Matsayin Malaman Sunnah Game
Da Tawaye A Kan Sarki Yazid
2. Muhammad Bin Ali Bin Abi Talib
A cikin yawon da suka yi na neman
goyon bayan jama’a, wadanda
suka shirya tawayen a Madina sun
je wurin kanen Husaini;
Muhammad wanda aka fi sani da
Ibnul Hanafiyyah. Muhammad ya
tambaye su, mene ne dalilinku na
yi wa Yazidu tawaye? Sai
jagoransu Abdullahi bin Muti’u ya
kada baki ya ce masa, saboda
Yazidu na shan giya, kuma ba ya
sallah, sannan yana tsallake
hukuncin Alkur’ani. Muhammad ya
ce masu, to amma ni na je wajen
Yazid ban ga abinda kuka fadi ba.
Na zauna tare da shi na wani
lokaci, na lura da yana tsayar da
sallah, yana kamanta yin alheri,
yana tambayar ilimi kuma yana
lazimtar Sunnah. Sai suka ce, ai
zai iya yin haka don riya! Ibnul
Hanafiyyah ya ce, to me yake so a
gurina ko yake tsoro da zai mani
riyar yin abinda bai saba yi ba? Ya
sha giyar ne a gabanku? In dai har
kun ga ya sha giya, to tare kuka
sha kenan. In ba haka ba to bai
halalta ku shedi abinda ba ku gani
ba. Sai suka ce, ba mu gani ba
kam amma wallahi mun yarda da
wannan magana, kuma tabbas
gaskiya ce. Sai ya ce, to, Allah
Ta’ala ya soke wannan shaida
taku, don cewa ya yi:
( ﺍﻻ ﻣﻦ ﺷﻬﺪ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﻫﻢ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ( ﺳﻮﺭﺓ
ﺍﻟﺰﺧﺮﻑ: ٨٦
“Face wadanda suka yi shaida da
gaskiya, kuma suna sane (da
abinda suka yi shaida a kansa).
Suratuz Zukhruf: 86
Da Ibnul Hanafiyyah ya tabbata
masu ba shi tare da su, sai suka ce
kamar dai kana ganin kai ka fi
cancanta mu sa gaba! Sai ya ce,
sam. Ba na halalta ma kaina yin
wannan al’amari a kowane
matsayi, ina jagora ko ina mabiyi.
Suka ce, to, amma ai ka yi yaki tare
da babanka. Ya ce, ku kawo min
wani irinsa in taya shi yaki. (A nan
sun manta cewa, babansa shi ne
sarki, ba tawaye ne yake yi ba).
Suka ce, to ka sa ‘ya’yanka Al
Qasim da Abul Qasim su biyo mu.
Ya ce, in har zan sa ‘ya’yana me
zai hana ni ma in je?
Suka ce, to ka zo mu je ba sai ka yi
yaki ba. Iyaka kawai ka yi mana
kamfe ga mutane. Ya ce, tsarki ya
tabbatar ma Allah! In ce mutane su
yi abinda ba zan yi ba? Suka ce, to
lalle ko kana so ko ba ka so sai
mun shigar da kai cikin wannan
lamari. Ya ce, ba zai maku dadi ba
don zan rinka ce ma mutane su ji
tsoron Allah, kada su yardar da
wani mahaluki a cikin fushin
ubangiji. Daga karshe dai
Muhammad ya fice ya bar Madina
zuwa Makka don gudun wannan
fitina. Duba AL BIDAYA WAN
NIHAYA na Ibnu Kathir (8/604) da
kuma MUKHTASAR TARIKH
DIMASH na Ibnu Manzhoor (8/256)
Leave a Reply