Ramadaniyyat: 1444 (22) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga karatu Online

Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (22)

Ci gaba…..

Jarabbawa Ta ƙarshe:

  1. Ibnu Taimiyya ya dawo ya ci gaba da karatuttukansa, ya kuma shiga aikin sake bitar littattafansa da rubuce-rubucensa, waɗanda suke da nasaba da aƙida da masu nasaba da siyasa shar’iyya da na fiƙhu. Sannan kuma yana kwarara wa almajiransa karatu mai zurfi da tarin yawa, har zuwa shekara ta 726 lokacin da aka umarce shi ya koma zuwa gine-ginen Fada. Ga abin yadda ya faru:
  2. Masu son su ga bayan Ibnu Taimiyya sun ci gaba da sa masa ido; wasu saboda hassada a kan matsayin da ya samu a wurin jama’a; wasu kuma saboda saɓanin aƙida da fahimta, kamar sufaye da ‘yan shi’a. Daga cikin Fuƙaha’u ma akwai masu gaba da shi saboda suna ganin ra’ayoyinsa na fiƙhu sun saɓa da na addini.
  3. Sai duka waɗannan suka haɗa baki wajen ganin sun lalubo wani abu da za su shirya masa kaidi a kansa, su kuma haɗa shi faɗa da mutane da shugabanni. Sai suka zaƙulo wata tsohuwar fatawa da ya taɓa bayar wa tun shekaru goma sha bakwai da suka wuce, a ciki yana bayanin rashin halaccin yin tattaki daga wurin mai nisa don zuwa ziyarar ƙaburburan salihai, ko ma ziyarar Raudha inda ƙabarin Manzon Allah (SAW) yake. Ga kaɗan daga abin da fatawar take cewa:
  4. “Ya zo a cikin littafin Sunan na Sa’id ɗan Mansur cewa, Abdullahi ɗan Husaini ɗan Hasan ɗan Aliyyu, ɗan Abu Ɗalib, ya ga wani mutum yana zaryar zuwa wajen ƙabarin Annabi (SAW), sai yake faɗa masa hadisin Annabi (SAW) da yake cewa: ‘Kada ku mayar da kabarina kamar idi, ku yi mini salati, domin salatinku yana iso wa gare ni a duk inda kuke’. Ya ƙara masa da cewa: “Da kai a nan, da mutumin da yake ƙasar Andalus duk ɗaya kuke”. Kuma ya zo cikin Sahihul Bukhari da na Muslim daga A’isha (RAH), daga Annabi (SAW), yana faɗa a cikin jinyarsa ta ƙarshe cewa: “Allah ya la’anci Yahudu da Nasara sun mayar da ƙaburburan Annabawansu masallatai”, yana gargaɗi game da abin da suka aikata. Ba don gudun haka ba, da an bayyana ƙabarinsa. Sai dai ba ya so ne ya mayar da shi masallaci. Sun binne Annabi (SAW) a cikin ɗakin Nana A’isha (RAH) saɓanin yadda suka saba binne mutane a sahara, don gudun kada a riƙa yin salla a daidai ƙabarinsa, sannan a mayar da shi masallaci, daga bisani ya koma tamkar gunki. Kuma Sahabbai da Tabi’ai, lokacin da ɗakin Nana A’isha yake rabe da Masallacin Annabi (SAW) har zuwa lokacin Walid ɗan Abdulmalik, babu mai shiga inda ƙabarin Annabi (SAW) yake, don su yi salla a wurin, ko don shasshafa ƙabarin, ko yin addu’a a wurin. Duk waɗannan abubuwa suna yin su ne a cikin Masallacinsa. Magabata na ƙwarai idan sun zo ziyarar sa, sukan yi masa sallama, sannan idan suka so yin addu’a, sai su fuskanci alƙibla su yi addua’a, ba sa fuskantar shi ƙabarin. Amma kuma game da tsayuwa don yi masa sallama, Abu Hanifa yana cewa, mutum zai fuskanci alƙibla ne ba ƙabarin ba. Yawancin malamai kuwa cewa suka yi, zai fuskanci ƙabarin ne yayin da zai yi addu’a”.
  5. Ibnu Taimiyya ya yi wannan fatawar tun da jimawa, ba kuma wani hazo da ta yamutsa a lokacin, sannan ba wanda ya yi amfani da ita don ya ƙuntata masa, saboda matsayi da yake da shi a wurin mai martaba Sarki a wancan lokacin. To amma yanzu da aka fuskanci an ɗan samu rashin jituwa tsakaninsu a dalilin mas’alolin saki, sai suka ga bari su yi amfani da wannan damar, su motsa Sarki da jama’ar gari a kan Ibnu Taimiyya. Sai suka tono wannan fatawar, domin ta shafi wani abu na Manzon Allah (SAW), kuma kowa ya san yadda ake saurin zaburar da Musulmi idan an zo da wani abu da ya shafi Manzon Allah (SAW).
  6. Masu ƙulla wa Ibnu Taimiyya makirci sun rubuta takarda zuwa ga mai martaba Sarki suna sanar da shi cewa, lalle Ibnu Taimiyya yana jirkita maganganu daga wurarensu. Sai Sarki ya ba da umarni a je a tsare shi a wurin da ya kamata a ajiye mutum mai matsayi irin nasa. Ya turo da wannan umarni zuwa Dimashƙa a ranar 17 ga watan Sha’aban na shekarar 726. A ka je a ka sanar da Ibnu Taimiyya saƙon Sarki, daga nan kuma aka kawo masa abin hawa, a ka ɗauke shi zuwa gine-ginen Fadar Dimashƙa aka tsare
  7. Aka kuma bar ɗan’uwansa Zainuddin ya zauna tare da shi, don ya riƙa yi masa hidima.
  8. Za mu ci gaba in sha Allah….
Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates