Labarin Kisan Husaini Ya Game
Duniya
Da sauri kuma ba da bata lokaci ba
wannan mugun labari ya game
duniya. Ana mamaki ya aka yi
musulmi mai neman ceton Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya iya kashe jikansa,
farin cikin rayuwarsa?! Wannan
labari ya mantar da musulmi
sauran musibu da fitinun da suka
gabata. Daman an ce, ba a jin
warin bera idan ana babbakar
giwa.
A hedikwatar halifanci Sham,
Yazidu ya samu wannan labari mai
ban mamaki. Sai dai kamar yadda
muka fadi a baya, ruwayoyi sun
sha banban game da irin tarbon da
Yazidu ya yi ma wannan labari.
Riwayoyi mafi kusa da gaskiya
sune wadanda suka ce, Yazidu ya
firgita da jin wannan labari, ya yi
tasalima. Sannan ya yi rantsuwa
shi bai ce a kashe Husaini ba,
kuma bai ji dadin kisan ba. Ya
la’anci gwamnansa Ubaidullahi, ya
ce bai kiyaye alfarmar Manzon
Allah ba.
Wannan magana ba a cikin
littattafan Sunnah kawai ba har a
cikin na Shi’ah akwai ta. Misali, a
cikin KITABUL IHTIJAJ na Tabarsi
cewa ya yi: A lokacin da aka zo da
Ali bin Al Husain wajen Yazid ya
ce ma sa, na samu labarin cewa
zaka kashe ni. Idan har haka ne,
ina son wadannan ‘yan mata (yana
nufin kannensa da aka zo da su)
ka nemi wanda zai kai su Madina.
Sai Yazidu ya ce masa, ai ba
wanda zai kai su in ba kai ba. Allah
ya la’anci Ibnu Murjanah –
Ubaidullahi bin Ziyad kenan –
wallahi ban sa shi kashe babanka
ba. Kuma da ni ne a wurin wallahi
ba zan kashe shi ba. Sannan ya yi
masa kyauta mai yawa, ya mutunta
shi, ya hada shi da ‘yan rakiya tare
da sauran matan suka wuce
Madina.
Leave a Reply