A wannan zamani ana samun kiraye kiraye na cewa a haɗe addinai su zamto ɗaya. Ta yadda kowa zai bauta wa abinda yaga dama, kuma kada wani ya rinƙa zargin wani don yana bautan wani abu.
Wannan da’awah ce da take yaɗuwa cikin Al’ummar mu ta Musulmi, ta yadda wasu sun amshi wannan da’awah har ya kai ga suna iya taimakawa wasu mabiya addinai kan cigaban addinin su, haka nan sukan tayasu wurin aikata wasu abubuwa da suka shafi addininsun, haka nan koda sun mutu sukan nema musu gafara ba tare da lura da Abinda Shari’a ta tanadar ba.
Ya kamata mu sani cewa Addinin Musulunci shine kaɗai addini da Allah ya yarje wa bayinsa suyi. Duk wani addini da mutum zaiyi ba Musulunci ba toh Allah bazai karɓa masa ba. Allah yace:
إن الدين عند الله الإسلام
Addini a wurin Allah shine addinin musulunci
A wani wuri yace:
وَمَن يَبْتَغِ غَيْرَ الإِسْلاَمِ دِيناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ
Wanda ya riƙi wani addini ba addinin Musulunci ba toh Allah bazai karɓa masa ba, kuma a rananr ƙarshe zai kasance cikin masu hasara.
Aal emran 85
Wannan ayoyi biyu sun tabbatar mana cewa duk wani addini da wani zai mutu akai ba addinin musulunci ba toh Allah bazai taɓa karɓa masa ba.
An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa:
والذي نفس محمد بيده لا يسمع بي في أحد من هذه الأمة يهودي ولا نصراني، ثم يموت ولم يؤمن بالذي أرسلت به، إلا كان من أصحاب النار
مسلم 153
Annabi yayi rantsuwa yace: ina rantsuwa da wanda ran Muhammad ke hanunsa, babu wanda zaiji labari na acikin wannan Al’ummah( Yana nufin Ummatu-dda’awah) bayahude ne ko banasare, sannan kuma ya mutu baiyi imani da abinda aka turoni dashi ba face ya kasance cikin ƴan wuta.
Muslim: 153
Wannan hadisi ya ƙara tabbatar mana da cewa Addinin Musulunci shine kaɗai addini da Allah ke karɓa.
Ya kamata Musulmi ya lura sosai, ya kuma kauce wa irin wa’innan ƙiraye ƙiraye da akeyi. Domin ƙira ne don a lalata wa mutum addinin sa.
A lokacin da maƙiya addini suka ga cewa bazasu iya canza wa mutum addini ba toh sai sunyi iya ƙoƙarinsu wurin su sanya masa irin wa’innan tunanin, ta yadda zai kasance shi yana ganin kansa musulmi ne, Amma a haƙiƙa ba haka yake ba.
Sannan kuma ya kamata mu sani cewa addini ba da ra’ayi da son zuciya ake yinsa ba. Dole sai mutum ya koma zuwa ga abinda yazo a Al-Qur’ani ko kuma Sunnah, da haka ne mutum zai tsira kuma ya dace da daidai.
Sannan mu sani duk Tausayin mutum, da taimakon sa idan har ya mutu ba akan tafarkin addinin Muslunci ba toh makomansa wuta ne. Kuma bashi halatta musulmi wanda yayi imani da Allah da ranar ƙarshe ya nema masa gafara a wurin Allah, domin hakan tsaɓawa Allah ne, Allah ya fika sanin abinda ke cikin zuciyarsa domin shi ya halicce shi, kuma da yaga dama da ya shiryar dashi zuwa ga addinin Musulunci amma baiyi ba sabida hikima tasa.
Hukuncin nema wa kafiri gafara bayan mutuwarsa:
batun hana nema wa kafiri rahama bayan mutuwarsa abu ne wanda Al-ƙur’ani yayi bayaninsa a zahirance wanda babu wani ƙura akansa. Kuma ba’a samu tsaɓani kan hakan ba tsaƙanin maluma. Allah maɗaukakin sarki yace cikin Surat- Attaubah 113
مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَى مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ
Bai halatta ga Annabi da wa’inda sukayi imani dashi su nema wa Mushrikai gafara ba koda ko sun kasance makusanta ne, bayan ya tabbata garesu cewa su ƴan wuta ne.
Wannan ayah ta tabbatar da haramcin nema wa kafiri gafara. Kuma kamar yadda na faɗi cewa wannan abu ne sananne wurin Al’ummah babu mai jayayya akai sai maƙiyin gaskiya.
Allah yasa mudace, ya kuma kare mana Imaninmu.
Leave a Reply