Ramadaniyyat 1443 (3) :Yafiya A Wajen Shugaba

Danna nan domin shiga karatu Online

  1. Annabi Yusuf (A.S) yana cikin annabawa da suka fada jarrabawa amma daga ƙarshe Allah (S.W.T) ya ba su nasara, ya kuma ɗaukaka su a dalilin wannan jarrabawa.
  2. Ya gamu da jarraba iri-iri daga wurin yan’uwansa waxanda suka yi ƙoƙarin ɓatar da shi, wasu daga cikin ma suka bayar da shawarar kashe shi, daga karshe suka zavi su ɓatar da shi ɓat.
  3. Annabi Yusuf (A.S) ya zauna a cikin kwararramar rijiya, sannan ya yi zama boyi-boyi, sannan ya yi zaman a kurkuku na wasu shekaru ba don yayi wa wani laifi ba. Daga kurkuku kuma ya zama ɗaya daga cikin manya-manya masu madafun iko na ƙasar Masar.
  4. Allah (S.W.T) ya ba shi Annabci da mulki. ‘Yan’uwansa kuma sun yi ta sintiri zuwa kasar Masar neman taimako wajensa ba tare da su gane da wa suke mu’amala ba. Amma shi Annabi Yusuf (AS) ya gane cewa, yana mu’amala ne da ‘yanuwansa waɗanda a baya suka yi yunkurin hallaka shi.
  5. Sun zo suna masu neman taimako a wajensa bayan farin da ya auka wa yankin kasarsu. Daga karshe ya bayyana musu cewa:
    (Ni ne Yusuf, kuma wanann ɗan’uwana ne; haƙiƙa Allah ya yi mana baiwa; lalle wanda ya kiyaye dokokin (Allah) ya kuma yi haƙuri, to tabbas Allah ba Ya tozarta sakamakon masu kyautatawa) [Yusuf aya ta 90].
  6. Nan take suka fara burin kunya bayan ganin matsayin da dan’uwansu yake ciki, da su kuma yadda suka koma, sai suka ce masa:
    (Wallahi haƙiƙa Allah Ya fifita ka a kanmu, mu kuma lalle mun tabbata masu kuskure!”
  7. Shi kuma sai ya ce musu: “A yau babu wani zargi a kanku; Allah zai yafe muku, Shi ne Mafificin masu rahama). [Yusuf aya ta 90-92].
  8. Annabi Yusuf (A.S) yana da dama ya ɗauki fansa ko kuma ya nuna fushinsa ko ya yi ramuwar gayya a kan ‘yan-uwansa, amma zuciyar Annabawa, da ta bayin Allah na kwarai daban take da sauran zukata. Saboda haka Annabi Yusuf (A.S) bai yi tunanin ɗaukar fansa ba, bai ma tsaya ya sake labarta abin da aka yi masa a baya ba, sai kawai cewa ya yi:” Shin ku kuwa kun san abin da kuka aikata wa Yusufu shi da ɗan’uwansa a lokacin da kuke cikin jahilci?”
  9. Da wannan ya ɓuɗa bayaninsa gare su tare da ba su uzuri, cewa sun yi abin da suka yi ne a cikin jahilci. Duk kuwa wanda aka ce, ya yi laifi a cikin rashin sani, to lalle an ba shi uzuri mai karfi, watau kamar ana cewa ne, da a ce ya san munin abin da ya aikata, to da ba zai aikata ba.
  10. Nan take sai ya kada baki ya ce musu: “A yau babu wani zargi a kanku; Allah zai yafe muku, Shi ne Mafificin masu rahama”

Darasi:

  1. Darasin da za mu ɗauka shi ne yafiya, ko kawar da kai daga shugaba. Duk wanda Allah (S.W.T) ya dora masa nauyin al’umma ya danqa masa ragamar shugabncinsu, to yana da kyau ya nesanta kansa da zuciyarsa daga dabi’ar ramuwa a kan wani abu da za a yi masa. Domin shi yana rayuwa ne don al’umma ba domin kansa ba. Kada ya fifita abin da ya shafi maslaharsa shi kaɗai, idan an yi masa laifi, kada ya shagalartar da kansa wajen ramuwa da ɗaukar fansa, domin yin haka zai dakile masa ayyukan da yake yi na ci gaban al’umma da maslaharsu, ko kuma mayar da hankali wajen samar da daidaito a cikin al’umma.
  2. Duk wanda yake tsaye da gudanar da lamarin al’umma dole ne zai yi ta ganin abubuwa masu sosa rai; a wasu lokata zai ji baqaqen maganganu na rashin adalci a kansa da habaici da ƙage, to dole ne ya hadiye duka wannan, ya yi kamar bai ji ba. Allah ya bayyana cewa, yana daga cikin siffofin shugabanci na kwarai akwai hakuri. [Duba, Suratus Sajda, 24].
Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates