Wa’innan abubuwa huɗu da zan lissafa yana da kyau Musulmi ya dawwama akansu matuƙar yana numfashi.
• Kada kabar godiyar Allah, domin kada Allah ya hana ka ƙarin falalansa: godewa Allah yana daga cikin abinda mutane suke mance wa dashi sosai, kuma godiya ga Allah yana daga cikin sababin ƙarin ni’imah daga Allah, sannan rashinsa yana janyo gushewar ni’ima. Allah yace:
وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكُمْ لَئِن شَكَرْتُمْ لَأَزِيدَنَّكُمْ ۖ وَلَئِن كَفَرْتُمْ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٌ
kuma alokacin da ubangijinku ya sanar da cewa idan kuka gode masa zaiyi muku ƙari, idan kuma kuka kafirce wa ni’imansa haƙiƙa azabarsa na da raɗaɗi.
Surat-Ibrahim: 7
Ya dace Musulmi ya kasance mai godiyar Allah a kowani lokaci domin Ni’imomi da Allah yayi masa basu ƙirguwa, sannan kuma kafirce wa Ni’imar Allah na janyo azabar sa.
• Kada ka bar Ambaton Allah: Ambaton Allah na daga cikin Aiki mai sauƙi wanda ke janyo Yardar Allah da kuma kariyar Allah, kuma bashi da wahalar aikatawa. Ya ishe Musulmi farin ciki yasan cewa idan ya ambaci Allah, Allah zai ambace shi. Allah yace:
فاذكروني أذكركم
Ku ambace ni, zan ambace ku.
Suratul-baqara: 152
• Kada kabar Addu’a: a koyaushe ka kasance mai roƙon Allah, domin Allah yana son masu roƙonsa, kuma shi addu’a shine ginshikin ibada, sannan mai yin addu’a baya asara, kodai Allah ya baka abinda ka nema, ko ya baka wanda ya fishi, ko kuma ya tunkuɗe maka wani musiba da ta tunkaro ka.
Allah yace:
ادعوني أستجب لكم إن الذين يستكبرون عن عبادتي سيدخلون جهنم داخرين
ku roƙeni zan amsa muku, haƙiƙa wa’inda suke girman kai ga barin roƙo na zasu shiga wutan jahannama suna masu dawwama aciki.
Surat-ghafir: 60
• Kada kabar istigfari: istigfari yana daga cikin sabuban tsira da kuma samun nasara a duniya da lahira. Kuma yana kau da azabar Allah a duniya da lahira. Allah yace:
وما كان الله معذبهم وهم يستغفرون
Allah bai kasance mai azabtar dasu ba a halin sun kasance masu istigfari.
Allah yasa mudace, ya bamu daman lazimtar Wa’innan abubuwa.
Leave a Reply