MAULUDI BAYA NUNA SON MANZON ALLAH. HASALI MA TSABA MASA NE.
Manzon Allah(saw) yace: ‘dayanku baya zama mai imani har sai na zama mafi soyuwa gareshi fiye da mahaifinsa, da dansa, da duk sauran mutane baki daya…
Sannan Allah(swt) yace:
ﻗﻞ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺁﺑﺎﺅﻛﻢ ﻭﺃﺑﻨﺎﺅﻛﻢ ﻭﺇﺧﻮﺍﻧﻜﻢ
ﻭﺃﺯﻭﺍﺟﻜﻢ ﻭﻋﺸﻴﺮﺗﻜﻢ ﻭﺃﻣﻮﺍﻝ ﺍﻗﺘﺮﻓﺘﻤﻮﻫﺎ
ﻭﺗﺠﺎﺭﺓ ﺗﺨﺸﻮﻥ ﻛﺴﺎﺩﻫﺎ ﻭﻣﺴﺎﻛﻦ ﺗﺮﺿﻮﻧﻬﺎ
ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻴﻜﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻭﺟﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻠﻪ
ﻓﺘﺮﺑﺼﻮﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺄﻣﺮﻩ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻬﺪﻱ
ﺍﻟﻘﻮﻡ ﺍﻟﻔﺎﺳﻘﻴﻦ.
Ka ce: “Idan ubanninku da
ɗiyanku da ´yan´uwanku da
mãtanku da danginku da
dũkiyõyi, waɗanda kuka yi
tsiwirwirinsu, da fatauci wanda
kuke tsõron tasgaronsa, da
gidaje waɗanda kuke yarda da
su, sun kasance mafiya sõyuwa
a gare ku daga Allah da
ManzonSa, da yin jihãdi ga
hanyarSa, to, ku yi jira har Allah
Ya zo da umurninSa! Kuma
Allah bã Ya shiryar da mutãne
fãsiƙai.
‘Yan’uwa ku sani duk musulmi mai amsa sunar musulunci ya zama wajibi ya fifita soyayyarsa ga annabi(saw) fiye da kowa…
Sannan soyayya da akeyiwa annabi soyayyace ta biyayya da kauna. Ba soyayyah bace kaman ta tsakanin samari da budurwa…
yadda za’a gane mutum na son annabi bawai kawai fada a baki ake ganewa ba, A’a a aikace ake ganeshi, kayi imani dashi sannan kabi umarninsa, ka fifitashi akan kowa.
In kuka duba zaku samu a rayuwar baffan annabi abu daalib. Babu wadda yafiso fiye da manzon Allah(saw) amma da yake baiyi imani da annabi ba ya tabbata annabi yace shine wadda za’ayi masa azaba mafi sauki a gidan wuta, lokacin mutuwarsa annabi(saw) ya masa tallan kalman shahada amma Allah bai azurtashi da karba ba, kunga inda kawai soyayya ba tare da imani da annabi da yi masa biyayya ba tana tsirar da mutum da abu dalib ya tsira… Toh saboda haka ya dace ku tantance soyayya da kukeyi wa annabi(saw) kada kuyi masa soyayya irinta abu dalib domin bazata tserar daku ba…
Yana daga cikin soyayya ga annabi girmama sakon da yazo da’ita da kuma yada ta, yana daga cikin soyayyar annabi girmama iyalan gidansa da kaunarsu. Yana daga cikin son annabi son sahabbansa da girmamasu, duk wanda ya tabbata cewa shi sahabi ne ko ahlulbaiti toh ya zama wajibi wa masoya annabi su soshi kuma su girmamashi, sannan su kyamaci duk wanda ya kyamace shi….
Ya zama wajibi ga duk masoyin annabi ya zama da’iman yana bibiyar ayyukan annabi, ya zama duk ibadoji ko mu’amaloli da zaiyi ya zama yana koyine da annabi(saw).. Iya gwargwado.
‘Yan’uwa kubi annabi(saw) ku soshi zaku sami tsira….
Allah(swt) yace:
ﻗﻞ ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﺤﺒﻮﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﺎﺗﺒﻌﻮﻧﻲ ﻳﺤﺒﺒﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﻳﻐﻔﺮ ﻟﻜﻢ ﺫﻧﻮﺑﻜﻢ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻏﻔﻮﺭ ﺭﺣﻴﻢ.
Ka ce: “Idan kun kasance kunã
son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya
sõ ku, kuma Ya gãfarta muku
zunubanku. Kuma Allah Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai.
Ga misali mai munasaba… Ya tabbata cikin sunnar annabi(saw) azumtar ranar alhamis da litini… Toh anan ake gane cikakkken masoya annabi(saw) ga lissafin kalandar musulunci yau sha biyu ga watar rabi’ul awwal ne, ko sha daya… Toh kaman yadda muka sani ne akwai da yawa daga cikin musulmai anan Nigeria da ma waje. wadda gobe sha biyu ga wata suke fita suna zaga cikin gari suna buka ganga suna rawa, suna fita da anko kala kala. Kuma suna fita manyansu da yaransu, domin a cewarsu sunayin haka ne don murnar haihuwar annabi(saw).. Toh kaga anan abinda nakeso ince shine su masu aikata wannan abu su sani ba da annabi(saw) suke koyi ba, kuma wannan abinda sukeyi shaidan ne kawai yake kawata musu shi su daukeshi a matsayin addini. Babu inda ya tabbata cikin addinin musulunci cewa annabi ya tara al’ummar musulmai suna gudu acikin gari saboda murnar aihuwansa.. Haka aikin sahabbai bai nuna haka ba, haka tabi’ai da tabi’ittaabi’een.. Toh indai yin haka nuna wa annabi soyayyane shin su masuyin wannan abu sunfi duk wa’innan son annabi ne? ‘Yan’uwa ya dace mu natsu musan me mukeyi kada shaidan ya wautar da hankulanmu ya janyo mana sanadiyyar halaka… Duk masoyin annabi(saw) abinda zaiyi gobe shine ya tashi da azumi, domin abinda ya tabbata annabi yakeyi kenan…. Sannan masu daukar wannan rana a matsayin ranan murna ya dace su fahimta cewa a wannan ranan annabi(saw) ya bar duniya, sannan kuma bayaanin cewa an haifeshi a wannan ranar akwai rauni, domin akwai ruwayoyi da suke nuna cewa ba’a sha biyu ga watan rabi’ul awwal aka haifeshi ba… Saboda haka bai dace mu dauki wannan ranar a matsayin ranar murnar haihuwansa ba kawai…. Sannan aima bai dace ace wai musulmi sai kawai cikin rana daya ne kawai zai nuna murnarsa ga haihuwar annabi(saw) ba.
Wannan gafala ce… Saboda haka ‘yan’uwa wannan abu duk ba nuna soyayya bace ga annabi(saw) nuna soyayya ga annabi shine kabi umarninsa, kada kayi abinda bai saka kayi ba. Muna fatan Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu daman binta ya kuma nuna mana karya ya bamu daman kauce mata….
Leave a Reply