SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) KAMAR YADDA HADISAI SUKA BAYYANA SU(Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gabatarwa Kowace al’umma tana
tinqaho ne da tarihinta. Kuma
magabatan kowace al’umma ana
kallon su a matsayin abin
girmamawa da darajantawa
wadanda kan zama abin koyi ga
na baya. Al’ummar musulmi ba a
bar ta a baya ba wajen sanin
matsayin magabata kamar yadda
karantarwar Alqur’ani ta nuna.
(( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺅﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ)) ((..ﻭﻳﺴﺘﻐﻔﺮﻭﻥ
ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ..)) Sahabban manzon
Allah (SAW) su ne almajiransa da
suka rayu da shi, suka sha daga
mavuvvugar ilminsa mai tarin yawa
da albarka. Haka kuma su ne
waxanda duk tsawon rayuwarsa
yake tare da su, kuma duk wata
nasara da Allah ya ba shi a cikin
rayuwarsa to, su ne abokan cin
nasarar nan masu farin ciki da ita.
Haka kuma duk wata matsala da
ya gamu da ita to, su ne abokan
juyayi da jin damuwa a kanta.
Kamar yadda buwayayyen sarki
Allah ya ce: (( ﻫﻮ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻳﺪﻙ ﺑﻨﺼﺮﻩ
ﻭﺑﺎﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ * ﻭﺃﻟﻒ ﺑﻴﻦ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ ..)) Sahabbai
su ne surukan manzon Allah
(SAW) waxanda ya auri ‘ya’yansu
kuma ya aura masu nasa ‘ya’ya.
Su ne kuma wadanda suka ba da
rayuwarsu da dukiyarsu da
mutuncinsu saboda kariyarsa da ci
gaban addininsa har sai da suka
cimma babban abin fata shine
yardar Allah madaukakin sarki
kamar yadda Alqur’ani ya shelanta
haka. Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya
ce: (( ﻟﻜﻦ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻣﻌﻪ ﺟﺎﻫﺪﻭﺍ
ﺑﺄﻣﻮﺍﻟﻬﻢ ﻭﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻟﻬﻢ
ﺍﻟﺨﻴﺮﺍﺕ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ ..)) Kuma ya ce:
((ﻭﺍﻟﺴﺎﺑﻘﻮﻥ ﺍﻷﻭﻟﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻭﺍﻷﻧﺼﺮ
ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﺗﺒﻌﻮﻫﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ ﻭﺭﺿﻮﺍ
ﻋﻨﻪ ..)) Maqasudin wannan mukala
shine fito da matsayin sahabban
manzon Allah (SAW) da fifikon su a
kan sauran musulmi kamar yadda
manzon Allah din da kansa ya
bayyana su. Haka kuma mukalar
zata tattauna a kan wasu hadisai
da ake yi wa kuskuren fahimta a
dauke su a matsayin suka da zargi
ga sahabbai, da kuma wasu
hadisai da masu son zuciya suka
qirqiro don bata hasken rayuwar
waxannan bayin Allah nagartattu
suka jingina su manzon Allah
(SAW). Zata kuma yi ishara zuwa
ga yadda mabiyan Sunnah suke
auna abinda aka bijiro na tarihi
wanda ya ci karo da irin waxannan
tabbatattun hadissai gami da
ayoyin Alqur’ani da kyakkyawar
natijar da suke fita da ita wadda ke
lamunce musu samun tsira. Ba
dukkan hadisan da suka zo a
kansu ne wannan mukala zata yi
magana ba sai dai zamu fito da
manyan manufofin da hadisan
suka kunsa ne ta hanyar bada
misali. Ingantattun Hadisan da
Suka yi Magana A Kan Sahabbai
1. Fifikon zamaninsu ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﺳﺌﻞ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﺃﻱ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺧﻴﺮ؟ ﻗﺎﻝ:
))ﻗﺮﻧﻲ، ﺛﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻠﻮﻧﻬﻢ ﺛﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻠﻮﻧﻬﻢ، ﺛﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ
ﻳﻠﻮﻧﻬﻢ، ﺛﻢ ﻳﺠﻲﺀ ﻗﻮﻡ ﺗﺒﺪﺭ ﺷﻬﺎﺩﺓ ﺃﺣﺪﻫﻢ ﻳﻤﻴﻨﻪ
ﻭﺗﺒﺪﺭ ﻳﻤﻴﻨﻪ ﺷﻬﺎﺩﺗﻪ(( ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ
ﺍﻟﺸﻬﺎﺩﺍﺕ ﺑﺎﺏ ﻻ ﻳﺸﻬﺪ ﻋﻠﻰ ﺷﻬﺎﺩﺓ ﺟﻮﺭ ﺇﺫﺍ ﺷﻬﺪ
(2652)، ﻭﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺑﺎﺏ ﻓﻀﻞ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺛﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻠﻮﻧﻬﻢ 2533) ). Dalilin
fifikonsu shine, sun yi imani tun da
wuri, sun samu rigaye. Sun taimaki
manzon Allah a lokacin tsanani da
bukata. Sun kuma yaxa addini, sun
samu ladar duk wanda yake bayan
su. Duba At- Tamhid na Ibn Abdil
Barr (20/251) da Faidh Al Qadeer
na Munawee (3/478). 2. Sahabbai
su ne garkuwar wannan al’umma
ﻓﻔﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺑﺮﺩﺓ
ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻣﻮﺳﻰ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺑﺮﺩﺓ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻗﺎﻝ : ﺻﻠﻴﻨﺎ
ﺍﻟﻤﻐﺮﺏ ﻣﻊ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ – ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ –
ﺛﻢ ﻗﻠﻨﺎ : ﻟﻮ ﺟﻠﺴﻨﺎ ﺣﺘﻰ ﻧﺼﻠﻲ ﻣﻌﻪ ﺍﻟﻌﺸﺎﺀ ، ﻗﺎﻝ :
ﻓﺠﻠﺴﻨﺎ ﻓﺨﺮﺝ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻘﺎﻝ ” :ﻣﺎ ﺯﻟﺘﻢ ﻫﻬﻨﺎ ؟” ﻗﻠﻨﺎ :
ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ، ﺻﻠﻴﻨﺎ ﻣﻌﻚ ﺍﻟﻤﻐﺮﺏ . ﺛﻢ ﻗﻠﻨﺎ ،
ﻧﺠﻠﺲ ﺣﺘﻰ ﻧﺼﻠﻲ ﻣﻌﻚ ﺍﻟﻌﺸﺎﺀ ،ﻗﺎﻝ ” :ﺃﺣﺴﻨﺘﻢ ﺃﻭ
ﺃﺻﺒﺘﻢ” ﻗﺎﻝ ﻓﺮﻓﻊ ﺭﺃﺳﻪ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﻛﺎﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ
ﻣﻤﺎ ﻳﺮﻓﻊ ﺭﺃﺳﻪ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻓﻘﺎﻝ “ﺍﻟﻨﺠﻮﻡ ﺃﻣﻨﺔ
ﻟﻠﺴﻤﺎﺀ . ﻓﺈﺫﺍ ﺫﻫﺒﺖ ﺍﻟﻨﺠﻮﻡ ﺃﺗﻰ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻣﺎ ﺗﻮﻋﺪ .
ﻭﺃﻧﺎ ﺃﻣﻨﺔ ﻟﺼﺤﺎﺑﻲ ﻓﺈﺫﺍ ﺫﻫﺒﺖ ﺃﺗﻰ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﻣﺎ
ﻳﻮﻋﺪﻭﻥ ﻭﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﺃﻣﻨﺔ ﻷﻣﺘﻲ ، ﻓﺈﺫﺍ ﺫﻫﺐ
ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﺃﺗﻰ ﻷﺻﺤﺎﺑﻲ ﻣﺘﻰ ﻣﺎ ﻳﻮﻋﺪﻭﻥ” ﺃﺧﺮﺟﻪ
ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺑﺎﺏ ﺑﻴﺎﻥ ﺃﻥ ﺑﻘﺎﺀ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ 2531) ).
Fassarar wannan shine, kamar
yadda taurari suke garkuwa ga
wargajewar sama da faruwar
tashin qiyama, idan sun gushe
alqiyama zata faru. Haka shi kuma
Annabi (SAW) garkuwa ne daga
rabuwar kan sahabbai da aukuwar
fitinar yaqin basasa a tsakaninsu.
Amma bayan wucewar sa hakan ta
faru. Su kuma sahabbai garkuwa
ne ga al’ummar musulmi daga
fantsama a cikin bidi’ah da lalata
hasken addini. Amma bayan
wucewar su sai wannan ya faru.
Duba sharhin Imam An Nawawi a
kan Sahih Muslim (16/83). Muna
iya lura cewa, hadisin ya bada
cikakkiyar sheda ga tsarkin
addininsu da kyawon aqidarsu,
amma bai mayar da su ma’asumai
ba. Wannan kuwa ya zo daidai da
ayoyin Alqur’ani masu yawa da
suka yaba ma imaninsu da
hijirarsu da jihadinsu da suka yi
saboda neman yardar Allah. 3.
Darajar Mujahidan Badar: ﻋﻦ ﺭﻓﺎﻋﺔ
ﺑﻦ ﺭﺍﻓﻊ ﺍﻟﺰﺭﻗﻲ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ـ ﻭﻛﺎﻥ ﺃﺑﻮﻩ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺑﺪﺭ
ـ ﻗﺎﻝ: ﺟﺎﺀ ﺟﺒﺮﻳﻞ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻓﻘﺎﻝ: ﻣﺎ ﺗﻌﺪﻭﻥ ﺃﻫﻞ ﺑﺪﺭ ﻓﻴﻜﻢ؟ ﻗﺎﻝ” :ﻣﻦ ﺃﻓﻀﻞ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ” ـ ﺃﻭ ﻛﻠﻤﺔ ﻧﺤﻮﻫﺎ ـ ﻗﺎﻝ: ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻣﻦ
ﺷﻬﺪ ﺑﺪﺭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ.” ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ
ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻐﺎﺯﻱ ﺑﺎﺏ: ﺷﻬﻮﺩ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﺑﺪﺭﺍ
(3992)، ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻘﺪﻣﺔ ﺑﺎﺏ ﻓﻀﻞ ﺃﻫﻞ
ﺑﺪﺭ .(160) ﻭﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﻋﺒﺪﺍ
ﻟﺤﺎﻃﺐ ﺟﺎﺀ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻳﺸﻜﻮ ﺣﺎﻃﺒﺎ ﻓﻘﺎﻝ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻴﺪﺧﻠﻦ ﺣﺎﻃﺐ
ﺍﻟﻨﺎﺭ، ﻓﻘﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ:
“ﻛﺬﺑﺖ، ﻻ ﻳﺪﺧﻠﻬﺎ، ﻓﺈﻧﻪ ﺷﻬﺪ ﺑﺪﺭﺍ ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺒﻴﺔ”
ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺑﺎﺏ: ﻣﻦ
ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺃﻫﻞ ﺑﺪﺭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ 2495) ).
Wannan gafara da Allah ya yi wa
mujahidan Badar ta shafi
hukuncinsu a alqiyama ne. Amma
a nan duniya ana yanke masu
hukunci idan sun yi laifi kamar
kowa. Kamar yadda manzon Allah
(SAW) ya tsayar da haddi a kan
Misxah bin Uthatha a lokacin ya sa
bakinsa cikin qazafin da aka yi wa
uwar muminai. Haka shi ma
sayyidina Umar (RA) ya tsayar da
haddin shan giya a kan Qudamah
bin Maz’un. Duka su biyun na daga
cikin mujahidan Badar da Allah ya
gafarta ma. 4. Matsayin waxanda
suka halarci yaqin Uhud ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” : ﻟﻤﺎ ﺃﺻﻴﺐ ﺇﺧﻮﺍﻧﻜﻢ ﺑﺄﺣﺪ ﺟﻌﻞ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﺃﺭﻭﺍﺣﻬﻢ ﻓﻲ ﺃﺟﻮﺍﻑ ﻃﻴﺮ ﺧﻀﺮ ﺗﺮﺩ
ﺃﻧﻬﺎﺭ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﺗﺄﻛﻞ ﻣﻦ ﺛﻤﺎﺭﻫﺎ، ﻭﺗﺄﻭﻱ ﺇﻟﻰ ﻗﻨﺎﺩﻳﻞ
ﻣﻦ ﺫﻫﺐ ﻓﻲ ﻇﻞ ﺍﻟﻌﺮﺵ، ﻓﻠﻤﺎ ﻭﺟﺪﻭﺍ ﻃﻴﺐ
ﻣﺸﺮﺑﻬﻢ ﻭﻣﺄﻛﻠﻬﻢ ﻭﺣﺴﻦ ﻣﻨﻘﻠﺒﻬﻢ ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﻳﺎ ﻟﻴﺖ
ﺇﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ﺑﻤﺎ ﺻﻨﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻨﺎ ﻟﺌﻼ ﻳﺰﻫﺪﻭﺍ ﻓﻲ
ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻭﻻ ﻳﻨﻜﻠﻮﺍ ﻋﻦ ﺍﻟﺤﺮﺏ ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ:
ﺃﻧﺎ ﺃﺑﻠﻐﻬﻢ ﻋﻨﻜﻢ”، ﻓﺄﻧﺰﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﻫﺆﻻﺀ
ﺍﻵﻳﺎﺕ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻟﻪ} :ﻭﻻ ﺗﺤﺴﺒﻦ ﭐﻟﺬﻳﻦ ﻗﺘﻠﻮﺍ ﻓﻰ
ﺳﺒﻴﻞ ﭐﻟﻠﻪ ﺃﻣﻮﺗﺎ ﺑﻞ ﺃﺣﻴﺎﺀ ﻋﻨﺪ ﺭﺑﻬﻢ ﻳﺮﺯﻗﻮﻥ] {ﺁﻝ
ﻋﻤﺮﺍﻥ.[169: ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ
ﺑﺎﺏ: ﻓﻲ ﻓﻀﻞ ﺍﻟﺸﻬﺎﺩﺓ (2520)، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻹﻣﺎﻡ
ﺃﺣﻤﺪ ﻓﻲ ﻣﺴﻨﺪﻩ ﺑﺮﻗﻢ (2384)، ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺣﺴﻨﻪ
ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺑﺮﻗﻢ (2199)
)2/4795 .( . Darajar waxanda suka
yi mubaya’a a Hudaibiyyah ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ
ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﻟﻨﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺤﺪﻳﺒﻴﺔ” :ﺧﻴﺮ ﺃﻫﻞ
ﺍﻷﺭﺽ” ﻭﻛﻨﺎ ﺃﻟﻔﺎ ﻭﺃﺭﺑﻌﻤﺎﺋﺔ، ﻭﻟﻮ ﻛﻨﺖ ﺃﺑﺼﺮ
ﻷﺭﻳﺘﻜﻢ ﻣﻮﺿﻊ ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ. ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ
ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻐﺎﺯﻱ ﺑﺎﺏ: ﻏﺰﻭﺓ ﺍﻟﺤﺪﻳﺒﻴﺔ (4155)،
ﻭﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻹﻣﺎﺭﺓ ﺑﺎﺏ: ﺍﺳﺘﺤﺒﺎﺏ ﻣﺒﺎﻳﻌﺔ
ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺠﻴﺶ .(4155) ﻭﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗﺎﻝ: ﺃﺧﺒﺮﺗﻨﻲ ﺃﻡ ﻣﺒﺸﺮ: ﺃﻧﻬﺎ
ﺳﻤﻌﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻝ ﻋﻨﺪ
ﺣﻔﺼﺔ” :ﻻ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﺇﻥ ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺃﺻﺤﺎﺏ
ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ ﺃﺣﺪ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺑﺎﻳﻌﻮﺍ ﺗﺤﺘﻬﺎ” ﻗﺎﻟﺖ: ﺑﻠﻰ ﻳﺎ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻓﺎﻧﺘﻬﺮﻫﺎ ﻓﻘﺎﻟﺖ ﺣﻔﺼﺔ} :ﻭﺇﻥ ﻣﻨﻜﻢ ﺇﻻ
ﻭﺍﺭﺩﻫﺎ{ ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ)) :ﻗﺪ
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ} :ﺛﻢ ﻧﻨﺠﻰ ﭐﻟﺬﻳﻦ ﭐﺗﻘﻮﺍ ﻭﻧﺬﺭ
ﭐﻟﻈـﻠﻤﻴﻦ ﻓﻴﻬﺎ ﺟﺜﻴﺎ] {ﻣﺮﻳﻢ(([72: ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ
ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺑﺎﺏ: ﻣﻦ ﻓﻀﺎﺋﻞ
ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ ﻭﺃﻫﻞ ﺑﻴﻌﺔ ﺍﻟﺮﺿﻮﺍﻥ .(2496)
6. Son Sahabbai Wajibi ne: ﻋﻦ ﻋﺒﺪ
ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﻐﻔﻞ ﺍﻟﻤﺰﻧﻲ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” : ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ، ﻻ
ﺗﺘﺨﺬﻭﻫﻢ ﻏﺮﺿﺎ ﺑﻌﺪﻱ، ﻓﻤﻦ ﺃﺣﺒﻬﻢ ﻓﺒﺤﺒﻲ ﺃﺣﺒﻬﻢ،
ﻭﻣﻦ ﺃﺑﻐﻀﻬﻢ ﻓﺒﺒﻐﻀﻲ ﺃﺑﻐﻀﻬﻢ، ﻭﻣﻦ ﺁﺫﺍﻫﻢ ﻓﻘﺪ
ﺁﺫﺍﻧﻲ، ﻭﻣﻦ ﺁﺫﺍﻧﻲ ﻓﻘﺪ ﺁﺫﻯ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﺁﺫﻯ ﺍﻟﻠﻪ
ﻳﻮﺷﻚ ﺃﻥ ﻳﺄﺧﺬﻩ” ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ
ﺍﻟﻤﻨﺎﻗﺐ ﺑﺎﺏ: ﻓﻴﻤﻦ ﺳﺐ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ (3862) ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺿﻌﻔﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ
ﺿﻌﻴﻒ ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﺑﺮﻗﻢ (808) ﻭﻗﺎﻝ ﻋﻨﻪ
ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ: ﻫﺬﺍ ﺣﺪﻳﺚ ﺣﺴﻦ ﻏﺮﻳﺐ ﻻ ﻧﻌﺮﻓﻪ ﺇﻻ ﻣﻦ
ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻮﺟﻪ7 . . Son “Ansar” yana cikin
Imani: ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ” :ﻻ ﻳﺒﻐﺾ
ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﺭﺟﻞ ﻳﺆﻣﻦ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻵﺧﺮ” ﺃﺧﺮﺟﻪ
ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻨﺎﻗﺐ ﺑﺎﺏ: ﺣﺐ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ
(3783) ، ﻭﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺑﺎﺏ
ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺣﺐ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﻋﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻪ .(75) ﻭﻋﻦ ﻋﺪﻱ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ ﻗﺎﻝ: ﺳﻤﻌﺖ
ﺍﻟﺒﺮﺍﺀ ﻳﺤﺪﺙ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ
ﻗﺎﻝ ﻓﻲ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ” : ﻻ ﻳﺤﺒﻬﻢ ﺇﻻ ﻣﺆﻣﻦ، ﻭﻻ
ﻳﺒﻐﻀﻬﻢ ﺇﻻ ﻣﻨﺎﻓﻖ، ﻣﻦ ﺃﺣﺒﻬﻢ ﺃﺣﺒﻪ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻦ
ﺃﺑﻐﻀﻬﻢ ﺃﺑﻐﻀﻪ ﺍﻟﻠﻪ” ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ
ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺑﺎﺏ: ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺣﺐ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻭﻋﻠﻲ
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ 8 (76) . Wasici da iyalan
gidan manzon Allah (SAW) ﻗﻮﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” :ﺃﻣﺎ ﺑﻌﺪ: ﺃﻻ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ،
ﻓﺈﻧﻤﺎ ﺃﻧﺎ ﺑﺸﺮ ﻳﻮﺷﻚ ﺃﻥ ﻳﺄﺗﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺭﺑﻲ ﻓﺄﺟﻴﺐ،
ﻭﺃﻧﺎ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺛﻘﻠﻴﻦ: ﺃﻭﻟﻬﻤﺎ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻬﺪﻯ
ﻭﺍﻟﻨﻮﺭ ﻓﺨﺬﻭﺍ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺳﺘﻤﺴﻜﻮﺍ ﺑﻪ” ﻓﺤﺚ
ﻋﻠﻰ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﻏﺐ ﻓﻴﻪ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ” : ﻭﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ،
ﺃﺫﻛﺮﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ، ﺃﺫﻛﺮﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﻫﻞ
ﺑﻴﺘﻲ، ﺃﺫﻛﺮﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ” ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ ﻓﻲ
ﻛﺘﺎﺏ ﻓﻀﺎﺋﻞ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺑﺎﺏ: ﻓﻀﺎﺋﻞ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ
ﻃﺎﻟﺐ 2408) ). Masu dogon nazari
daga vikin ma’abota ilmi sun gano
a wannan hadisi cewa, manzon
Allah (SAW) yana sane da cewa,
tafiyar da sha’anin wannan
al’umma a bayansa ba ga iyalansa
zai koma ba. Domin da su ne zamu
mulki sai ya ce ma su “Ina tunatar
da ku Allah game da sahabbaina”.
9. Hatsarin cuta masu ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﻣﻐﻔﻞ ﺍﻟﻤﺰﻧﻲ _ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ_ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ -ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” – ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ
ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ، ﻻ ﺗﺘﺨﺬﻭﻫﻢ
ﻏﺮﺿﺎ ﺑﻌﺪﻱ ﻓﻤﻦ ﺃﺣﺒﻬﻢ ﻓﺒﺤﺒﻲ ﺃﺣﺒﻬﻢ ﻭﻣﻦ
ﺃﺑﻐﻀﻬﻢ ﻓﺒﺒﻐﻀﻲ ﺃﺑﻐﻀﻬﻢ ﻭﻣﻦ ﺁﺫﺍﻫﻢ ﻓﻘﺪ ﺁﺫﺍﻧﻲ
ﻭﻣﻦ ﺁﺫﺍﻧﻲ ﻓﻘﺪ ﺁﺫﻯ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺒﺎﺭﻙ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﻣﻦ ﺁﺫﻯ
ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻴﻮﺷﻚ ﺃﻥ ﻳﺄﺧﺬﻩ” ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ 5/54 ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
(3862) ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﻌﺐ 2/191 ﻭﻗﺎﻝ
ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ : ﻫﺬﺍ ﺣﺪﻳﺚ ﻏﺮﻳﺐ ﻻ ﻧﻌﺮﻓﻪ ﺇﻻ ﻣﻦ ﻫﺬﺍ
ﺍﻟﻮﺟﻪ ﺍ.ﻫـ 10 . . Haramcin zagin su ﻋﻦ
ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ _ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ_ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ -ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” – ﻻ ﺗﺴﺒﻮﺍ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﻻ
ﺗﺴﺒﻮﺍ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ ﻓﻮﺍﻟﺬﻱ ﻧﻔﺴﻲ ﺑﻴﺪﻩ ﻟﻮ ﺃﻥ ﺃﺣﺪﻛﻢ
ﺃﻧﻔﻖ ﻣﺜﻞ ﺃﺣﺪ ﺫﻫﺒﺎ ﻣﺎ ﺃﺩﺭﻙ ﻣﺪ ﺃﺣﺪﻫﻢ ﻭﻻ ﻧﺼﻴﻔﻪ”
ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ( 3470) ﻭﻣﺴﻠﻢ (2540) ﻭﺍﻟﻠﻔﻆ
ﻟﻪ . ﻭﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ” :ﻣﻦ ﺳﺐ ﺃﺻﺤﺎﺑﻲ
ﻓﻌﻠﻴﻪ ﻟﻌﻨﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ” ﺃﺧﺮﺟﻪ
ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ )3/174( ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺑﻤﺠﻤﻮﻉ
ﻃﺮﻗﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ 2340) ).
Sharhin Ibn Taimiyyah a kan
waxannan hadissai: Shehin
musulunchi Ibn Taimiyyah yana
cewa: “Hadisan nan da ke
maganar girman matsayin
sahabbai da yaba masu da fifita
zamaninsu a kan na bayan su
hadisai ne da suka game duniya
(Mutawatirai). Saboda haka yin
suka a kan su yin suka ne ga
Alqur’ani da hadisi. Don haka ne
ma mutane (yana nufin malamai)
suka rinka magana a kan kafircin
‘yan Shi’ah, bayanin da mun riga
mun shinfida shi a wani littafi ba
wannan ba”. Majmu’ Al- Fatawa
(4/430). Akwai kuma hadisai masu
tarin yawa da suka bayyana falalar
wasu xaixaiku daga cikin sahabbai
da iyalan manzon Allah (SAW)
waxanda ba za a samu damar
kawo su ba – saboda buqatar
taqaitawa – a cikin wannan mukala.
Amma a qunshe suke cikin “Kitabul
Fadha’il” na cikin Sahihul Bukhari
da Sahihu Muslim da sauran
littafan Sunnah. Shubhohin ‘Yan
Shi’ah Daga Cikin Hadisai Addinin
Shi’ah shubha ce zallarta. Shi ya
sa ba su da aiki sai wahalar da
malamai wajen maida masu
martani. Haka kuma addinin nasu
addini ne marar makama. Zaka
gane wannan in kayi la’akari da
cewa, duk wata aqidarsu ko
fahimtarsu zaka iya warware ta
daga cikin littafansu xin kansu.
‘Yan Shi’ah sukan yi fatali da
hadissan nan duka da muka kawo
da ma duk ire-irensu. Hujjarsu a
kan wannan ita ce, ai su dai
sahabban ne suka ruwaito hadisan
da kansu. Idan kuwa aka bi
wannan tafarki nasu – na qin
amincewa da sahabbai, duk da
yake Allah da kansa ya amince da
su – Alqur’ani ma ba zai tsira ba tun
da su ne suka karantar da mu shi.
A maimakon haka, ‘yan Shi’ah
suna amfani da wasu hadissai
wajen suka da tuhuma da suke yi
ma sahabban manzon Allah (SAW)
cewa, sun yi ridda kuma sun canja
addini. Ga yadda hadissan da su
ke kafa hujja da su suke: Na farko:
Hadisai Ingantattu Akwai hadissan
da suke ingantattu ne amma ba su
nuna zargi ko suka ga sahabbai,
sai dai sukan jirkita ma’anarsu ko
su xora su a inda son zuciyarsu ya
ga dama. Misalin wannan shi ne:
Hadisin Ridda An fi sanin wannan
hadisi da “Hadith Al- Haudh” kuma
ingantaccen hadisi ne wanda babu
tantama a game da ingancinsa. Sai
dai masu son zuciya sun yi amfani
da shi don qarfafa tuhumar da
suke yi ma sahabban manzon
Allah (SAW) da yin ridda bayan
wafatinsa. Nassin hadisin: ﻋﻦ ﺳﻬﻞ
ﺑﻦ ﺳﻌﺪ ﻗﺎﻝ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” : ﺇﻧﻲ
ﻓﺮﻃﻜﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﻮﺽ، ﻣﻦ ﻣﺮ ﻋﻠﻲ ﺷﺮﺏ ﻭﻣﻦ
ﺷﺮﺏ ﻟﻢ ﻳﻈﻤﺄ ﺃﺑﺪﺍ. ﻟﻴﺮﺩﻥ ﻋﻠﻲ ﺃﻗﻮﺍﻡ ﺃﻋﺮﻓﻬﻢ
ﻭﻳﻌﺮﻓﻮﻧﻲ ﺛﻢ ﻳﺤﺎﻝ ﺑﻴﻨﻲ ﻭﺑﻴﻨﻬﻢ.” ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺣﺎﺯﻡ :
ﻓﺴﻤﻌﻨﻲ ﺍﻟﻨﻌﻤﺎﻥ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﻴﺎﺵ ﻓﻘﺎﻝ ﻫﻜﺬﺍ ﺳﻤﻌﺖ
ﻣﻦ ﺳﻬﻞ؟ ﻓﻘﻠﺖ: ﻧﻌﻢ. ﻓﻘﺎﻝ ﺍﺷﻬﺪ ﻋﻠﻰ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪ
ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ ﻟﺴﻤﻌﺘﻪ ﻭﻫﻮ ﻳﺰﻳﺪ ﻓﻴﻬﺎ “ﻓﺄﻗﻮﻝ: ﺇﻧﻬﻢ ﻣﻨﻲ
ﻓﻴﻘﺎﻝ ﺍﻧﻚ ﻻ ﺗﺪﺭﻱ ﻣﺎ ﺃﺣﺪﺛﻮﺍ ﺑﻌﺪﻙ، ﻓﺄﻗﻮﻝ ﺳﺤﻘﺎ
ﺳﺤﻘﺎ ﻟﻤﻦ ﻏﻴﺮ ﺑﻌﺪﻱ” ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ٦٠٩٧
An karbo daga Abu Hazim daga
Sahl bin Sa’ad (RA) ya ce, annabi
(SAW) ya ce: “Ni zan riga ku zuwa
tafkin (Al-Kauthar). Duk wanda ya
same ni a wurin zai sha. Wanda
kuwa duk ya sha ba zai sake qishi
ba har abada. Kuma lalle wasu
jama’a zasu same ni, na san su,
sun san ni. Sannan sai a
shamakance a tsakani na da su”.
Abu Hazim ya ce: Sai Nu’uman bin
abi Ayyash ya ji ina faxin hadisin,
sai ya ce, haka ka ji shi a wurin
Sahl bin Sa’ad (RA)? Sai na ce, eh.
Ya ce, ni kuma na sheda cewa na
ji shi daga Abu Sa’id Al-khudri (RA)
kuma yana qarawa da cewa, “Sai
in ce, su suna daga gare ni. Sai a
ce min, ai baka san irin abinda
suka farar ba a bayanka. Sai in ce,
nesa.. nesa da waxanda suka
canja a bayana”. Wannan hadisi
ya tabbata ta hanyar sahabbai da
dama kamar Anas (Bukhari 6582,
Muslim 2304) da Sahl bin Sa’ad
(Bukhari 6585) da Asma’u bint
Abibakr (Bukhari 6593, Muslim
2293) da Abdullahi bin Mas’ud
(Bukhari 6593) da wasu sahabbai
da dama. Kuma ya zo da lafazi iri
daban daban, wanda ya tattara
lafuzzansa idan yana da tsarkin
zuciya zai yi ma sa fahimta mai
kyau. Ya kuwa za ayi mai tsarkin
zuciya da ya yarda da abinda Allah
da manzo ya faxi a kan su cewa,
Allah ya yarda da su, kuma ya san
tsarkin zukatansu, har ya ce ya
bada misalinsu a cikin Taurata da
Linjila, kuma ya yaba ma su a kan
jihadin da suka yi da taimakon
manzon Allah, sannan ya jinjina
ma masu yi masu addu’a da roqon
gafara, ya yi allawaddai da
munafukai da ke masu izgili, kuma
ya ce, da su ne ya qarfafi
annabinsa. Ya za ayi wanda ya
yarda da wannan ya munana
fahimtar irin wannan hadisi?! Tarihi
ma ba zai qarfafa maganar riddar
sahabbai ba in aka kalli irin
jajircewar da suka yi da
sadaukarwa wadda tarihi bai tava
ganin irinta ba. Kuma ma da ridda
ta bayyana bayan wafatin manzon
Allah (SAW) ai sahabban ne suka
yaqi ‘yan ridda. Ga dai wasu daga
cikin maganganun malamai
magadan annabawa masu tsarkin
zuciya a kan wannan hadisi: 1.
Hadisin ya yi maganar waxanda
zasu yi ridda ne, ya kira su
sahabbai da ma’anar su mabiyan
annabi ne ba almajirai ko
sahabban da suka zauna da shi
ba. Kamar yadda ake cewa
“As’habu Malik” da “As’habus
Shafi’i” da sauran su. 2. Ba wanda
ya yi ridda daga cikin sahabban da
suka zauna tare da manzon Allah
(SAW). Waxanda suka yi ridda
sune qauyawan da suka ji labarin
musulunci kuma suka musulunta
saboda wasu dalilai, amma basu
tava taimaka ma addini ko yin yaqi
don kariyar sa ba. Waxannan ‘yan
kaxan ne kamar yadda lafazin
“Usaihabi” wato ‘yan sahabbaina
yake nunawa. Haka ma akwai
ruwayar da ta ce, “Rahxun min
as’habi” wanda yake nuna
yawansu daga mutane uku ne
zuwa goma domin shi kalmar
“Rahx” take nunawa. 3. Ko kuma
yana nufin su munafukai ne tunda
bai san su duka ba kamar yadda
Allah ya ce: “Kai ba ka san su ba.
Mu ne muka san su”. Kuma ai a
zahiri su sahabbai ne tunda sun
shiga cikin jama’arsa. shi ya sa da
aka ce ma manzon Allah (SAW) ya
kashe su ya ce, a’a. Ba zan bari
mutane su ce Muhammadu yana
kashe sahabbansa ba”. 4. Wasu
malaman na ganin cewa, hadisin
yana nuni da ‘yan bidi’a da suka
canja addinin Allah daga yadda
manzo ya bar shi domin a hadisin
yana cewa: “Sai a ce min: ba ka
san irin abinda suka farar ba a
bayanka”. 5. Wasu malaman na
ganin ban da ‘yan bidi’a ma akwai
yiwuwar masu sabo su shiga ciki.
Tunda wannan magana ta nuna
zasu shiga wuta amma ba ta nuna
zasu dawwama ba. 6. Wasu kuma
na da ra’ayin cewa, hadisin na nuni
ne zuwa ga Khawarij, waxanda
hadisai da dama sun bayyana su
da masu ficewa daga addini kamar
yadda kibiya ke fita daga dabbar
da aka harba. Duk waxannan
maganganu suna tattare a littafin
Imam An-Nawawi na sharhin Sahih
Muslim (3/136-137). Shi kuma
shehun malamin nan na malikiyyah
Al-Hafizh Ibn Abdilbarr yana ganin
cewa, duk waxannan da aka faxa
zai yiwu a kore su daga shan
ruwan tafkin Al-Kauthar tunda yake
lafuzzan hadisin suna nuna haka.
At- Tamhid (20/262) da kuma At-
Tadhkirah na Imam Al-Qurtubi
(1/348). To, amma masu son
zuciya sai su kafa hujja da cewa,
annabi (SAW) ya ce ya san su. Sai
su manta ruwayar da ta faxi cewa
ya san su ne da alamomin da ke
fuskarsu da hannaye da qafafunsu
na hasken alwala. Nasibawa su
kuma sai su kan xora wannan
hadisi a kan sayyidina Ali da
‘ya’yansa. Ba kuwa yadda zaka iya
ba su amsa sai ta hanyar Ahlus-
Sunnah. Kuma duk wani yunqurin
tuhumar sahabbai da yin ridda idan
da zai tabbata a kan su to, ba zai
koru ba daga waxannan bayin
Allah. ina nufin sayyidina Ali da
‘ya’yansa. Allah ya yi mana kariya
daga son zuciya. Misali na biyu:
Hadisin Abdullahi bn Amr wanda
Muslim ya ruwaito cewa: ” ﺇﺫﺍ ﻓﺘﺤﺖ
ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺧﺰﺍﺋﻦ ﻓﺎﺭﺱ ﻭﺍﻟﺮﻭﻡ ﺃﻱ ﻗﻮﻡ ﺃﻧﺘﻢ؟” ﻓﻘﺎﻝ
ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻋﻮﻑ: ﻛﻤﺎ ﺃﻣﺮﻧﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ. ﻓﻘﺎﻝ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” : ﻛﻼ، ﺑﻞ
ﺗﺘﻨﺎﻓﺴﻮﻥ ﺛﻢ ﺗﺘﺪﺍﺑﺮﻭﻥ ﺛﻢ ﺗﺘﺒﺎﻏﻀﻮﻥ ﺛﻢ ﺗﻨﻄﻠﻘﻮﻥ
ﺇﻟﻰ ﻣﺴﺎﻛﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﻓﺘﺤﻤﻠﻮﻥ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻋﻠﻰ
ﺭﻗﺎﺏ ﺑﻌﺾ.” ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﺭﻗﻢ ٢٩٦٢
Wannan hadisi kamar yadda muka
gani ya tabbatar da cewa, masu
laifin ba muhajirai ne ba. Haka
kuma tarihi ya tabbatar ba Ansarai
ne ba. Domin babu inda Ansar
suka haxa muhajirai faxa. Su wane
ne kenan? Su ne ‘yan baya,
fitinannu, tsinannu irin su Ashtar
An-Nakha’i waxanda suka yi wa
sayyidina Usman (RA) juyin mulki
kuma suka kashe shi, suka
haddasa rikici mai yawa a tsakanin
al’umma. Misali na uku: Ruwayar
