KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI (Manhajus Salafis Salih) *** 14 MATSAYIN WANDA YA SABA WA TAFARKIN MAGABATA NA QWARAI(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah (S.W.A) Ya Yi mana umarni qarara na riqo da abin da ManzonSa (S.A.W.) ya zo mana da shi na daga magana ko aiki, a inda yake cewa:.“Kuma abin da Manzo ya zo muku, da shi, ku karve shi, abin da kuwa ya hane ku, ku bar shi, kuma ku bi Allah da taqawa. Lallai Allah mai tsananin uquba ne.” (Hashr:07).
Shi kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya fayyace mana dukkan al’amuran addini babu abin da ya rage ko ya qara daga cikin saqon Musulunci da aka aiko shi da shi. A cikin ingantattun maganganunsa ya fitar mana da tafarkinsa a fili wanda shi ne sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu, suka yi riqo da shi.
Wannan tafarki na muminan farko, manzon Allah (S.A.W.) ya tabbatar mana cewa ita ce hanyar gaskiya, wadda kuwa duk ya saba mata ya tabe daga tafarki madaidaici. Ayar da ta fito da wannnan saqo tana wurin da Allah yake cewa: “Wanda ya saba wa manzo bayan shiriya ta bayyana a gare shi, sannan ya bi hanyar da ba ta muminai ba, za mu jibintar ma sa abin da ya jibinta, kuma mu qone shi da jahannama, kuma makomarsa ta munana. (Nisa’i: 115).
Wanann umarni na Ubangiji mai girma yana da fadi matuqa, kamar yadda ma’abota ilimi suka yi magana a kansa. Hukunci bai tsaya ga saba wa manzon Allah (S.A.W.) kawai ba, a a, ya hada har da qin bin hanyar muminai. Don haka bin tafarkin muminai ko qin bin tafarkin na su, al’amari ne babba. Wanda duk ya bi tafarkin muminai to ya tsira, wanda kuwa ya saba wa tafarkin muminai to sakamakonsa wutar Jahannama.
To abin tambaya a nan shi ne, me ake nufi da tafarkin muminai?
Wannan shi ne Manzon Allah ya amsa a cikin Hadisinsa da muka gabatar wanda suka hada da hadisin da annabi (S.A.W.) ya yi bayanin rarrabuwar Yahudawa da Nasara da Musulunci. Sannan ya ce hanyar Aljama’ah ita ce kawai ke kan gaskiya. Akwai kuma Hadisin da annabi (S.A.W.) ya umarce mu da bin sunnarsa da ta halifofinsa shiryayyu.
Bayan nan kuma duk lokacin da Allah (S.W.T.) ko manzonSa suka kira muminai, suke fara amsawa, don su ne suke raye a lokacin saukar Alquani kuma suna tare da manzon Allah (S.W.A.). Bayansu sai wadanda suka biyo bayansu, da kuma wadanda suka biyo bayan wadanda suka biyo bayansa, sannan tukun sauran alummar musulmi su amsa.
Rukunan farko na muminai, su ne magabata kuma tafarkinsu shi ne tafarkin Manzon Tsira (S.A.W.). Wadanan magabata su ne kan gaba wajen tsoron Allah su suka koyi Alqurani daga Manzon Allah (S.A.W.) suka rayu tare da shi, don haka fahimtarsu ta addini tabbatacciya ce daga Ma’aikin Allah (S.A.W.) take kai tsaye. Saboda haka ba ya halatta ga wani ya yanke hukunci kan wata fassara ta Alqurani ko hadisi don kawai ya iya Larabci ko makamancin hakan. Babu makawa sai an samu cikakkiyar fassararsa daga wadannan magabata na qwarai.
Mene ne hukuncin wanda ya ce ba zai iya aiki da tafarkin magabata ba sai ya yi tsani da fahimtar wani malaminsa ko shaihinsa…?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates