Inaso na koyi Nahwun larabci wani littafi ya dace na fara dashi?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Amsa: a haƙiƙanin gaskiya Akwai littafai da yawa da aka rubuta a fannin Nahwun Larabci, wasu suna da sauƙi wasu kuma suna da ɗan wuya. Amma a irin tawa gwaji zance littafi da yafi dace wa Mai fara koyan Nahwun Larabci ya fara karantawa shine littafin Ajrumiyya. Da so samu ne ɗalibi ya haddace matanin sai kuma ya samu sharhinsa.

Maluma da dama sunyi sharhin wannan littafi. Amma daga cikin sharhin da yafi shahara shine Attuhfatu-ssaniyyah wanda Sheikh Muhyidden Abdul-hamid ya wallafa.

Sharhin na da kyau, sannan kuma bashi da yawa.

Yana da kyau ɗalibi ya sami wannan sharhi ya samu malami ya karanta masa. Sannan sai kuma sharhi na biyu wanda shima yana da kyau matuƙa, shine Sharhin da Sheikh Ibn Uthaymeen yayi. Shima wannan sharhi na da kyau matuƙa, kuma ɗalibi zai fa’idantu da wasu ilimomi wanda Malam ya zuba acikin wannan littafi. Domin malam ya taɓa janibi da yawa. Kana karanta littafin wani lokaci zaka ji kaman kana karanta littafin Aqeedah ne. Domin duk wurin da Malam ya samu dama sai ya tsaya yayi bayani. Duk da littafin na da girma amma gaskiya yana da sauƙi sosai, kuma ɗalibi zai fa’idantu matuƙa.

In Allah ya taimaki ɗalibi ya gane wannan littafi na Ajrumiyya to haƙiƙa ya samu makulli da zai gane Nahwu dashi. Kuma duk wani zance da zaiyi bazai sami matsala ba wurin yin kuskure ta larabci, sai dai kuma in yanason cigaba sai ya ƙara ya nemi Alfiyyah.

Allah yasa mudace. Zan sanya Link na littafan a ƙasan wannan rubutu.


التحفة السنية


شرح آجرومية للشيخ ابن عثيمين


Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories