Saqon Musulunci wanda Manzon Allah (S.A.W.) ya zo da shi zuwa ga mutane da aljanu, manufarsa ita ce rarrabe tsakanin abubuwan da ke da kyau da kuma munana, don amfanin talikai baki daya. Wato a rarrabe tsakanin kadaita Allah wajen bauta da kuma akasin haka, ko tsakanin imani ingantacce da bin hanyar dagutu, ko kuma tsakannin bin tafarkin Manzon Allah (S.A.W.) da yarda da qirqirarrun al’amura. Babu shakka cewa saqon da Manzon Allah (S.A.W.) ya zo da shi ya fayacce wadannan masalolin da kuma makamantansu ya kuma shiryar da mutane zuwa ga miqaqqiyar hanya wadda babu karkata a cikinta. Sai dai kuma musulmi da suka biyo baya, sun sami kansu a cikin sabani da rarrabuwa mai yawa. Har ya kai ga wasu ba su iya bambancewa tsakanin ra’ayoyin son zuciya na miyagun malamai da kuma tafarkin Manzon Allah (S.A.W.) wanda magabata na qwarai suka rayu a kansa (Salafus Salih). Saboda haka babbar manufar kira zuwa ga riqo da tafarkin magabata shi ne, don komawa zuwa ga asalin addini da rayuwa cikin sahihiyar turbar musulunci wadda manzon Allah (S.A.W.) ya shimfida. Annabi (S.A.W.) bai bar kowa cikin shakku a kan tafarkin da ya kamata musulmi ya yi riqo da shi ba. Don haka har sabani da jayayya a cikin alamuran addini, sai da musulunci ya koyar da mu yadda za mu tunkare shi idan ya bijiro mana. Allah (S.W.A) yana cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku bi Allah da manzonSa da kuma majibanta al’amura daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi ga Allah da ManzonSa, idan kun kassance kuna imani da Allah da ranar lahira. Wannan ne mafi alheri (a gareku ) kuma mafi kyan fassara. Nisa’i:59)
Ibn Kasir (Allah ya yi masa rahama) yana cewa ma’anar biyayya ga Allah shi ne bin littafinSa, biyayya ga manzo kuma yana nufin riko da sunnarsa. Su kuma ma’abota alamura (watau shugabanni) ana yi musu biyayya ne a wurin da suka yi umarni da yi wa Allah da’a, amma banda wajen saba maSa. Game da komawa ga Allah da ManzonSa wajen sabani ko jayayya a tsakanin alumma kuma, Mujahid da wasu magabata (rahamatul lahi alaihim) sun yi bayani cewa abin da ake nufi da komawa ga Allah da manzonSa shi ne a koma ga Alqurani da sunnar manzon Allah (S.A.W.) Wannan umarni ne daga Allah cewa dukkan abin da ake jayayya a kansa cikin alamuran aqida ko furu’a ( ayyukan ibada), to wajibi ne a koma ga Allah da sunnar manzonSa don warware su. Domin a wata ayar ma Allah (S.W.T.) Yana cewa: “Kuma duk abin da kuka yi sabani a cikinsa, to hukuncinsa yana ga Allah.” (Shura:10).
Har ila yau, manzon Allah (S.A.W.) ya yi qarin bayani a kan wannan mas’ala ta sabani ko jayayya wadda har za ta kai ga samun baraka cikin alummar Musulmi, hakan kuwa ya kai ga rarrabuwa cikin addini. Kasancewa tafarkin manzon Allah (S.A.W.) hanya ce guda daya miqaqqiya kuma ita ce Allah ya umarce mu da riqo, to wajibi ne mu tantance abin da yake karbabbe a kan hujjoji daga Alqurani da Hadisi domin warware sabani. A cikin wani shahararren Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: “Yahudawa sun rarrabu kashi sabain da daya (71) Nasara kuma sun rabu kashi sabain da biyu (72). Sannan kuma alummata za ta rabu har kashi sabain da uku (73). Dukkan bangarorin suna wuta banda guda daya. Sai sahabbai suka ce, Wacce ce a cikinsu ya Manzon Allah (S.A.W.)? Annabi (S.A.W.) ya ce, Aljamaa (masu riqo da Sunnah).” Wannan Hadisi yana nuna mana mafita a cikin yanayin sabani, ita ce komawa ga jama’a. su kuma jama’ar da ake magana a kansu su ne wadanda suka rayu da Manzon Allah (S.A.W.) Sannan sai wadanda suka bi bayansu da kyautatawa, domin sahabbai su ne suka fi alummar da suka biyo bayansu da tsoron Allah da qarfin zuciya da fahimtar ma’anar ayoyin Allah da warware matsalolin addinin, kuma ta hannunsu ne Musulunci ya watsu a cikin duniya.
Saboda haka babbar manufar kira ga tafarkin magabata (Sahabban Manzon Allah da wadanda suka biyo su da kyautatawa), ita ce don komawa ga asalin addini da guje wa rarrabuwa ko lanqayuwa ga ra’ayoyin wasu malamai ko da ya saba wa ingantacciyar magana.
Leave a Reply