Assalamu alaikum.
1. Hadisi ya inganta cewa:
Babu Wani Musulmi Wanda Zai Dasa Wani Dashe Ko Ya Shuka Wata Shuka, Sai Wani Tsuntsu Ya Ci Daga Gareshi, Ko Wani Mutum Ko Wata Dabba Face Ya Na Zama Wata Sadaka Ce Gare Shi” a wata riwayar MUSLIM: 1552, Annabi ya ce a na samun lada har ta satar amfanin gonar.
[SAHI’HUL BUKHA’RI; 2320, MUSLIM; 1553]
2. Babu kyau a kashe ķwari marasa cutarwa, kuma babu laifi a kashe idan an damu da su, idan babu wata mafita sai ta hakan. [AL-A’DA’BUSH SHAR-IYYA; 3/354]
3. Halal ne a kashe tururuwa ko ƙwari da kowace halitta mai cutarwa a gida ko gona, kuma a na iya amfani da komai, idan dai ba wuta ba ce. [FATA’WA ISLA’MIYYA; 4/451, FATA’WA IBNI BAZ; 5/301]
4) Babu laifi a yi amfani da wutar lantarki na shocking đin ƙwari don kashesu, idan su na cutarwa. [FATA’WAL LAJNATID DA’IMA; 26/192]
Leave a Reply