0. Gabatarwa:
0.1 Malanta, kamar kowace irin sana’a a rayuwan ɗan’adam, akan samu ƙwararru waɗanda suka san sana’arsu ciki da waje, suke kuma kula da ita suna tsare mata mutunci. Hakanan akan kuma samu bara-gurbi ’ya shisshigi a cikinta, waɗanda suka yiwo kutse da taka-haye. Sai dai samuwar ‘yan take-haye a cikin sha’anin malanta abu ne mai matuƙar haɗari a ruyuwar al’umma, domin varnarsu ba za ta taƙaita a kan gangar jiki kawai ba, a’a, za ta tavo har zukata, ta kuma yi mungun ta’adi a addini mutum. Yawan waɗannan bara-gurbin malaman ya jefa mutane dadama cikin ɗimiwa da ruɗani har sun kasa tantance tsakanin ‘yan gaske da kuma ’yan gangan.
0.2 Babu mamaki a samu bara-gurbi a cikin rukunin malamai duk kuwa da kasancewar sana’arsu sana’a ce ta masu neman lahira da yardar Allah, saboda malamai su ne magada annabawa, to amma kuma har a tarihin annabta an samu ‘yan tamore maƙaryata waɗanda suka yi da’awar annabta ba tare da hujja ba.
0.3 Tun a ƙarshe-ƙarshen rayuwar Annabi (SAW) aka samu al-Aswad al-Ansi wanda ya yi da’awar annabata, kuma ya ja zugar mabiyansa har suka mamaye wani vangare na ƙasar Yaman, kafin Allah ya ba wa Musulmi nasarar gama wa da shi, bayan sun sami haɗin kan matarsa wadda ya tursasa mata auren sa ba tare da tana son sa ba. Hakanan aka samu Ɗulaihatu al-Asadi wanda shi ma ya yi da’awar annabata, Khalid ɗan Walid ya yi arangama da rundunansa, ya kuma yi nasarar karya lagonsa, amma daga bisani sai ya dawo Musulunci ya fita yaƙe-yaƙe tare da Musulmi har ya yi mutuwar shahada a Nahawand. Sannan kuma an yi irin su Musalima al-Kazzab, shi ma haka ya bushi iska ya kira kansa annabi, Musulmi suka yaƙe shi tare da mabiyansa, suka yi kuma nasarar muruƙushe ta’addancinsa, Wahshi ya kashe shi murus har lahira, tasa ta zo ƙarshe.
0.4 To haka nan aka ci gaba da samun masu da’awar annabata na ƙarya, waɗanda suka riƙa ruɗar wasu makakkun mutane masu gaskata su. To idan har an samu irin wannan shisshigi a cikin sha’anin annabta, to ka ga babu wani mamaki a samu irinsu da yawa a cikin malamai, domin malamai su ne magada annabawa. Da jimawa Imam Auzai ya tava cewa, “Wannan ilimi ya kasance abu ne mai daraja, mutane suna koyon sa daga junansu, to yayin da ya shiga cikin littattafai, sai waɗanda ba ahalinsa ba suka kutsa kai cikinsa”. [Ibn Salah, sh. 182, 183]. To tun daga wannan lokaci ne, wato ƙarni na biyu bayan hijira, matsalar malantar gangan da taka-haye ta samo asali.
0.5 Ibn Hazm yana faɗa cewa, “Babu abu mai cutar da ilimi da malanta kamar ‘yan shisshigi a cikinta, domin su ne suke yaɗa jahilci da sunan ilimi, suna kuma varna amma suna zoton gyara suke yi”. [Ibn Hazm, Mudawat an-Nufus, sh. 23].
Za mu ci gaba da tattauna wannan matashiya ta Ilimi da malanta a tsawon kwanakin Ramadan masu albarka in sha Allah.
Leave a Reply