HUDUBA DAGA MASALLACIN
ABU HURAIRA (RA), SOKOTO A
KAN HADARIN SIGARI DA
DANGOGINTA
14 ga Zhul Qi’ida 1434H (20 ga
Agusta 2013)
Ya ku bayin Allah!
Yana daga cikin kyawon addinin
musulunci cewa, ba wani alheri ko
jin dadi tatacce a duniya ko a
lahira da bai nuna mana shi kuma
ya umurce mu da kokarin neman
sa ba. Babu wani sharri ko wahala
ko kunci da addinin musulunci bai
jawo hankalinmu zuwa ga kauce
ma sa ba da kuma kauce ma duk
abinda ke kawo shi.
Addinin musulunci ya umurci
mutum ya mutunta hankalin da
Allah ya ba shi tunda shi ne abinda
Allah ya fifita shi da shi a kan
sauran halittu. Saboda haka, duk
abinda ke taba hankali Allah ya
haramta shi.
Wannan darajar ita ce Allah
madaukakin sarki yake cewa a kan
ta:
(( ﻭﻟﻘﺪ ﻛﺮﻣﻨﺎ ﺑﻨﻰ ﺀﺍﺩﻡ ﻭﺣﻤﻠﻨـﺎﻫﻢ ﻓﻰ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺒﺤﺮ
ﻭﺭﺯﻗﻨـﺎﻫﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﻴﺒـﺎﺕ ﻭﻓﻀﻠﻨـﺎﻩﻡ ﻋﻠﻰ ﻛﺜﻴﺮ
ﻣﻤﻦ ﺧﻠﻘﻨﺎ ﺗﻔﻀﻴﻼ] ((ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ70: ].
Da hankali ne mutum ke gane
abinda ke amfanin sa da mai cutar
sa, ya san masoyinsa ya san
makiyinsa, ya shirya rayuwarsa
yadda za ta zama mai mai amfani
gare shi da sauran jama’a.
Nazarin alkur’ani ya nuna cewa,
Allah madaukakin sarki yana
magana ne da dan adam kawai ta
fuskar hankalinsa.
(( ﻗﺪ ﺑﻴﻨﺎ ﻟﻜﻢ ﺍﻷﻳـﺎﺕ ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﻌﻘﻠﻮﻥ] ((ﺍﻟﺤﺪﻳﺪ[17:
))ﻓﺘﻘﻮﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺎﺃﻭﻟﻰ ﺍﻻﻟﺒـﺎﺏ] ((ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ.[100:
))ﺇﻥ ﻓﻰ ﺫﻟﻚ ﻻﻳـﺎﺕ ﻻﻭﻟﻰ ﺍﻟﻨﻬﻰ]((ﻃﻪ.[281:
))ﻫﻞ ﻓﻰ ﺫﻟﻚ ﻗﺴﻢ ﻟﺬﻯ ﺣﺠﺮ] ((ﺍﻟﻔﺠﺮ5: ].
Da zaran mutum ya rasa hankali
musulunci bai magana da shi,
domin ya koma daidai da dabba.
Wata dabbar ma ta fi shi don tana
da amfani. Shi ya sa ma ake zuwa
kasuwa a sawo ta.
Nassin alkur’ani dangane da giya a
fili yake bai bukatar dogon tunani:
(( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻟﺨﻤﺮ ﻭﺍﻟﻤﻴﺴﺮ
ﻭﺍﻷﻧﺼﺎﺏ ﻭﺍﻷﺯﻻﻡ ﺭﺟﺲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ
ﻓﺎﺟﺘﻨﺒﻮﻩ ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﻔﻠﺤﻮﻥ ﺇﻧﻤﺎ ﻳﺮﻳﺪ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﺃﻥ ﻳﻮﻗﻊ
ﺑﻴﻨﻜﻢ ﺍﻟﻌﺪﺍﻭﺓ ﻭﺍﻟﺒﻐﻀﺎﺀ ﻓﻲ ﺍﻟﺨﻤﺮ ﻭﺍﻟﻤﻴﺴﺮ
ﻭﻳﺼﺪﻛﻢ ﻋﻦ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻋﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻬﻞ ﺃﻧﺘﻢ
ﻣﻨﺘﻬﻮﻥ؟] (ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ90: ].
