Abinda ka shayar da yaronka yana karami dashi Zai tashi Iyaye ku kula da Tarbiyyar yayan ku

Ƴaƴa da Allah ya bamu Amana ne, kuma Allah zai tambayemu akansu kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya bada labari cewa ” Dukkanmu masu kiwo ne, kuma ko wanne daga cikinmu za’a tambaye shi kan kiwon da aka bashi”

A yanzu muna wani zamani ne mai cike da ban tsoro, Zamani ne mai cike da haɗarurruka masu yawa, da lalacewar Tarbiyya, sabida haka dole Musulmi ya zamto ya lura da halin da ake ciki, sannan dole ya sanya idanu kan Tarbiyyar yaransa da iyalansa baki ɗaya.

Sau da yawa iyaye basu damu da sanya idanu kan Halin da ƴaƴansu suke ciki ba, Musamman abubuwa da suke kallo, ko suke sauraro, zaka samu mahaifi zai saya wa ƴarsa ko ɗansa babbar waya ya bashi, amma bai damu da bincikan abinda

wannan ɗa ko ƴa suke aikata wa ba. Wannan babban kuskure ne, Idan bai zama dole ba idan har yaro bai girma ya mallaki hankalin kansa ba kada ma a saya masa waya, idan kuma ya zamto dole sai an saya masa sabida wasu dalilai to Ya zama dole a sanya masa idanu kan abubuwa da yakeyi, kada a barshi ya rinƙa shiga inda yaga dama, ya rinƙa magana da wanda yaga dama, domin daga haka shikenan zai iya faɗa wa wata hanya mummuna.

Wasu iyayen kuma sukan sayi Kayan kallo su sanya a ɗakin ƴaƴansu, basu damu da abinda ƴaƴan suke kallo ba, ko wasu tashoshi suke kama wa su kalla ba, wannan shima babban kuskure ne.

Domin Zasu iya suje su kalli wasu abubuwa da zasu ɓata musu ƙwaƙwale su halakar dasu.

Wasu iyayen kuma tun yara suna ƙananu su iyayen suke kunna wasu tashoshi ko wasu fina finai wa’inda basu dace ba, Kuma yaran suna gani, Daga haka yaran sai su tashi da wannan abin acikin ƙwaƙwalwarsu, su rinƙa ganin kaman abin yana da kyau.

Iyaye ku sani cewa shi yaro duk abinda ka sanya masa a ƙwaƙwalwa yana zama masa, sabida haka kuyi ƙoƙari wurin cusa alheri acikin zuƙatan ƴaƴayenku tun suna ƙananu, domin zasu tashi dashi.

Shiyasa akeso a fara koya wa yaro Al-Qur’ani tun yana ƙarami kafin ya kai wasu shekaru, domin hakan zai ƙara buɗa masa ƙwaƙwalwa ya ƙara fahimtar Karatu. Iyaye ku guji lalata ƴaƴanku da kallace kallace marasa ma’ana, Domin hakan zai sa su zama kasalallu marasa amfani, babu abinda suka iya sai kallo sai wasa da Shiririta.

Mu guje wa irin tashoshin Arewa 24 da makamantansu, domin babu wani alheri acikinsu. Idan har kunaso su kalli wani abu to ku nema musu abin kallo mai fasali mai ma’ana, da zasu amfana da kallonsa.

Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: