Mutuwar Sarki Yazid
Ga dukkan alamu Yazidu ya bar
duniya da juyayin abu guda daya
da yake fargaban gamuwa da
Allah a kan sa. Wannan lamarin
kuwa shine kisan Husaini da
danginsa. An fadi cewa, karshen
kalaman da ya furta a duniya su
ne: “Ya Allah! kada ka rike ni da
abinda ban so ba kuma ban bada
umurni ba. Ya Allah! Kayi hukunci
a tsakani na da Ibnu Ziyad”. Yana
nufin gwamnansa na Kufa wanda
ya sa aka kashe Husain. Duba:
Mukhtasar Tarikh Dimashq (8/256).
Idan har maganarsa gaskiya ce,
kuma ya samu kubuta daga
wannan danyen aiki, to ko zai
kubuce ma alhakin mutanen
Madina ga abinda ya biyo baya?
Hukunci yana wurin Allah. Idan
Allah ya so shi da rahama zai yiwu
jihadinsa na cin babbar hedikwatar
Qaisar ya ceci shi tun da ya
tabbata cewa, manzon Allah
(SAWW) ya ce wannan runduna
sun wajabta shiga aljanna. Kuma
rahamar Allah tana rinjayar
fushinsa. Idan kuma madaukakin
sarki ya yi masa wani hukuncin
daban a kan laifukansa to, Allah
bai zalunce shi ba. Daman Allah
ba azzalumi ne ba ga bayinsa. A
nan yana da kyau mu sani cewa,
duk wani hadisi da ya ayyana
Yazid da sunansa ko ma da sunan
wanda ya kashe Husaini (RA) ya
yanke ma sa hukunci, ba
ingantacce ba ne, kage-kagen
mawallafa ne na daga baya.
Sunan Yazidu bai tabbata a
kowane hadisi ba da yabo ko da
fallasa.
Yazid ya rasu a ranar 14 ga Rabi’
Awwal na shekarar 64H. Duka
duka mulkinsa bai cika shekaru
hudu ba amma al’ummar musulmi
ta samu ja da baya matuka daga
karfinta da kwarjininta a cikin
wannan bakin lokaci.
To, ko me ya faru ga rundunarsa
da take Makka?
sai ku dakace mu.
Leave a Reply