Haka ma hadissan manzon Allah
(S):
” ﻛﻞ ﻣﺴﻜﺮ ﺧﻤﺮ، ﻭﻛﻞ ﻣﺴﻜﺮ ﺣﺮﺍﻡ، ﻭﻣﻦ ﺷﺮﺏ
ﺍﻟﺨﻤﺮ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻓﻤﺎﺕ ﻭﻫﻮ ﻳﺪﻣﻨﻬﺎ ﻟﻢ ﻳﺘﺐ ﻣﻨﻬﺎ ﻟﻢ
ﻳﺸﺮﺑﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ” ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.
ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ -ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ-
ﻗﺎﻝ” :ﺍﺟﺘﻨﺒﻮﺍ ﺍﻟﺨﻤﺮ؛ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﻣﻔﺘﺎﺡ ﻛﻞ ﺷﺮ” ﻭﻗﺎﻝ
ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ.
ﻭﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺪﺭﺩﺍﺀ -ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ- ﻗﺎﻝ” :ﺃﻭﺻﺎﻧﻲ
ﺧﻠﻴﻠﻲ.. ﻭﻻ ﺗﺸﺮﺏ ﺍﻟﺨﻤﺮ؛ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﻣﻔﺘﺎﺡ ﻛﻞ ﺷﺮ ”
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ.
Lokacin da aka tambayi annabi (S)
hukuncin dabino idan aka tsima shi
sai ya ce: “Duk abinda ke bugar da
hankali ai giya ne”. Kuma ya ce:
“Duk abinda idan ya yi yawa yake
bugarwa to, kadan dinsa ma
haramun ne”.
Haka duk abinda ke bugar da jiki,
ya sa rauni, ya janye kuzari
sawa’un abinda ake ci ne ko ake
sha, ko wanda ake shaka ko
wanda ake yin allurarsa ko ta
kowace hanya yake kai ga jiki, shi
ma a matsayin giya yake.
Duk wanda ya kalli masu shan giya
da irin halin da take sa su ba zai yi
shakkar cewa, ita ce mafi
kaskancin abinda dan adam zai yi
kalaci da shi ba.
Imam Alqurdubi – Allah ya jikan sa
– ya ga wani mashayi yana fitsari
sannan ya dibi fitsarin yana wanke
fuska yana fadin: “Allahummaj’alni
minat tawwabin..!”
Shi ya sa Al-Hasan Al-Basri yake
cewa, in da ana sayar da hankali
da masu sayar da shi sun sayar da
haja mai tsada. Amma kash! Ga
wasu nan suna biyan kudi su gusar
da hankulansu.
Malam Dahhak bin Muzahim ya ce
ma wani mashayi, me ya yi maka
dadi ne wai a giya? Sai ya ce, tana
taimaka min wajen ruguza abinci.
Dahhak ya ce, abinda ta ruguza na
addininka da hankalinka ya fi
yawa.
Ya ku bayin Allah!
Kafin bayyanar manzon Allah (S)
giya na cikin ababen alfahari a
wurin balarabe. Zai sha giya ya yi
tatil, sai a kashe dare tare da shi
ana holewa. Ba kuma zai ji
damuwa ba sam idan a cikin
wannan daren ya rabe dukiyarsa
ga banbadawa da maroka.
Har a jikin Ka’aba sun lika waken
Amr bn Kulthum wacce ya fara ta
da yabon giya.
Zuwan manzon Allah (S) ke da
wuya sai musulunci ya dauki
matakin hana ta. Saboda me?
Saboda giya ba ta taba haduwa da
madara.
A lokacin da annabi (S) ya yi isra’i
an kawo ma sa kwarya biyu; ta
madara da ta giya. Sai (S) ya dauki
kwaryar madara ya kafa kai ya sha.
A nan ne Jibril (AS) ya kada baki
ya ce ma sa: “Ka shiriya, kuma
al’ummarka ta shiriya. Amma da ka
dauki giya da ka halaka, ita ma
al’ummarka da ta halaka”.
Kenan babu wata al’ummar da za
ta rabauta matukar jagororinta
suka zamo yan giya. Madara tana
nuni ne ga lafiyayyen abinci na
masu hankali.
Allahu akbar! Ita dai giya ba ta
cikin dabi’un mummuni sam sam.
Shi ya sa manzon rahama (S) yake
cewa:
” ﻻ ﻳﺰﻧﻲ ﺍﻟﺰﺍﻧﻲ ﺣﻴﻦ ﻳﺰﻧﻲ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ، ﻭﻻ
ﻳﺴﺮﻕ ﺍﻟﺴﺎﺭﻕ ﺣﻴﻦ ﻳﺴﺮﻕ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ، ﻭﻻ
ﻳﺸﺮﺏ ﺍﻟﺨﻤﺮ ﺣﻴﻦ ﻳﺸﺮﺑﻬﺎ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ” ﺭﻭﺍﻩ
ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.
Da irin wannan karantarwar ce
manzon Allah (S) ya canja rayuwar
larabawa daga shiririta da
tabargaza zuwa karantarwa da
jihadi.
Abu Mihjan da ya kasance a
jahiliyya yana cewa, ko mutuwa ya
yi a rufe shi kusa da bishiyar
dabino don ya rinka jin kanshin
giyar dabino a kusa da shi:
ﺇﺫﺍ ﻣﺖ ﻓﺎﺩﻓﻨﻲ ﺇﻟﻰ ﺟﻨﺐ ﻛﺮﻣﺔ
ﺗﺮﻭﻱ ﻋﻈﺎﻣﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻤﺎﺕ ﻋﺮﻭﻗﻬﺎ
ﻭﻻ ﺗﺪﻓﻨﻨﻲ ﺑﺎﻟﻔﻼﺓ ﻓﺈﻧﻨﻲ
ﺃﺧﺎﻑ ﺇﺫﺍ ﻣﺎ ﻣﺖ ﺃﻻ ﺃﺫﻭﻗﻬـﺎ
Sai ga wannan bawan Allah –
bayan musuluntar sa – ya bar giya
har abada saboda ta zamo ma sa
sarka mai hana yin jihadi.
Ya ku bayin Allah!
Giya da sauran ababen da ke sa
maye na da mugun tasiri ga dan
adam ta fuskar addininsa da
lafiyarsa da tattalin arzikinsa da
zamantakewarsa da jama’a bayan
ta rushe masa hankali da tunani, ta
tafi da karfin jikinsa.
Ta fuskar addini dai, shan duk
abinda ke kau da hankali ko
shakarsa babban zunubi ne da
saba ma Allah. Kuma yana cikin
abinda ke janyo fushin Allah da
gaggauta ukubarsa ga mutum a
nan duniya kafin lahira.
Maye na nisanta mutum daga
Allah, ya kusantar da shi ga
shaidan, ya hana shi tsaida sallah
bale sauran zikirin Allah da ibada.
Haka kuma maye na canja halin
mutum ya mayar da shi mai kuncin
zuciya, mai saurin fushi, mai rashin
kunya. Idan ya dage a kan sa
kuma take ya zama mayaudari,
mai cin mutunci da saba alkawari
da zubar da mutunci da rashin
gaskiya.
Ta fuskar tattalin arziki babu mai
hasara kamar wanda ke kashe
kudinsa a kan abinda ke cutar sa.
Watakila ma ya samo kudin da
wahala da dankaren aiki amma ya
je ya sawo abinda ke halaka shi da
kudin.
Ta fuskar zamantakewa kuma,
maye na wargaza gidaje ta hanyar
lalata aure, da rusa sana’a, ya
gadar da zaman banza da lalaci da
sata. Wani lokaci har mashayi ya
kan kai ga yin fashi da makami.
Daga karshe ya tozarta a duniya,
ga kuma azabar Allah tana jiran sa
a alkiyama.
Ga lafiya kuma, maye na gusar da
hankali, ya lalata tunani, ya
raunana jiki da mazakuta, ya bude
kafar kamuwar mutum da curutoci
iri daban daban. Allah ya kare mu.
Me ya sa aka kira giya da ummul
khaba’is?
Imamun Nasa’i ya ruwaito hadisi
cewa, sayyidina Uthman (RA) ya yi
wata huduba a lokacin da yake
halifa inda yake cewa: “Ya ku
mutane! Kashedin ku da shan giya,
domin ita ce uwar sharri gaba
daya. Sannan ya ba da labarin
mutumin da wata karuwa ta yi ma
sa zoba ta ce, sai ya yi alfasha da
ita ko ya kashe wani jinjiri a gidan
ko ya kurba giya. Da ya ga ba shi
da wata mafita sai ya dauka cewa,
shan giyar ya fi sauki. Amma da ya
kwankwade ta har ya bugu sai ya
kashe jinjirin kuma ya yi alfasha da
wannan mata.
Wannan shi ya sa Allah (Tabaraka
Wa Ta’ala) ya la’ance ta, ya la’anci
mai shan ta da masu taimakawa
wajen sarrafa ta da yada ta.
Annabi (S) ya ce:
” ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺨﻤﺮ، ﻭﺷﺎﺭﺑﻬﺎ، ﻭﺳﺎﻗﻴﻬﺎ، ﻭﻣﺒﺘﺎﻋﻬﺎ،
ﻭﺑﺎﺋﻌﻬﺎ، ﻭﻋﺎﺻﺮﻫﺎ، ﻭﻣﻌﺘﺼﺮﻫﺎ، ﻭﺣﺎﻣﻠﻬﺎ،
ﻭﺍﻟﻤﺤﻤﻮﻟﺔ ﺇﻟﻴﻪ” ﻭﻫﻮ ﺣﺪﻳﺚ ﺣﺴﻦ .
Kuma ya ce:
” ﻣﻦ ﺷﺮﺏ ﺍﻟﺨﻤﺮ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ، ﺛﻢ ﻟﻢ ﻳﺘﺐ ﻣﻨﻬﺎ،
ﺣﺮﻣﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ” ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
Ya kuma kara da cewa:
” ﻣﺪﻣﻦ ﺍﻟﺨﻤﺮ ﺇﻥ ﻣﺎﺕ، ﻟﻘﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﻌﺎﺑﺪ ﻭﺛﻦ” ﺭﻭﺍﻩ
ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺭﺟﺎﻟﻪ ﺭﺟﺎﻝ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ.
Ga kuma hadisin da Muslim ya
ruwaito:
” ﻛﻞ ﻣﺴﻜﺮ ﺣﺮﺍﻡ، ﺇﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ـ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ـ ﻋﻬﺪﺍ
ﻟﻤﻦ ﻳﺸﺮﺏ ﺍﻟﻤﺴﻜﺮ ﺃﻥ ﻳﺴﻘﻴﻪ ﻣﻦ ﻃﻴﻨﺔ ﺍﻟﺨﺒﺎﻝ،
ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﺎ ﻃﻴﻨﺔ ﺍﻟﺨﺒﺎﻝ؟ ﻗﺎﻝ: ﻋﺮﻕ
ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ، ﺃﻭ: ﻋﺼﺎﺭﺓ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ” ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
Masu shan taba sigari idan ana
maganar ‘yan giya kada ku dauka
ana magana da wasu mutane da
suka banbanta da ku banbanci mai
nisa. Domin kuwa duk illolin da
suka sa shari’a ta haramta giya
akwai kwatankwacinsu a cikin
sigari.
Bincike ya tabbatar da cewa, zukar
taba sigari na sa bushewar zuciya,
kari a kan curotuci masu dinbin
yawa da yake sabbabawa ga baki
da zuciya da tsarin tafiyar nunfashi
da na mafitsara. Kuma shi ne
babban abin da yake kawo kansar
koda. Haka kuma shan sigari na
sabbaba bugun zuciya da ciwon
hanta da hawan jini da rubewar
datanna (pancreas) da kuma
mutuwar sashen jiki.
Kada ku ga na faifaye ya ku yan
uwa musulmi. Akwai wadanda
suka lissafa hatsarin taba sigari da
illolinta har guda 120. A nan na
kawo guda goma ne kawai.
Sannan abu ne da kowa ya sani
cewa, shan taba yana zubar da
girma da mutuncin mutum a idon
jama’a.
