Yana daga cikin lokuta wanda ake son Musulmi yayi addu’a aciki ɗayan bisa ukun dare. A lokacin ne Allah Maɗaukaki sarki yake saukowa zuwa ga saman duniya( Irin sauƙa wacce ta dace dashi) yace:
Waye zai ƙirani na amsa masa?
Waye zai roƙeni in bashi?
Waye zai nemi gafara ta na gafarta masa?
Wannan hadisi bukhari da Muslim sun rawaito shi.
يَنْزِلُ رَبُّنا تَبارَكَ وتَعالَى كُلَّ لَيْلَةٍ إلى السَّماءِ الدُّنْيا، حِينَ يَبْقَى ثُلُثُ اللَّيْلِ الآخِرُ فيَقولُ: مَن يَدْعُونِي فأسْتَجِيبَ له، مَن يَسْأَلُنِي فَأُعْطِيَهُ، مَن يَسْتَغْفِرُنِي فأغْفِرَ له.
البخاري: 7494
مسلم: 758
Haka nan Muslim ya rawaito daga hadisin Jabir Allah ya ƙara masa yarda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:
عن جابر قال سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول إن في الليل لساعة لا يوافقها رجل مسلم يسأل الله خيرا من أمر الدنيا والآخرة إلا أعطاه إياه وذلك كل ليلة
مسلم : 757
Manzon Allah yace acikin dare akwai wani lokaci wanda babu wani bawa Musulmi da zai dace da shi kuma ya roƙi Allah wani alheri na duniya da lahira face Allah ya bashi abinda ya roƙa. Kuma wannan lokaci ana samunsa a kowani dare.
Wannan ba ƙaramin garaɓasa bane da mumini ya dace ya ribata. Ta yadda Allah da kansa yake ƙiran bayinsa da su roƙeshi.
Idan kana da buƙata ka tashi a wannan lokaci ka roƙi Allah kana mai yaƙini, Insha’Allah zaka ga Abin mamaki.
Sannan kuma yana da kyau in zakayi addu’ar kayi a sujada. Kaga ansamu sabuba biyu kenan na ƙarɓan addu’a. Ga lokaci, ga kuma Guri.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply