Ranar Aashura: shine ranar goma ga watan Al-muharram, kuma rana ne da akeso musulmi ya azumceshi sabida falaloli dake cikinsa, sannan kuma anaso wanda zaiyi azumin ranar Aashura ya azumci ranar tara .
Falalar Azumin Ranar Aashura: Abu Qatada Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yace :
Azumin ranar Aashura tana kankare zunuban shekarar da ta gabata.
– Muslim 2746-2747
Kuma Manzon Allah yana fifita azumin wannan rana ta Aashura akan waninsa, kamar yadda aka rawaito daga Ibn Abbas Allah ya ƙara masa yarda
– Bukhari 2006
Tunatarwa: Ba’a rawaito daga Annabi ko Magabata na gari cewa wannan Rana ta Aashura ranace ta nuna baƙin ciki ko kuma yin wasu bukukuwa ba, Abinda aka Rawaito shine yin azumi a wannan Rana, sai mu gujewa yin duk wasu abubuwa da basu da asali wanda bazasu jawo mana wani amfani ba, sai dai abinda zai cutar damu, a duniyanmu da kuma Addinin mu.
Leave a Reply