‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (3)
Ci gaba…..
- Taƙiyyuddin Ibnu Taimiyya ya kama hanyar neman ilimi gadan-gadan kamar yadda ya gada daga gidansu. Mahaifinsa, kamar yadda ya gabata, babban malamin hadisi ne, kuma shugaban wata makarantar Hadisi ne a birnin Dimashƙa. Ibnu Taimiyya bai zama attajiri ba, kamar yadda Abu Hanifa ya zama, domin ya gaji kasuwanci daga mahaifinsa, kuma har ƙarshen rayuwarsa yana zuwa kasuwa. Don haka kyan ɗa ya gaji mahaifinsa na ƙwarai. Wannan ne ya sa Ibnu Taimiyya ya rungumi neman ilimi tun daga farko. Ya tunkari ilimin Hadisi bayan ya gama haddar Alƙur’ani ya san tafsirinsa.
- Ya fara karatunsa ne a wurin mahifinsa. Sannan ya yi karatu a hannun manyan malamai na zamaninsa. Ya karanci littattafan Hadisi a wurinsu masu yawa, kamar littafin Musnad na Imamu Ahmad bn Hanbal da Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunanu Abi Dawud da Jami’ut Tirmizi da Sunanun Nasa’i da na Ibn Maja da na Daraƙuɗni, har ma wani masani a zamaninsa yana cewa, ya Ibnu Taimiyya ya haddace ‘Al-Jam’u bainas Sahihain, na Al-Humaidi.
- Bayan ya yi zurfi a ilimin Hadisi sai kuma ya juya zuwa ga ilimin Fiƙhun Mazhabar Hanbaliyya wadda ita ce Mazhabar da ya taso ya ga ana karantawa a gidansu. Mahaifinsa da kakanninsa manyan malamai ne na wannan Mazhabar. Kuma Mazhaba ce da ta yi suna wajen bin diddigin hadisai na Manzon Allah (SAW). Ibnu Taimiyya ya karanci wannan Mazhabar daga mahaifinsa har ya laƙance ta sarai. Sannan ya laƙanci sauran Mazhabobi guda uku; Hanafiyya da Malikiyya da Shafi’iyya. Ya kai matakin da idan yana magana a kan kowace mazahaba daga cikinsu, mai sauraron sa zai yi tsammanin bai son wata mazahaba ba sai wannan kaɗai saboda faɗin fahimtarsa a kanta.
- Ibnu Taimiyya tun yana matashinsa ya ƙwallafa ransa a kan bibiyar riwayoyin sahabbai da tabi’ai da maganganunsu da fatawoyinsu, waɗanda yake ɗauka a matsayin madogara ta farko wajen fahimtar duk wata mas’ala ta addini, har ya zamanto bai yarda ya ga wani ya fita daga fahimtar da suka yi wa addinin Musulunci ba. Duk wanda yake karanta littattafansa ya san da haka.
- Karatun Ibnu Taimiyya bai taƙaita a kan ilimin addini kaɗai ba; (watau ilimin Alƙur’ani da Hadisi da Fiƙihu da Tafsiri). A’a, Ibnu Taimiyya ya mai da hankalinsa har ila yau a kan ilimin harshen Larabci, ya kutsa cikinsa sosai inda a nan ma ya haddace abubuwa da dama na rubutun zube da na waƙe. Ya kuma ƙware wajen sanin tsohon tarihin Larabawa da kuma tarihinsu bayan zuwan Musulunci. Ya goge matuƙa a ilimin Nahawu, domin kuwa ya laƙanci littafin Sibawaihi, watau Al-Kitab, ya yi masa karatu na ƙalailaicewa, har ma yakan ci gyaran sa da hujja a kan wasu mas’alolin ilimin Nahawu.
- Baya ga ilimin addini da Ibnu Taimiyya ya yi fice a kansa, ya kuma san ilimin lissafi, sannan ya fahimci ra’ayoyin malaman Falsafa na Girikawa da Farisawa da Indiyawa fahimta ba ta wasa ba. Kamar yadda ya fahimci ilimin Girikawa na Manɗiƙi, domin kuwa har rubuta littafi ya yi sukutum da guda, don ya warware wasu mas’aloli da bai gamsu da su ba a ciki wannan ilimi. Wannan yana nuna ba ƙaramar laƙanta ya yi wa wannan fanni ba.
Za mu ci gaba insha Allah……
Leave a Reply