Ku dubi na ƙasa daku, kada ku dubi na sama daku hakan zai taimaka muku wurin godiya wa Allah

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa:

” ku kalli wanda ke ƙasa daku, kada ku kalli wanda ke sama daku, hakan zaifi saku kada ku Raina Ni’imar da Allah yayi muku.”

-Muslim


A wannan hadisi annabi yana kira ne ga Musulmi a kullum ya rinƙa duba wanda bai kaishi falala ba, kada ya rinƙa ɗaga kansa yana kallon wanda Allah ya bashi falala fiye da nashi, domin a duk lokacin da mutum ya yawaita kallon na sama dashi toh hakan zaisa ya rinƙa raina Ni’imomi da Allah yayi masa, kuma haka zaisa ya kasa gode wa Allah, kuma rashin godiya ga Allah yana kawo gushewar Ni’imah, yin godiya ga Allah kuma yana kawo yalwantar Ni’ima. A ko wani hali ka samu kanka in ka duba zaka ga cewa akwai wanda ka fishi, toh ka kalli wannan wanda ka fishin kallo na Tadabburi, sai ka godewa Allah kan wannan Ni’imah da Allah yayi maka, kuma Allah zai ƙara maka. Kamar yadda ya bada labari.
وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكُمْ لَئِن شَكَرْتُمْ لَأَزِيدَنَّكُمْ ۖ وَلَئِن كَفَرْتُمْ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٌ

Allah yace:

Tuna lokacin da Allah ya sanar da cewa idan kuka min godiya kan Ni’imomi da nayi muku toh haƙiƙa zanyi muku ƙari, haka nan kuma idan kuka kafirce wa ni’ima ta toh Haƙiƙa Azaba ta tana da tsanani.

-Surat Ibrahim 7

Idan mutum ya dubi Ni’imomin da Alla yayi masa bazai iya ƙirguwa ba, sabida haka ya dace kullum musulmi yakasance cikin godiya ga Allah cikin jin daɗi da kuma tsanani, hakan zai sa ya samu yalwantar Ni’imomin Allah, sannan kuma hakan zai ƙara wa mutum lafiyar zuciya da jiki. Ta yadda zai samu kwanciyar hankali da natsuwa domin yasan duk abinda Allah ya kasa ya bashi zai sameshi, sai dai kawai ya kyautata nema.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories