KAMEWA DA KAWAICI KAMALA
NE:
Musulmi yana da daraja bisa
baiwar da Allah yayi masa ta
ni’imar musulumci, kuma muna da
kyak-kyawan abin koyi daga
halaye na karimci, mutumci, da
nagarta daga Annabin mu
Muhammad saw. Sahabban
Manzon Allah masu daraja sun
sami tarbiyya daga farin jakada
Annabi saw, hakanan sauran
magabata na kwarai Allah ya kara
masu yarda.
Ana son musulmi ya zamo mai
halin da’a, saukin kai, tsare
mutumci, gaskiya, amana, da koyi
da dukkan halayen kirki na
magabatn mu na kwarai. Pls mu
natsu mu nemowa kan mu amsar
wadannan tambayoyi mana:
1.Ina al’ummar mu ta yau suka
samo bayyana tsiraici ne?
2. Yaya ake samun marasa kunya
cikin magana da mu’amala cikin
mu ne a yau?
3. Shin shaye-shayen kayan maye
na cikin tarbiyya ta gari da ake son
musulmi na kwarai da ita?
4. Yaya dogon buri, alfahari da son
karya ya mamaye mu ne?
5. Shin Jin kida da waqe-waqe
halin kirki ne da ya samo asali
daga addini?
6. Sakin baki ana aibata masu
daraja da yawan zagin mutane hali
ne na managarta?
‘Yan uwa mu sani kowa sai ya
zubda ruwa zai taka damshi, kuma
duk wanda ya shuka alheri zai ga
sakamakon sa duniya da lahira,
hakanan duk wanda ya zabi
hannun haggu wajen gudanar da
rayuwar sa zai ga sakamakon
hakan anan duniya da gobe lahira.
Allah ya datar damu karshe mai
kyau, amin
Leave a Reply