Mas'alolin aure fitowa ta 10(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ci gaban bayani akan auren kisan wuta:
TAMBAYA:
Idan mace ta yi aure da niyyar kisan wuta ba tare da ta sanar da kowa ba, mene ne hukuncin wannan auren?
AMSA:
Malamai sun ce wannan auren ya inganta, saboda igiyar auren ba a hannunta take ba.
Dalilinsu kuwa shi ne: hadisin da ya tabbata daga Nana A’isha رضى الله عنها ta ce:
أن امرأة رفاعة القرظي جاءت إلى رسول الله.صلى الله عليه وسلم فقالت يا رسول الله أن رفاعة طلقني فبت طلاقي وأني نكحت بعده عبد الرحمن بن الزبير القرظي وإنما معه مثل الهدبة قال رسول الله.صلى الله عليه وسلم ( لعلك تريدين أن ترجعي إلى رفاعة ؟ لا حتى يذوق عسيلتك وتذوقي عسيلته )
Ma’ana:
Hakika matar Rifa’atal kurazī ta zo wurin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ta ce da shi: Rifa’atul Kurazī ya sake ni saki uku, sai Abdurrahman Ibn Zubair ya aure ni, amma ba shi da mazakutar da zai iya biya mini bukata. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya yi murmushi ya ce: shin kina so ki koma wurin mijinki Rifa’ata ne? ba za ki koma ba har sai mijinki na biyu ya dandani zumarki (ma’ana ya sadu da ke) kuma ke ma kin dandani zumarsa.
Malamai suna kafa hujja da wannan hadisin ne, don ita matar Rifa’a ta yi niyyar komawa wurin mijinta na farko, amma Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama bai hana ta ba, sai dai ya kafa mata sharadin cewa sai an samu saduwa tsakaninta da mijinta na biyu, sannan idan ya sake ta sai ta koma.
Kuma Imam Malik ya ce: Idan mace ta yi niyyar yin auren kisan wuta, to, wannan auren ya yi, domin saki ba a hannunta yake ba, sabanin idan hada baki aka yi, ko shi me auren na ta ne yayi niyar haka. .
Wasu daga malaman Malikiyya sun ce: ko da ita da mijinta na farko suka kulla, amma shi mijinta na biyu bai sani ba, to, auren ya yi, saboda saki a hannun mijinta na biyun yake, sai ya ga dama zai sake ta. Don haka idan ya sake ta, dama niyyar sa ba auren kisan wuta bace, to, za ta iya komawa wurin mijinta na farko.
Allah shi ne mafi sani.
TAMBAYA:
A jiya mun yi bayanin nau’ikan auren kisan wuta, da haramcin sa, da bacin sa koda an daura shi. Tambaya anan itace; Idan aka yi auren kisan wuta sai aka raba auren, shin za ta iya komawa wurin shi mijinta na farko?
AMSA:
Magana mafi rinjaye ita ce; ba za ta koma ba, sai idan ta sake yin wani auren ingantacce. Kuma wannan itace maganar Jumhurum malamai, Allah shi ne mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Mas'alolin aure fitowa ta 10(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)”
  1. Kabiru Ibrahim Avatar

    Jazakumullahu bikhair

Leave a Reply

Categories
Latest updates