Yana da kyau a irin wannan lokaci na jarabawa mu rinƙa tunawa da maƙotanmu, da makusantanmu, da kuma ƴan’uwanmu. Da yawa mutane sun shiga cikin halin tashin hankali da ɗimuwa, ta yadda an kulle kasuwanni, iyakoki da wuraren kasuwanci da dama.
wani bashi da abinda zaici sai ya fita ya nema a kullum. Gashi kuma an hanashi fita, toh kai wanda Allah ya hore maka kana dashi ka samu ka taimaka ma wanda bashi dashi, ka fitar dashi daga cikin wannan bala’i da yake ciki kaima Allah zai taimake ka. mafi kyawun taimako da zaka taimaki mutum dashi shine ka taimake shi a lokacin da yake da tsananin buƙata. Allah yasa mudace, ya kuma yaye mana wannan musiba. Ya kuma sanya ta ta zamto mana aya, mu samu daman komawa zuwa gareshi. Ameen.
Leave a Reply