da ta zo daga Anas bn Malik (RA)
inda yake cewa: ﻻ ﺃﻋﺮﻑ ﺷﻴﺌﺎ ﻣﻤﺎ ﺃﺩﺭﻛﺖ
ﺇﻻ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﻗﺪ ﺿﻴﻌﺖ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﺭﻗﻢ
٥٣٠ Sai masu son zuciya – ‘Yan
Shi’ah – suna kafa hujja da
wannan magana cewa, sahabbai
sun canja komai na addini! Anas
(RA) kuwa ya faxi wannan
maganar ne a zamanin sarki Hajjaj
wanda aka san shi da jinkirta
sallah har lokacinta ya yi nisa. A
lokacin kuwa sahabbai na da
qaranci qwarai. kuma a kan haka
ne Ibnu Umar (RA) ya daina bin sa
sallah. Wasu kuma suka rinqa yin
sallarsu a cikin lokaci, idan ya tayar
da tasa sallar sai su bi shi a
matsayin nafila don kada su raba
kan jama’a kuma su janyo ma
kansu ta’addancinsa. Don haka ba
inda wannan magana ta Anas ta
nuna cewa sahabbai sun tozarta
sallah. Abin ban mamaki ma shine
yadda a wani lokaci zaka samu
nassoshi da suke nuna alherin
sahabbai sai – da gangan – a juya
su a mayar da su abin suka a gare
su. Misalin wannan shine hadisin
Abu Sa’id Al-Khudri (RA) da ke
cikin Bukhari da Muslim: ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪ
ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ) : ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺨﺮﺝ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﻭﺍﻷﺿﺤﻰ
ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﺼﻠﻰ، ﻓﺄﻭﻝ ﺷﻲﺀ ﻳﺒﺪﺃ ﺑﻪ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺛﻢ
ﻳﻨﺼﺮﻑ ﻓﻴﻘﻮﻡ ﻣﻘﺎﺑﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ – ﻭﺍﻟﻨﺎﺱ ﺟﻠﻮﺱ ﻋﻠﻰ
ﺻﻔﻮﻓﻬﻢ – ﻓﻴﻌﻈﻬﻢ ﻭﻳﻮﺻﻴﻬﻢ ﻭﻳﺄﻣﺮﻫﻢ، ﻓﺈﻥ ﻛﺎﻥ
ﻳﺮﻳﺪ ﺃﻥ ﻳﻘﻄﻊ ﺑﻌﺜﺎ ﻗﻄﻌﻪ ﺃﻭ ﻳﺄﻣﺮ ﺑﺸﻲﺀ ﺃﻣﺮ ﺑﻪ ﺛﻢ
ﻳﻨﺼﺮﻑ. ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺳﻌﻴﺪ: ﻓﻠﻢ ﻳﺰﻝ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ
ﺣﺘﻰ ﺧﺮﺟﺖ ﻣﻊ ﻣﺮﻭﺍﻥ – ﻭﻫﻮ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ – ﻓﻲ
ﺃﺿﺤﻰ ﺃﻭ ﻓﻄﺮ، ﻓﻠﻤﺎ ﺃﺗﻴﻨﺎ ﺍﻟﻤﺼﻠﻰ ﺇﺫﺍ ﻣﻨﺒﺮ ﺑﻨﺎﻩ
ﻛﺜﻴﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺼﻠﺖ، ﻓﺈﺫﺍ ﻣﺮﻭﺍﻥ ﻳﺮﻳﺪ ﺃﻥ ﻳﺮﺗﻘﻴﻪ ﻗﺒﻞ
ﺃﻥ ﻳﺼﻠﻲ ﻓﺠﺒﺬﺕ ﺑﺜﻮﺑﻪ ﻓﺠﺒﺬﻧﻲ ﻓﺎﺭﺗﻔﻊ ﻓﺨﻄﺐ
ﻗﺒﻞ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻘﻠﺖ ﻟﻪ: ﻏﻴﺮﺗﻢ ﻭﺍﻟﻠﻪ، ﻗﺎﻝ: ﺃﺑﺎ ﺳﻌﻴﺪ
ﻗﺪ ﺫﻫﺐ ﻣﺎ ﺗﻌﻠﻢ، ﻓﻘﻠﺖ: ﻣﺎ ﺃﻋﻠﻢ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎ ﻻ
ﺃﻋﻠﻢ، ﻓﻘﺎﻝ: ﺇﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻢ ﻳﻜﻮﻧﻮﺍ ﻳﺠﻠﺴﻮﻥ ﻟﻨﺎ ﺑﻌﺪ
ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﺠﻌﻠﺘﻬﺎ ﻗﺒﻞ ﺍﻟﺼﻼﺓ( ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ
(956) ﻭﺍﻟﻠﻔﻆ ﻟﻪ ﻭﻣﺴﻠﻢ 889) ). Ga shi
qarara a cikin hadisin sahabbai
suna kariyar sunnar manzon Allah
(SAW) daga canjin da ‘yan baya
suka yi, amma sai ake kawo
hadisin a matsayin hujjar cewa,
sun canja ma manzon Allah
sunnarsa. Shi kansa Marwan – duk
da yake ba sahabi ba ne – ya nuna
ijtihadi ne ya yi domin mutane su
saurari huxuba kar su watse, ba ya
yi haka ba ne kawai don yana son
ya canja sunnah. Kashi na biyu:
Hadisai Marasa Inganci da kuma
qagaggu waxanda aka kitsa su
musamman don tabbatar da
waccan aqida ta yin suka ga
almijiran fiyayyen halitta. Idan
muna maganar tarihi wannan fage
ba a ko magana. Domin abinda
kundin tarihi ya qunsa na labaran
qarya da shaci-faxi waxanda aka yi
su da wannan manufa ba wanda
ya san iyakarsu sai Rabbus-
samawati. Amma hadissan da aka
jingina ma manzon
Allah bisa qarya a kan xaixaikun
sahabbai da kuma ilahirinsu to,
waxannan malamai sun tona
asirinsu. A nan dai zamu bada ‘yan
misalai ne a kan abinda suka faxa
a kan wasu xaixaikun sahabbai: 1.
Hadisin “ﺇﺫﺍ ﺭﺃﻳﺘﻢ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻋﻠﻰ ﻣﻨﺒﺮﻱ ﻓﺎﻗﺘﻠﻮﻩ”
An bincika littafan musulunci gaba
xaya ba a samu wannan hadisi ba.
Don haka ne ma Ibnul Jauzi ya sa
shi a cikin “kundin hadisan qarya”
AL-MAUDHU’AT (2/25). Akwai xan
uwan wannan hadisi da yake
cewa: ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺎﻝ: ﺃﺗﻴﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﺴﻤﻌﺘﻪ ﻳﻘﻮﻝ” :ﻳﻄﻠﻊ ﻋﻠﻴﻜﻢ
ﺭﺟﻞ ﻳﻤﻮﺕ ﻋﻠﻰ ﻏﻴﺮ ﺳﻨﺘﻲ” ﻓﻄﻠﻊ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ . Da
na ukunsu wanda yake cewa: ﻗﺎﻡ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺧﻄﻴﺒﺎ ﻓﺄﺧﺬ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ
ﺑﻴﺪ ﺍﺑﻨﻪ ﻳﺰﻳﺪ ﻭﺧﺮﺝ ﻭﻟﻢ ﻳﺴﻤﻊ ﺍﻟﺨﻄﺒﺔ، ﻓﻘﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” :ﻟﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻟﻤﻘﻮﺩ “.
Ga dukkan alamu wanda ya qaga
wannan na uku ya haxa qarya da
rafkanwa. Domin kuwa tarihi ya
sheda cewa, ba a haifi Yazid ba a
zamanin manzon Allah (SAW) ko
zamanin Abubakar ko Umar (RA).
An haife shi ne a zamanin sarkin
musulmi Usman (RA). To, ya aka yi
manzon Allah (SAW) ya gan shi
har ya la’ance shi alhalin ba a ko
haife shi ba?! Malaman tarihi sun
haxu a kan kawo wasicin da
manzon Allah (SAW) ya yi wa
sayyidina Mu’awiyah cewa, idan ka
jivinci wani al’amari na wannan
al’umma to, ka ji tsoron Allah kuma
ka yi adalci. Wanda Mu’awiyah ya
ce, tun daga ranar nake xammahar
yin sarauta. Sau da yawa rashin
sani kan sa wasu daukar cewa,
samun irin waxannan hadisan a
cikin littafan Sunnah shi kaxai ya
isa ya tabbatar da ingancinsu. Da
yawa ma mabiyan Shi’ah kan yi
tutiya da wannan cewa ai ga
hadisan nan ma a cikin littafanku.
Alhali kuwa a duk inda aka samu
ruwaya wajibi ne a xora ta a
ma’aunin ilmi don tabbatar da
sahihancinta ko rauninta. Daga
nan ne ma za a iya gano ko idan
zuqi ta mallau ce. Sai fa idan an
same ta a xaya daga cikin littafan
zaqaquran malamai waxanda suka
sharxanta inganci kamar Bukhari
da Muslim. Qa’idar da Ahlus-
sunnah suke bi a game da ayoyi
da hadisai da ake ganin kamar sun
kunshi suka ga Sahabbai: 1. Dole
ne mu mayar da duk abinda ya
rikitar da mu zuwa ga wanda ba shi
da rikici. Alqur’ani a cike yake da
yabon sahabban manzon Allah.
Haka ma ingantattun hadisai. A
cikinsu har da waxanda suke ba su
shedar zama yardaddu a wurin
Allah, masu gaskiyar imani da yin
jihadi saboda Allah, da kuma
tabbatar da cewa su ‘yan aljanna
ne. 2. Duk nassin da ya saba ma
wannan idan aka bi diddigi za a
tarar bai inganta ba. Ko kuma ya
gamu da sauyi da canja magana
zuwa inda ba a nufe ta ba. Ilahirin
irin waxannan ruwayoyin na Abu
Mikhnaf da Hisham Al-Kalbi ne da
sauran maqaryata. 3. Idan kuwa ya
inganta bai wuce wani zunubi ne
da wani ko wasu daga cikin
sahabbai suka yi, tunda yake su ba
ma’asumai ba ne. 4. Galibin zunubi
idan ya zo daga irin waxannan
zavavvun bayin Allah bai wuce an
yi shi ne bisa ga kuskure ko ta’awili
ko ijtihadin da Allah yake uzuri
gare shi. 5. Umurnin da shari’a ta yi
na kyautata ma kowane musulmi
zato, da rashin shiga cikin rigar
mutuncinsa na wajabta a tantance
tarihin duk da yake da alaqa da
wasu magabatan musulmi
ballantana sahabbai. 6. Zunubi ba
shi hana zaman mutum xan
aljanna. kamar yadda ba shi
wajabta zargi ga irin waxannan
mutane bale zagi. Saboda akwai
yiwuwar wanda ya yi shi daga
bisani ya yi nadama ya koma ma
Allah ta hanyar tuba, ko kuma tarin
ladarsa ya shafe zunubin, ko an
jarabce shi da wata musiba a nan
duniya mai goge zunubbai, ko ya
samu addu’ar muminai daga cikin
mutane ko mala’iku – ko da a
bayan mutuwarsa – wadda ta
kankare zunubinsa, ko ya yi dace
da ceton manzon Allah (SAW) ko
dai duk wani dalilin da Allah zai
kuvutar da shi daga hatsarin
zunubin a cikin rahamarsa.
Nadewa An umurci musulmi da ya
zama mai kyautata addu’a ga
waxanda suka riga shi imani.
Kuma ya nemi Allah kariya daga
samun wani qulli a zuciyarsa na
qiyayya da jin zafi ga muminai. A
cikin waxanda suka riga mu yin
imani babu kamar sahabban
manzon Allah (SAW) su da
wannan addini ya kafu ta
hannunsu. Kuma bisa ga umurnin
da Allah ya xora ma manzonsa na
yin tarbiyyah a gare su, manzo ya
yi iyakar qoqarinsa ya kuma ci
nasara matuqa ta hanyar sauya
rayuwarsu daga shirka zuwa
tauhidi, daga jahiliyyah zuwa
musulunci. Hadisan manzon Allah
(SAW) a cike suke da yabawa a
kan waxannan tsarkakun bayi
kamar yadda Alqur’ani yake a cike
da yabon su. Taliqin Dr. Abubakar
Birnin Kudu (Shugaban zama):
Duk wanda ya samu matsala a kan
fahimtar matsayin sahabbai to, zai
samu gurguwar fahimta ga
addininsa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) KAMAR YADDA HADISAI SUKA BAYYANA SU(Mansur Sokoto)”
 1. asheer gimi Avatar

  allah ya bada lada

 2. Abubakar Usman Avatar
  Abubakar Usman

  Allah saka da alkhairi, amin.

 3. Bukhari Musa Avatar
  Bukhari Musa

  Allah kara taimako

Leave a Reply

Categories
Latest updates