AL'AWRA GA MACE(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)

·

·

Watau duk abunda zai ja hankalin
namiji zuwa ga son mace ko
sha’awarta to wannan haramun ne
ga mace da ta bayyana shi zuwa
ga namiji ko mace mai sha’awar
mata.
Ita fuska da tafin hannu ba alawra
bane a wurin sallah amma wurin
mutane sai da sharadin basu fitinar
mai kallonsu, amma a wannan
zamani na fitina, mace ta fi kowa
sanin abunda ya kansa maza su
kalleta da sha’awa, saboda haka
ya zama wajibi ta suturtashu kuma
babu banbanci tsakanin mai aure
da marassa aure. Wannan kuwa
kamar yadda manzon Allah – tsira
da amincin Allah su tabbata
agaresa – yace:
ﻟﻜﻞ ﺍﺑﻦ ﺁﺩﻡ ﺣﻈﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺰﻧﺎ ﻓﺰﻧﺎ ﺍﻟﻌﻴﻨﻴﻦ ﺍﻟﻨﻈﺮ
ﻭﺯﻧﺎ ﺍﻟﻠﺴﺎﻥ ﺍﻟﻤﻨﻄﻖ ﻭﺍﻷﺫﻧﺎﻥ ﺯﻧﺎﻫﻤﺎ ﺍﻻﺳﺘﻤﺎﻉ
ﻭﺍﻟﻴﺪﺍﻥ ﺗﺰﻧﻴﺎﻥ ﻓﺰﻧﺎﻫﻤﺎ ﺍﻟﺒﻄﺶ ﻭﺍﻟﺮﺟﻼﻥ ﺗﺰﻧﻴﺎﻥ
ﻓﺰﻧﺎﻫﻤﺎ ﺍﻟﻤﺸﻰ ﻭﺍﻟﻔﻢ ﻳﺰﻧﻰ ﻓﺰﻧﺎﻩ ﺍﻟﻘﺒﻞ ) ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ،
ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻰ ﻓﻰ ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﻋﻦ ﺃﺑﻰ ﻫﺮﻳﺮﺓ)
“Kowane dan Adam yana da nashi
rabo na zina. Zinar idanu biyu itace
kallo, zinar halshe Magana, kuma
kunaye biyu zinarsu saurare,
hannaye biyu suma suna zina,
zinarsu kuwa itace kamawa, kuma
kafafu biyu suna zina, kuma zinar
su itace tafiya, kuma baki yana
zina, kuma zinarsa itace
sumbunta”
Allah Ya taimake mu da matan
musulmi wurin bin abinda shine
alheri garemu duniya da lahira.
Amin.

One response to “AL'AWRA GA MACE(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)”
  1. UMAR ADAMU FASKARI Avatar
    UMAR ADAMU FASKARI

    Allah yasaka da alkhairi

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: