MAULUDI BAYA NUNA SON MANZON ALLAH. HASALI MA TSABA MASA NE.

Danna nan domin shiga group na karatu Online

MAULUDI BAYA NUNA SON MANZON ALLAH. HASALI MA TSABA MASA NE.
Manzon Allah(saw) yace: ‘dayanku baya zama mai imani har sai na zama mafi soyuwa gareshi fiye da mahaifinsa, da dansa, da duk sauran mutane baki daya…
Sannan Allah(swt) yace:
ﻗﻞ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺁﺑﺎﺅﻛﻢ ﻭﺃﺑﻨﺎﺅﻛﻢ ﻭﺇﺧﻮﺍﻧﻜﻢ
ﻭﺃﺯﻭﺍﺟﻜﻢ ﻭﻋﺸﻴﺮﺗﻜﻢ ﻭﺃﻣﻮﺍﻝ ﺍﻗﺘﺮﻓﺘﻤﻮﻫﺎ
ﻭﺗﺠﺎﺭﺓ ﺗﺨﺸﻮﻥ ﻛﺴﺎﺩﻫﺎ ﻭﻣﺴﺎﻛﻦ ﺗﺮﺿﻮﻧﻬﺎ
ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻴﻜﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻭﺟﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻠﻪ
ﻓﺘﺮﺑﺼﻮﺍ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺄﻣﺮﻩ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻬﺪﻱ
ﺍﻟﻘﻮﻡ ﺍﻟﻔﺎﺳﻘﻴﻦ.
Ka ce: “Idan ubanninku da
ɗiyanku da ´yan´uwanku da
mãtanku da danginku da
dũkiyõyi, waɗanda kuka yi
tsiwirwirinsu, da fatauci wanda
kuke tsõron tasgaronsa, da
gidaje waɗanda kuke yarda da
su, sun kasance mafiya sõyuwa
a gare ku daga Allah da
ManzonSa, da yin jihãdi ga
hanyarSa, to, ku yi jira har Allah
Ya zo da umurninSa! Kuma
Allah bã Ya shiryar da mutãne
fãsiƙai.
‘Yan’uwa ku sani duk musulmi mai amsa sunar musulunci ya zama wajibi ya fifita soyayyarsa ga annabi(saw) fiye da kowa…
Sannan soyayya da akeyiwa annabi soyayyace ta biyayya da kauna. Ba soyayyah bace kaman ta tsakanin samari da budurwa…
yadda za’a gane mutum na son annabi bawai kawai fada a baki ake ganewa ba, A’a a aikace ake ganeshi, kayi imani dashi sannan kabi umarninsa, ka fifitashi akan kowa.
In kuka duba zaku samu a rayuwar baffan annabi abu daalib. Babu wadda yafiso fiye da manzon Allah(saw) amma da yake baiyi imani da annabi ba ya tabbata annabi yace shine wadda za’ayi masa azaba mafi sauki a gidan wuta, lokacin mutuwarsa annabi(saw) ya masa tallan kalman shahada amma Allah bai azurtashi da karba ba, kunga inda kawai soyayya ba tare da imani da annabi da yi masa biyayya ba tana tsirar da mutum da abu dalib ya tsira… Toh saboda haka ya dace ku tantance soyayya da kukeyi wa annabi(saw) kada kuyi masa soyayya irinta abu dalib domin bazata tserar daku ba…
Yana daga cikin soyayya ga annabi girmama sakon da yazo da’ita da kuma yada ta, yana daga cikin soyayyar annabi girmama iyalan gidansa da kaunarsu. Yana daga cikin son annabi son sahabbansa da girmamasu, duk wanda ya tabbata cewa shi sahabi ne ko ahlulbaiti toh ya zama wajibi wa masoya annabi su soshi kuma su girmamashi, sannan su kyamaci duk wanda ya kyamace shi….
Ya zama wajibi ga duk masoyin annabi ya zama da’iman yana bibiyar ayyukan annabi, ya zama duk ibadoji ko mu’amaloli da zaiyi ya zama yana koyine da annabi(saw).. Iya gwargwado.
‘Yan’uwa kubi annabi(saw) ku soshi zaku sami tsira….
Allah(swt) yace:
ﻗﻞ ﺇﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﺤﺒﻮﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﺎﺗﺒﻌﻮﻧﻲ ﻳﺤﺒﺒﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﻳﻐﻔﺮ ﻟﻜﻢ ﺫﻧﻮﺑﻜﻢ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻏﻔﻮﺭ ﺭﺣﻴﻢ.
Ka ce: “Idan kun kasance kunã
son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya
sõ ku, kuma Ya gãfarta muku
zunubanku. Kuma Allah Mai
gãfara ne, Mai jin ƙai.
Ga misali mai munasaba… Ya tabbata cikin sunnar annabi(saw) azumtar ranar alhamis da litini… Toh anan ake gane cikakkken masoya annabi(saw) ga lissafin kalandar musulunci yau sha biyu ga watar rabi’ul awwal ne, ko sha daya… Toh kaman yadda muka sani ne akwai da yawa daga cikin musulmai anan Nigeria da ma waje. wadda gobe sha biyu ga wata suke fita suna zaga cikin gari suna buka ganga suna rawa, suna fita da anko kala kala. Kuma suna fita manyansu da yaransu, domin a cewarsu sunayin haka ne don murnar haihuwar annabi(saw).. Toh kaga anan abinda nakeso ince shine su masu aikata wannan abu su sani ba da annabi(saw) suke koyi ba, kuma wannan abinda sukeyi shaidan ne kawai yake kawata musu shi su daukeshi a matsayin addini. Babu inda ya tabbata cikin addinin musulunci cewa annabi ya tara al’ummar musulmai suna gudu acikin gari saboda murnar aihuwansa.. Haka aikin sahabbai bai nuna haka ba, haka tabi’ai da tabi’ittaabi’een.. Toh indai yin haka nuna wa annabi soyayyane shin su masuyin wannan abu sunfi duk wa’innan son annabi ne? ‘Yan’uwa ya dace mu natsu musan me mukeyi kada shaidan ya wautar da hankulanmu ya janyo mana sanadiyyar halaka… Duk masoyin annabi(saw) abinda zaiyi gobe shine ya tashi da azumi, domin abinda ya tabbata annabi yakeyi kenan…. Sannan masu daukar wannan rana a matsayin ranan murna ya dace su fahimta cewa a wannan ranan annabi(saw) ya bar duniya, sannan kuma bayaanin cewa an haifeshi a wannan ranar akwai rauni, domin akwai ruwayoyi da suke nuna cewa ba’a sha biyu ga watan rabi’ul awwal aka haifeshi ba… Saboda haka bai dace mu dauki wannan ranar a matsayin ranar murnar haihuwansa ba kawai…. Sannan aima bai dace ace wai musulmi sai kawai cikin rana daya ne kawai zai nuna murnarsa ga haihuwar annabi(saw) ba.
Wannan gafala ce… Saboda haka ‘yan’uwa wannan abu duk ba nuna soyayya bace ga annabi(saw) nuna soyayya ga annabi shine kabi umarninsa, kada kayi abinda bai saka kayi ba. Muna fatan Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu daman binta ya kuma nuna mana karya ya bamu daman kauce mata….

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

14 responses to “MAULUDI BAYA NUNA SON MANZON ALLAH. HASALI MA TSABA MASA NE.”
 1. Buhari Nuhu Avatar

  I’m very happy of finding this site,may Allah reward those who create this site.Because it is very important for every muslim brothers and sisters..,@ I wish long life from Allah Ameen….@!

 2. SANI M. YABO Avatar
  SANI M. YABO

  Allah ya biya amin.

 3. SANI M. YABO Avatar
  SANI M. YABO

  Allah ya biya amin. kuma duk mai ganin yana da hujjoji na sharia to, ya kawo. saki kowa kama Allah!.

 4. Ahmad Yusuf Assqalaini Avatar
  Ahmad Yusuf Assqalaini

  Malam, bukin maulidi da kake ganin anayi, wallahi “KADAN KENAN”

 5. bello ahmad gidadawa Avatar
  bello ahmad gidadawa

  alhamdulillahi damuka sanu malaman sunnah suna wayaddakan jama’a gameda wannan mummunan buki da aka kirkiro cikin addini. kuma aka dangana shi ga manzon tsira.

  1. bello ahmad gidadawa Avatar
   bello ahmad gidadawa

   musulmi kuguji tauhidin ash’ariyya. yana da muni da kuma sabawa aqidar magabata shiryayyu.

 6. ILIYASU IBN ALIYU Avatar
  ILIYASU IBN ALIYU

  Assalamu alaikum yan,uwa musulmi ina maku fatan alkhairi.
  Dan uwa malam mai fatwa inaso kakara tunani kuma kai ilimi na hakika bana jayayya ba kuma karoki Allah ilimi mai anfani kuma kanimi tsari ga ilmin da bashida amfani idan kai haka to kasamu ka bi umarni manzon Allah(S.A.W).
  Dan,uwa kasani acikin ma.auni na shari,a babu Annabi bai ba duk wanda ya rike wannan hujja jahiline kuma mainiman hargitsa jama,a .idan kariki Duk abinda Annabi baiyiba ba addini bane ko kuma batane to Ashe sahabbai duk batattune domin sun ta aikata abunda Annabi baiyi ba kuma bai barmasu wasiyin cewa suyi abayansaba kuma abubuwanda sukai ta karawa a musulunci muna tayinsu haryanzu Amma sabo da tabewa ku bakwa ganin hakan. Gasan karatun alqur.ani shima sabo ne ai kuma maulud tunkan ahaifi uwar makiyin maulud yakenan. Kaga ashe idan da akwai adalci to bazaka raina mauludawa ba.
  Allah yasa mudace

  1. Ali Yunusa Zakariyya Avatar
   Ali Yunusa Zakariyya

   Madallah Allah ya saka Da Alkairi amiin

 7. auwalu abdullahi. Avatar
  auwalu abdullahi.

  Assalam dan uwa mun gude to amma akan mauludi kai sharhi to ni tambayata anan itace ita kuma musabaka a ina annabi yayi ko sahabbai sukayi kuma wanne sahabine ya taba yin na daya kuma kuma waye alkalin alkalan lokacin.a huta lafiya.

 8. Rabiu Nuhu Avatar

  Ai kai baka da hujjar tuhumar sahabban annabi (s.a.w) saboda sune allah (s.w.t) yaba da shaida akansu acikin alqur’ani agurare masu yawa sannan kuma manzon allah yace (alaikum bisunnatiy wasunnatil khulafa’urrashidun….) ma’ana na horeku dabin sunnata dasunnar khalifofina shiryayyu masu shiryarwa kuriqeta da haqoranku kuma na haneku da fararrun al’amura (a cikin addini) domin lallai kowane fararren al’amari (a addini) bid’a ne kuma kowace bid’a batace kuma kowane bata yana jagoranci izuwa wuta. Kaga anan gurin sai ya katange sahabbansa allah yasa mudace amin

 9. Bazullahi Abdulkadir Avatar
  Bazullahi Abdulkadir

  Malam kada zafin qiyayya tagusar da hankalinka kazo kana nadama alokacin da nadama bazatai amfani garekaba, Soyayya da kyaunar shugaba s.aw tareda bin umarnin ALLAH SWT su sukasa akeyin MAULID inda ALLAH SWT YACE: WAMA ARSALNAKA ILLA RAHMATAN LIL ALAMIN ( shin waye rahma ) kaduba ibn kasir ko ihsanul mannan ko jala -laini kaga bayani, Amma ataqaice shugaba s.a.w shine(RAHMA) dole mufito muyi MAULID domin nuna farin cikinmu da samun abin kyaunarmu . ALLAH SWT yace” (LA’IN SHAKARTUM LA’AZIDANNAKUM ) shiyasa mafi yawammu idan watan yakama mukeyin AZUMI wasu su dafa abinci su bayar kyauta wasu tufafi wasu sutara jama’a afadi halayen shugaba duk soyayyace ta kawo haka, kai dan babu ita azuciyarka shiyasa kake suka bazamu daina MAULUDBA (HARAMUN ALAIHINNARU QALBUN AHABBAHU ) mu 12 R,A shekarar giwa muka dauka mafi rinjayen magana kai nawa ga wata kadauka awace shekara?

 10. Bashiru muhammad Avatar

  Maganan son annabi dole ne, sannan maganan ku na cewa ba a nuna soyayya karyene, sannan kunce sai mutum yaso iyalen gidansa da sahabbai amma ku baku sonsu da kuke cewa muki shi a dan suna zagin sahabbai ku bakuna zagin sayyidina aliyu bn abi talib ba? Kuna kushe darajar annabi s.A.W. Kunce sharifai basu annan yakamata inza a ki shi a dole aki yazidu dan mu awiya ko baku san shi bane? Kuma kuna kaunansa

 11. Bashiru muhammad Avatar

  Assalamu alaikum warahmatullah Maganan son annabi dole ne, sannan maganan ku na cewa ba a nuna soyayya karyene, sannan kunce sai mutum yaso iyalen gidansa da sahabbai amma ku baku sonsu da kuke cewa muki shi a dan suna zagin sahabbai ku bakuna zagin sayyidina aliyu bn abi talib ba? Kuna kushe darajar annabi s.A.W. Kunce sharifai basu annan yakamata inza a ki shi a dole aki yazidu dan mu awiya ko baku san shi bane? Kuma kuna kaunansa

 12. Ali Yunusa Zakariyya Avatar
  Ali Yunusa Zakariyya

  Akaramakalllahu kayi Bayanai Dalla Dallah Amma kuma kash saidai ka sirka da son xuciyar ka sosai dan uwa duk abin da zakayi akama kana cire son xuciya cikin lamurranka

Leave a Reply

Categories
Latest updates