HUKUNCE-HUKUNCEN ZAKKAR
FIDDA KAI!!!
Imamul Bukhari ya ruwaito hadithi
na 1503 da Imamu Muslim a
hadithi na 984 daga Abdullahi Dan
Umar cewa: ((Manzon Allah Mai
tsira da amincin Allah ya farlanta
zakkar fidda-kai sa’I daya na
dabino, ko sa’I daya na sha’ir, a
kan bawa, da da, da namiji, da ta-
mace, da karami, da babba, daga
cikin Musulmi, ya yi umurni a fidda
zakkar kafin fitar mutane zuwa
sallar idi)).
Sannan ita Zakkar fidda-kai tana
zama wajibi ne a kan Musulmi a
lokacin faduwar rana a yinin
karshe na watan Ramadhan,
saboda haka dukkan wanda ya
musulunta ko aka yi masa haifuwa
kafin faduwar ranar wannan yini,
to, zakkar fidda-kai ta zama wajibi
a kansa, wanda kuma ya
musulunta ko aka yi masa haifuwa
bayan faduwar ranar wannan yini,
to, zakkar fidda-kai ba ta zama
wajibi ba a kansa. Mutumin da ya
zamanto bai mallaki abin da zai
bayar na zakka ba a lokacin da
zakkar ta zama wajibi, to, zakkar ta
fadi a kan sa ke nan har abada.
Wannan shi ne mazhabar
Shafi’iyya, da Hambaliyya, da
Malikiyya cikin wata riwaya. Amma
a wurin Hanafiyya, da kuma
Malikiyya cikin wata riwayar,
Zakkar tana zama wajibi ne a
lokacin hudowar alfijir na yinin Idi.
HUKUNCE-HUKUNCEN RANAR
IDI:
Abu ne da yake mustahabbi;
al’ummar Musulmi su rika yin
kabbarori a bayyane a daren Idin
karamar salla da Idin babbar salla,
su yi kabbarorin a kan hanyoyinsu,
da cikin masallatansu, da
gidajensu, haka nan za su ci-gaba
da yin su a safiyar Idi har zuwa
masallaci, har zuwa lokacin da
liman zai fara yin huduba. Sannan
in gari ya waye sai su yi wanka, su
sanya tufafi masu kyau, su sanya
turare, su tafi masallacin idi suna
kabbara kamar yadda muka fada,
idan Idin karamar salla ne, to,
mustahabbi ne su karya da dabino
daya, ko uku, ko fiye da haka a
bisa adadi mara, kafin su tafi Idi, in
kuma idin Layya ne to, kada su
karya sai bayan Sallar Idi. Kuma
Sunna ce mai karfi; dukkan mata
su fita zuwa masallacin Idi, Imamul
Bukhari ya ruwaito hadithi na 351
da Imamu Muslim hadithi na 890
daga Ummu Atiyya ta ce:
“Manzon Allah Mai tsira da amincin
Allah ya umurce mu da mu fidda
mata zuwa Idin karamar salla, da
Idin babbar salla; ‘yan mata, da
masu haila, da ma’abuta khuduri
(matan aure), to, amma su masu
haila sai su nisanci salla, su halarci
alkhairi da addu’ar musulmi. (ta ce:
Sai) na ce: Ya Manzon Allah! Daya
daga cikimmu ta yiwu ba ta mallaki
mayafi ba. Sai ya ce: Sai ‘yar
uwarta ta ba ta aron mayafi”.
Kuma yana da kyau idan aka gama
sauraron huduba za a koma gida a
sake hanya, Imamut Tirmithi ya
ruwaito hadithi na 542 da Imam
Ibnu Maja hadithi na 1317, kuma
Albani ya inganta shi cikin Sahihu
Sunani Ibnu Majah 1/390 daga
Abu Huraira cewa “Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ya
kasance idan ya tafi idi ta wata
hanya, to, ya kan dawo ta wata
hanya daban”.
Da Fatan Za’ayi Sallar Idi Lami
Lafiya, Aci Shinkafa Kaza Cikin Jin
dadi da Annushuwa, Abokaina Sai
Mun Sake Haduwa da yardan
Allah.
Leave a Reply