KA TABA YIN ZINA?(Malam Aminu Ibrahim Daurwa)

Zina tana cikin manyan laifuffuka,
wanda dukkan shariun da Allah
taa’la ya saukar sun hadu akan
haramcin zina,
Al kur’ani mai girma da Sunnar
Annabi saw, da dukkan Malamai
sun hadu akan haramcin zina,
Kofofin zina guda biyar ne
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya
Haramta
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- kebancewa da matar da ba
muharrama ba,
5- Shaawa Mai karfi babu aure
Allah taala yace: ” kada ku kusanci
zina”
Manzon Allah saw yace : Mai zina
ba zaiyi zina ba, yayin da yake
zina, sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas’ud Ra yace :
Duk Al’ummar da take zina, ta jawo
wa kanta fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare
abubuwa biyar, sune : Addini,
Dukiya, Rayuka, Hankali, Mutunci,
Nasaba, amma zina ita kadai, tana
rusha wadannan duka,
Hukuncin mazinaci, mai aure kisa
ta hanyar jifa, mara aure Bulala
dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku,
shedu guda hudu, Mutun yayi
ikirari da kansa, samun mace da
ciki, babu aure, ko shubha. Bisa
sharudda da aka sanyawa ko
wanne.
Zina wata babbar musifa ce da
bala’i da dukkan sharri, da take
ruguza al’umma, take wargaza
iyali, take tarwatsa gari, take rushe
mutunci, take jawo karayar tattalin
arziki, da fatara, da tsiya, da
annoba, a cikin rayuwar dai dai ku,
da gidaje, da unguwanni, da
gururuwa, da kasashe, da duniya
baki daya,
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin
zina ake samun dukkan sharri
kamar :
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12-Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- cikawa babu imani
16- Azabar Allah
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da
dukkan al’ummar musulmi daga
afkawa zina, wadanda suke yi
Allah ya shirye su.

Click Here to Support our work

12 Comments

  1. malam ni dalibine na daya daga cikin jami,o,in kaduna ina degreena nabiyu ammafa bansamu aikiba haryanzu kuma ni wallahy ina mutukar son nayi aure. dan Allah atallatani ko Allah zaisa nasamu wacce iyayenta zasu iya karbar sadaki kawai donna na aureta. babu wata matsala abinda yashafi abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: