Tambaya: Shin yin Bismillah lokacin yin alwala wajibi ne? Idan Mutum baiyi ba alwalarsa babu?
Amsa: Ansamu tsabani tsakanin Maluma game da wajabcin yin Bismillah yayin alwala. Mafi yawan Malamai sun tafi kan cewa ba wajibi bane, Sunnah ne, sabida haka idan mutum baiyi ba don mantuwa ko da gangan alwalarsa tayi, sai dai yin Bismillar itace tafi dace wa, kuma bai dace mutum ya bar yinta ba da gangan. Wasu Maluman kuma sun tafi akan cewa yin Bismillah wajibi ne.
Dalili wa’inda sukace ba wajibi bane: Tirmidhi ya rawaito hadisi 302
Annabi Ya koya wa wani alwala, sai yace masa kayi Alwala kamar yadda Allah ya umarceka.
Wannan yana nuni ne zuwa ga aya dake cikin Suratul-Ma’ida aya ta 6. Wanda acikin ayan Allah yayi bayanin rukunan alwala, amma kuma bai kawo Bismillah aciki ba, domin inda wajibi ne da yayi bayaninsa.
Haka nan mafi yawancin wa’inda suka siffanta Alwalar Annabi Sallallahu alaihi wasallama basu kawo Bismillah aciki ba. Hakan yake nuna Ba wajibi bane, sunnah ne.
Dalilin wa’inda sukace wajibi ne: an rawaito hadisi daga Manzon Allah yace:
Babu Alwala ga wanda bai ambaci sunan Allah.
Sai dai wannan Hadisi maluma sunyi bayani akan cewa bai inganta ba. Koda ma ya inganta ba yana nunin cewa mutum bashi da alwala bane gabadaya, ana nufin Bashi da alwala cikakkiya, sabida kamar yadda mukayi bayani a baya Sahabbai da yawa sun rawaito yadda annabi Yake alwala, da yawa daga cikinsu basu rawaito da Bismillah ba.
Abin Lura: Idan mutum zaiyi alwala yana da kyau yayi Bismillah, kuma hakan zaisa ya samu karin lada, bai dace mutum yaki yin Bismillah yana sane ba sai dai in ya mance. Idan mutum ya mance ko kuma baiyi ba alwalarsa tana nan. Wannan shine magana mafi inganci.
Allah shine mafi sani.
Domin neman karin bayani zan sanya wasu links a kasa ga wanda yakeson yaga zantukan malamai Game da wannan Mas’ala.
Hukuncin Bismillah a alwala(Islamqa)
Hukuncin Bismillah a alwala(Sheikh Bin Baz)
Leave a Reply