Ta fuskar adadin mashayanta,
alkaluman kididdiga sun yi nuni da
cewa sama da mutane maza da
mata miliyan dubu daya da dari
biyu da ashirin (1,220,000,000) ke
shan taba a sassan duniya.
Wannan ya nuna kenan a cikin
kowane mutun dubu daya a duniya
akwai mashaya sigari 165. Daga
cikin su a kowace shekara sama
da mutane miliyan hudu ne masu
zukar ta take hallakawa.
Kasancewar akwai sugar a cikin
abubuwan da ake hada sigari da
su ya sa ta fi zama hatsari ga masu
ciwon sukari.
A cikin karen sigari 5 ana iya
samun sanadarin Necotine da ya
isa ya halaka dan adam in da zai
tattauna shi ya hadiye.
Sigari tana dauke da sama da
sanadarai 50 da ke iya kawo
kansa.
Mashayan sigari na da wasu
halaye da suka banbanta da na
masu cikakken hankali.
Mai shan sigari ba kansa kawai
yake cuta ma ba. Cutarsa tana kai
har ga iyalinsa da abokansa da
makwautansa. Kai, har da jinjirin
da ke cikin ciki idan ana hura
hayakin sigari yana shiga cikin
cikin uwarsa zai cutu da wannan
hayakin sigari.
Sanin wannan hatsari da taba
sigari take dauke da shi ya sa
makiyan musulunci suka taru suka
zayyana yadda za su kwararo da
ita a cikin duniyar musulmi. Ga
gyara tattalin arzikinsu ta hanyar
kwashe dukiyarmu, ga kuma biyan
bukata; ita ce lalata hankalinmu da
tunaninmu ta yadda zamu yi saukin
zama bayi a hannunsu.
Ba ni zaton bayan samun
wadannan bayanai akwai wanda
ke shakkar cewa shan taba sigari
haramun ne a shar’ance. Sai fa
idan mutum bai da masaniya sam
sam ga manufofin shari’ar
musulunci.
Wasu hukunce-hukuncen shari’a
da suka shafi mashaya sigari. Mun
dauko su daga cikin littafin
ﺍﻷﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ ﺍﻟﻤﺘﻌﻠﻘﺔ ﺑﺎﻟﺘﺪﺧﻴﻦ
Na Sheikh Ahmad bn Muhammad
bn Atiq, alkali a kotun shari’a da ke
Riyadh.
1. Makaruhi ne mashayin sigari ya
yi kiran sallah ko ya bada sallah.
Amma haramun ne a nada shi
alkali.
2. An hana duk wanda ke shan
sigari shiga cikin masallaci tare da
jama’a matukar akwai warin sigari
tare da shi.
3. Malamai da dama sun tafi a kan
cewa, ba a karbar shedar mashayi
a ganin wata da sauran hukunce-
hukunce saboda hukunci da
fasiccinsa.
4. Haramun ne ayi aikin hajji da
kudin da aka samu ta hanyar
cinikin sigari.
5. Duk wata hanya da zata taimaka
a kan sigari ita ma haramun ce
kamar noma ta ko sayar da ita ko
bada shago haya don a sayar da
ita ko dako da saukalen ta ko
sayen hannun jari a kamfaninta ko
makamancin haka.
6. Shan sigari na cikin ayubban da
ke sa a warware aure. Idan mace
ta kai karar mijinta saboda ya fara
shan sigari bayan aurensu za a
raba auren a bar mata sadakinta.
Amma idan ta kai karar sa alhali ta
same shi yana shan sigari, za a
warware auren amma ta maida
masa da sadakinsa.
7. Wajibi ne ga hukumomi su yi
doka don hana shan sigari a
wuraren zaman jama’a kamar
dakin taro ko cikin aji ko motar
haya ko gidan abinci ko
makamancin haka.
8. Haka kuma wajibi ne a yi doka
da za ta hana kafafen watsa
labarai tallata sigari gaba daya kai
tsaye ko a kaikaice kamar shan ta
a cikin finafinai.
Ya kai dan uwana musulmi wanda
Allah ya jarabta da shan sigari!
Dan tsaya kadan ka yi wa kanka
hisabi. Ka sani ko ba ka yi ba za a
yi maka shi gobe kiyama. Lissafa
ka gani tun daga sadda ka fara
shan taba zuwa yau kimanin nawa
ne ka kashe a kan ta? Ko ka san
wanda yake shan taba ta N50 a
kowace rana, cikin shekara biyu
kacal ya kashe N36,500 a kan
iska?! A shekara goma wannan
mashayin ya kone N180,250
Nawa ne ka kashe kai?
Kana tsammanin ka yi wa kanka
adalci cinna ma wadannan
makudan kudi wuta?
Ko kuma Allah na kyale ka kana
kone arzikin da ya hore ma ka
alhalin ga mabukatansa nan birjik
kamar ruwan zamzam a Makka?
Ya zaka kalli wanda ya dauko kudi
zunzurutu har N180,250 a wannan
hali da bayin Allah suke ciki a
bainar jama’a ya kunna masu
ashana? Kana yi masa kallon mai
hankali?
Ka tuna shi idan ya kona kudin zai
koma gidansa ya kwanta lafiya lau
ba abinda ya cuce shi. Kai kuma
kana kona su ne a cikin zuciyarka,
kuma karan kake konawa amma
kudin kana zura su ne a cikin
asusun ajiyar kamfunan sigari
wadanda kaffataninsu na makiyan
Allah ne makiyan musulmi masu
kashe muna yan uwa a Falasdinu
da sauran wurare. A nan yana da
kyau ka sani cewa, hukumar yaki
da miyagun kwayoyi da ke
karkashin majalisar dunkin duniya
ta kiyasta kudaden da kamfunan
sigari da sauran miyagun ababen
hadiya suke samu da cewa, ya kai
dalar amurka miliyan dubu dari
hudu a shekara (Tasar ma tiriliyon
bakwai na kudin Najeriya kenan,
budget dinmu na shekara biyu). Da
kai a cikin masu zuba wannan
jarin.
Idan kana yi ma wancan da ya
kone kudinsa kallon mahaukaci, su
kuma jama’a ya ya kake son su
kalle ka?
Saboda haka, yi maza ka shata ma
kanka hanyar rabuwa da wannan
bala’i.
Ya kai mai sayar da aswakin
shedan! Ka amince duk zunubin
masu zukarta ana rabawa da kai?
Kai ma ka gaggauta canza sana’a
don maslahar kanka.
Wanda ya san kuma ya zuba jari a
wani kamfani da ke sarrafa irin
wadannan abubuwa na maye shi
ma ya tsarkake dukiyarsa don
rayuwarsa da ta iyalansa da ke cin
abinci a ciki ta yi albarka.
Ya ku yan uwa magidanta!
Babban kalubalen da yake a
gabanmu a yau shi ne na yaran da
suka wuce zancen sigari, suka fara
shake-shake da kurbe-kurbe na
ababen da tun asali ba a yi su don
kwankwadar dan adam ba. Ko
kuma ababen da an yi su don
maganin wasu curutoci amma
saboda lalacewar rayuwa
wadannan matasa suka mayar da
su ababen sha da shakawa don su
kawar da hankalinsu. Irin
wadannan matasa da zaran sun
kai wani mataki al’umma tana iya
hasarar su gaba daya. Abin da duk
ya fi ban takaici kuma shi ne
wadanda ke da alhakin samar da
wani mataki na gyaran su, su ke da
bukata da lalacewar su. Sai dai mu
ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Daga karshe ina ba da shawara ga
wadanda abin ya shafa a shigar da
zancen shan giya da illolinta da
dangoginta kamar sigari da we-we
da tetolin da makamantansu a cikin
syllabus na karatun yaranmu tun
daga firamare don bada kariya
gare su tun da wuri.
Ya ku bayin Allah! Mu tuba zuwa
ga Allah gaba daya kamar yadda
madaukakin sarki ya kira mu da
cewa:
(( ﻭﺗﻮﺑﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ ﻟﻌﻠﻜﻢ
ﺗﻔﻠﺤﻮﻥ)).
Leave a Reply