Mai rubutu: Abdurrahman Muhd Sani Umar
Wani Secularist (Dan boko Akida) ya rubuta cewa :
Bazan tilastawa ‘ya’yana suyi sallah ba bazan farlantamusu saka hijabi ba. Ita ibada ko dai ta kasance sabo da gamusuwa da da ikhlasi ko kuma shirme da shirirta
Sai wani yamai comment ya bashi amsa da cewa:
Amma zaka tilastamusu tashi da safe domin tafiya makaranta! zaka tilastamusu bitar karatun aji! da kuma yin Assignment, zaka tilastamusu shan maganin zazzabi ko da dure ne! wanda wadannan abubuwane da suka shafi Duniya mai gushewa da samun daukaka da tsira a cikinta
Amma kokarin cetonsu daga azaba ranar Alkiyama da yi musu nuni zuwa ga jin dadi na har abada wannan yana bukatar Gamsuwa !!
Abun la’akari anan shine:
A wurin wadannan mutanen wadanda Turawa suka yiwa barbarar tinani: Haddin Ridda wannan ya ci karo da hakkin dan adam na ‘yancinsa na yayi addinin da yaga dama, amma ukubar kisa ga wanda yaci amanar kasa wannan daidaine wayewace ba zancen tausayamusu.
Haddin sata da kuma fashi da makami wannan akwai rashin imani da tausayi da rashin dan adamtaka a ciki, amma ukubar kisa ga masu harkar kwaya wannan yayi daidai ita ce wayewa ba zancen tausayawa wanda yake cutar da Al’umma !
Haddin zina wannan akwai rashin imani da kuma shisshigi da kuma keta ‘yancin mutane amma kuma ukubar Sexual harassment wannan daidaine sabo da kiyaye mutumunci ‘ya Mace da kuma kiyaye Al’umma daga lalacewa !! Da sauran misalai ire-iren wadannan masu yawa
Abinda zamu lura da shi anan shi ne:
Matsalarsu ba dokokin bane akaran kansu ba matsalarsu itace tushen wadannan dokokin idan daga Allah da manzonsa suke to wannan kauyacine da gidadanci da ci baya da rashin wayewa. in kuma daga Turuwan yammane komin tsaurinsu da rashin dacewarsu to wannan wayewace da cigaba kuma abune mai kyau da ya wajaba abi ko ana so ko ba’a so !
Wannan itace matsalarsu !!!!
Leave a Reply