Bayan shudewar sahabban manzon Allah (S.A.W.), wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa duk sun gina fahimtarsu ta addini ne a kan tafarkin da sahabbai suka rayu a kai na gamsuwa da Alqurani mai girma da Sunnar Manzon Allah (S.A.W.). Wadannan manyan malamai daga cikin Tabiai da Tabiut-Tabi’una sun karbo ilimi daga kafofi daban-daban, sun kuma tafiyar da rayuwarsu cikin koyarwa (yada ilimi) da amsa fatawowin addini da ba da misalin rayuwa mai inganci. Sai dai ba su dora kowa a kan wata hanya ta musamman wadda suka qirqiro don gudanar da addini ba. Dukkan abin da suka koyar sun gina shi a kan Nassi (Alqurani da Hadisi) ko kuma Ijtihadinsu (Wato fahimtarsu a kan masalolin addini) a cikin abin da Alqurani da Hadisi ba su yi magana a kansu kai tsaye ba, ko kuma maganar nassi ba ta isa garesu ba. Daga cikin wadannan malamai akwai Imam Said bin Musayyib, Sufiyanu Al-Thauriy, Hasanul-Basri, Abdullahi bin Mubarak, Ishaq Bin Rahuya, Abi Thauri, Laithu Bin Saad, Annakha’i Daudu bin Aliyu, (Imamul Zahiriyya) Al-Auza’i, Imam Abu Hanifa, Imam Malik dan Anas, Imam Muhammad ibn Idris Shafii da Imam Ahmad bin Hambal. Daga cikin almajirai da magoya bayan wadannan manyan malamai ne aka sami wasu wadanda suka gina tafarki bayyananne a kan abin da malamansu su ka tafi a kai wanda ake kira da sunan Mazhaba. Malamai sun fassara ma’anar mazhaba da cewa ita ce:
“Qa’idojin da aka gina hukunce-hukuce a kansu, kuma almajiransu suka tafi a kan wanan tafarki.”
Don qara wa wannan ma’ana qarfi, shaihin malami Abubakar bin Hassan Al-Kashnawiyya Al-Malikiy ya fassara mazhabarsa ta Imam Malik dan Anas da cewa:
“Abin da (Imam Malik) ya tafi a kai na fahimtar addini kuma ya ba da fatawa a kai tsawon rayuwarsa kuma almajiransa suka ginu a kai bayan rayuwarsa.
Leave a Reply