Matakan kariya daga hatsarin tukunyar Gas

Danna nan domin shiga karatu Online

Haƙiƙa duk Abinda Allah ya hukunta akan bawa dole sai ya sameshi, amma komi yana tare da sababinsa, Shiyasa Allah da Manzonsa suka umarce mu muyi riƙo da sababi sannan mu dogara ga Allah.

a yau zamuyi magana ne akan matakan kariya daga hatsarin Tukunyar Gas (Gas Cylinder).

Mutane da dama a birane da ƙauyuka sun fara ƙaurace wa hanyoyin girki wacce ake amfani dasu a baya kamar itace da Kerosine da makamantansu zuwa ga Sababbin hanyoyi wanda sukafi sauƙi da kuma inganci, Daga cikin wa’innan hanyoyi akwai Tukunyar Gas wacce tana da sauƙin amfani matuƙa.

Sai dai sabida haɗari da ke tattare da amfani da wannan hanya idan har ba’a yi amfani da ita yadda ta dace ba shi yasa da yawa mutane suke jin tsoron amfani da ita, wanda kuma a haƙiƙanin gaskiya idan har mutum ya kiyaye wa’innan hanyoyi da zamuyi bayaninsu anan toh babu wani abin tada hankali game da amfani da wannan hanya Insha’Allah.

Fashewar tukunyar gas tana da sabbuba, kuma za’a iya kiyayewa Insha’Allah. Sabida haka babu wani abin tsoro cikin yin amfani da shi.

Mu sani cewa Abinda yake kawo hatsarin Tukunyar Gas A gida shine tsiyayar iskar Gas daga cikin Tukunyar (Gas leak). Idan har aka samu Tsiyayar iskan gas daga cikin Tukunyar to hakan ka iya kawo Fashewar tukunyar ko kuma tashiwar gobara a gida wacce ka iya kai ga fashewar Tukunyar.

sabida haka abu mai mahimmanci shine Mutum yasan hanyoyi da zai hana Tsiyayar Iskar gas. Idan har ya ɗau wannan mataki toh babu wani abinda kuma zai ɗaga masa hankali Insha’Allah.

Ga kaɗan daga cikin Matakan kariya da mutum zai ɗauka

Ka sayi gas wadda akwai Sinadarin ethanol aciki: Shi iskar gas bashi da ƙamshi ko wari a asalinsa, sabida haka koda ace yana tsiyaya a gida bazaka iya jin warinsa ba, sabida haka ne ake sanya masa wannan sinadari na ethanol domin ya sanya masa wari da za’a iya ji. Hakan zai taimaka idan aka samu Tsiyayar gas a gida za’a iya jinsa da wuri. Amma wasu masu kasuwancin Gas basu sanya wannan sinadarin sabida hakan yana sanya su ƙara kashe kuɗi wadda basu so suyi, sabida haka kafin ka zaɓi wurin Sayan iskar gas ɗinka ka tabbatar Gas ɗinsu akwai wannan sinadari aciki. Zaka fahimci haka idan kaji kana iya shaƙar warin Gas ɗin. Amma in kaji baka iya jin wani wari irin ta Gas to da Alama basu saka sinadarin ethanol aciki, sai ka tambaye su domin ƙarin bayani.

Kada ka siya Tukunyar gas da aka riga akayi amfani da ita: Domin hakan ka iya janyo matsaloli da yawa, domin zai iya yiwuwa Tukunyar tana da matsala, ko ta kusa Ta gama aiki.

Kada kabi araha wurin sayan Tukunyar Gas: Mutane sukan bi araha wurin sayan Tukunyar Gas wanda wannan kuskure ne babba, Gwanda ka daure ka sayi mai kyawu wanda zai daɗe yana maka aiki ba tare da wata matsala ba, wa’innan masu arahan basu da inganci, wasu ma tsafffi ne ake yi musu fenti a dawo a siyar dasu.

Ka duba Shekarar da Aka ƙayyade masa: ko wani Tukunyar Gas yana zuwa da shekaru da aka ƙayyade masa na yin aiki ba tare da matsala ba, ƙarewar wannan shekaru ba yana nufin Tukunyar ya daina aiki bane sai dai ya kamata mutum yayi ƙoƙari ya canza shi idan ya samu dama, domin zai iya fara bashi matsala wanda ka iya kai ga Tsiyayar iskan gas daga cikin Tukunyar.

A rinƙa canza baƙin roban da ke bakin tukunyar lokaci zuwa lokaci: yana da kyau a rinƙa canza wannan ɗan ƙaramin baƙin roban dake bakin Tukunyar lokaci zuwa lokaci domin hakan yana kare aukuwar Tsiyayar iskan gas daga bakin tukunyar, wasu daga cikin masu Sayar da iskan gas ɗin sukan canza wa mutum kyauta, zaka iya musu magana su canza maka.

A kiyaye yawan girgiza Tukunyar: Yawaita jijjiga Tukunyar gas ka iya janyo masa matsala idan har akwai gas aciki, sabida haka a kiyaye idan har bai zama dole ba.

A sanya Tukunyar a wuri da akwai iska: a kiyaye sanya Tukunyar Gas a wuri wanda babu iska, domin hakan zai taimaka wurin tashiwar gobara da zarar aka samu Tsiyayar iskar gas domin rashin iskan da zai tafiyar da wannan gas ɗin da sauri.

Kada a cika shi fiye da ƙima: kowani Tukunya yana zuwa da iya adadin gas da ya dace a sanya acikinsa daga 0.5kg yayi sama. Duk da cewa za’a iya sanya masa fiye da abinda yake rubuce a jikin Tukunyar sai dai hakan bashi da kyau. Idan Tukunyar ka mai ɗaukan 6kg ne toh kada ka sanya masa Gas fiye da 6kg duk da cewa zata iya ɗauka har 8kg. Domin yin haka zai takura wa Tukunyar kuma zai iya sa ta fashe idan akayi rashin sa’a.

Kammalawa: Kamar yadda nayi bayani Tukunyar gas bata da babban haɗari. sabida haka babu abin tsoro wurin yin amfani da ita, sai dai kamar yadda ko wani abu yana da matsalar sa to haka nan Tukunyar gas tana da tata, kuma za’a iya kiyaye wa idan aka bi wa’innan ababe da muka lissafo a sama. Muna roƙon Allah ya tsaremu baki ɗaya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates