻣﺘﻲ ﻣﻦ ﺍﻣﺮ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ ﻻ ﻳﺘﺮﻛﻮﻧﻬﻦ:
ﺍﻟﻔﺨﺮ ﻓﻲ ﺍﻷﺣﺴﺎﺏ ﻭﺍﻟﻄﻌﻦ ﻓﻲ ﺍﻷﻧﺴﺎﺏ
ﻭﺍﻻﺳﺘﺴﻘﺎﺀ ﺑﺎﻟﻨﺠﻮﻡ ﻭﺍﻟﻨﻴﺎﺣﺔ. ﻭﻗﺎﻝ: ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺔ ﺍﺫﺍ ﻟﻢ
ﺗﺘﺐ ﻗﺒﻞ ﻣﻮﺗﻬﺎ ﺗﻘﺎﻡ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻭﻋﻠﻴﻬﺎ ﺳﺮﺑﺎﻝ ﻣﻦ
ﻗﻄﺮﺍﻥ ﻭﺩﺭﻉ ﻣﻦ ﺟﺮﺏ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Akwai abu hudu cikin
al’ummata na lamarin jahiliyya da
ba za su bar yin su ba: Alfahari da
asali, da sukar asalin wani, da
ganin tasirin taurari cikin saukan
ruwan sama’ da kuma kururuwa a
lokacin mutuwa. Ya ce: Mai
kururuwa saboda mutuwa idan ba
ta tuba kafin mutuwarta ba, to za a
tsaida ita a ranar Kiyama tana
sanye da tufar narkakken dalma ko
man petur, da kuma wata irin rigar
gazuwa)). Intaha.
Daga littattafan Shi’ah kuma:
Husainul Bawajurdii ya ruwaito a
cikin Jaa’mi’u Ahaa’dii,thish Shii’ah
3/488, shi ma Yusuful Bahraa’nii ya
ruwaito a cikin Al-Hadaa’iqun
Naa’dhirah 4/167, shi ma Al- Hurrul
A’alamii ya ruwaito a cikin
Wasaa’iliush Shi’ah 2/915, shi ma
Abu Ja’afar Ibnu Baa’bawaihi
Wanda ake masa lakabi da As-
Saduuq ya ruwaito a cikin littafin
Man La Yahdhuruhul Faqiih
4/271-272 dukkan wadannan sun
ruwaito cewa:-
(( ﺍﻥ ﻣﻦ ﺃﻟﻔﺎﻅ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﻳﺴﺒﻖ ﺍﻟﻴﻬﺎ: ﺍﻟﻨﻴﺎﺣﺔ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ .((
ﺍﻧﺘﻬﻰ.
Ma’ana: ((Yana daga cikin lafuzzan
Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah wadanda wani bai rigaye shi
zuwa gare su ba: Kururuwa
saboda mutuwa yana daga cikin
aikin jahiliyyah)). Intaha.
Fiska ta biyu: Sai a ce da su: Ko
shakka babu, mafi girman musibar
da ta taba samun Al’ummar
Musulmi lalle ita ce mutuwar
Annabi mai tsira da amincin Allah’
kamar yadda hakan ya tabbata
cikin nassin Annabi mai tsira da
amincin Allah cikin littattafan Ahlus
Sunnah, da kuma littattafan Shi’ah
duka.
A cikin littattafan Ahlus Sunnah
Imamut Tabaraanii ya ruwaito cikin
Al-Mu’ujamul Kabir hadithi na
6,579, da Imamud Daa’ra-Qudnii
hadithi na 84, da Imamul Baihaqii
cikin Shu’abul Iiman hadithi na
10,153, sannan Albaa’nii ya
inganta shi cikin Silsilah Sahihah
3/97, da Sahihul Jaa’mi’is Sagir
hadithi na 348, cewa Annabi mai
tsira da amincin Allah ya ce:-
(( ﻣﻦ ﺃﺻﻴﺐ ﺑﻤﺼﻴﺒﺔ ﻓﻠﻴﺬﻛﺮ ﻣﺼﻴﺒﺘﻪ ﺑﻲ ﻓﺈﻧﻬﺎ
ﺍﻋﻈﻢ ﺍﻟﻤﺼﺎﺋﺐ.(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Duk wanda aka sama da
wata musiba, to ya tuna da
musibar da ta same shi saboda ni –
watau saboda mtuwata- lalle ita ce
mafi girman musibu)). Intaha.
Wannan nassin hadithi an ruwaito
shi cikin littattafan Shi’ah ma,
kamar: Littafin Al-Kaa’fii 3/220, da
Wasaa’ilush Shi’ah 2/911.
To amma duk da kasancewar
ranar mutuwar Annabi ita ce ranar
bakin ciki mafi girma ga dukkan
wani Musulmi to amma Shari’ar
Musulunci ba ta ce Musulmi su riki
wannan ranar a matsayin wani Idi
na nuna bakin ciki da juyayi, da
yayyaga tufafi, da yi wa jikkuna
rauni ba.
Kuma Ahlul Baiti da sauran Sabbai
babu daya daga cikinsu da ya riki
ranar mutuwar shi Annabi mai tsira
da amincin Allah a matsayin Idi na
nuna bakin ciki da juyayi, haka nan
babu wanda ya riki ranar mutuwar
Sayyidina Abubakar, da ranar
kashe Sayyidina Umar, da
Sayyidina Uthmanu, da Sayyidina
Aliyyu a matsayin ranar Idin nuna
bakin ciki da juyayi da yayyaga
tufafi da yi wa jikkuna rauni jini na
fita.
In kuwa haka lamarin yake, to
mene ne zai sa su ‘Yan Shi’ah su
riki ranar kashe Sayyidina Husaini
a matsayin ranar Idin nuna bakin
ciki, da juyayi, da yayyaga tufafi,
da yi wa jikkuna rauni jini na fita,
amma kuma ba sa rikon ranar
mutuwar Annabi, da ranar kashe
Sayyidina Aliyyu uban shi
Sayyidina Husaini kuma mutumin
da ya fi shi daraja a wurin Allah
nesa ba kusa ba, me ya sa ba sa
rike wadannan ranakun a matsayin
ranakun juyayi da bakin ciki?
Amsar wannan tambaya ita ce:
Saboda su ‘Yan Shi’ah mutane ne
wadanda Shaidan ya batar da su
Duniya da Lahira, wannan shi ya
sa suke gina addininsu a kan
tsabar wauta da kuma son zuciya.
Allah Ya tsare mu daga fadawa
cikin ko wace irin bidi’ah. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories