Da sunan Allah Mai Rahama Mai
Jinkai. Tsira da aminci su tabbata
ga fiyayyen halitta, da alayensa da
sahabbansa gaba daya.
Na karanta rubutun da dan uwa
mal Madu Iro ya yi a cikin jaridar
Hausa Leadership, (ta ranar 14/
safar/1434 = 28/12/2012, bugu na
326) wanda ya yi masa take da
cewa : “Salatil Fatihi A Ma’aunin
Musulunci” Kuma babu ko shakka
ya yi kokarin ya fadi abin da ya
fahimta dangane da wannan salati
da aka dade ana ja-in-ja a kanshi,
sai dai kash bai tabo ruhin rikicin
ba, ko kuma in ce ya yi wa ruhin
rikicin shigar shantun kadangare,
don haka na ga ya dace in dan tofa
albarkacin bakina, watakila na kara
fito da wasu abubuwan da za su
sanya dan uwa Mal Madu ya kara
bincike akan wanda ya yi a baya.
Da farkon farawa dai bayan Mal
Madu ya kawo ayar da Allah ya
umarci muminai da su yi wa
Manzon Allah da salati sai ya ce,
“A tafsirin wannan aya, Ibni Kasir
ya kawo salatil fatihi a cikin wata
ruwaya a jerin salatan Annabi
(S.A.W) da ya kawo. Sai dai ya
dauke kalmomin “Nasiril hakki bil
hakki har zuwa karshe”, amma ya
dora wasu kalmomin a
maimakonsu”
Haka Mal Madu ya fada, amma
alal-hakika a cikin wannan magana
akwai lauje cikin nadi, saboda
kuwa Ibni Kasir bai kawo salatil
fatihi a cikin tafsirinsa ba, wurin da
Mal Madu yake son ya yi ishara
zuwa gare shi, ba salatin fatihi ba
ne Ibnu Kasir ya kawo, ya kawo
wata addu’a ce daga Sayyidina
Aliyyu Bini Abi Dalib (R.A.), wanda
a cikinta lafazin “Alfatihi lima
Uglika, Wal khatimi lima sabaka”
ya zo, banda wadannan lafuzza da
suka zo a cikinta, babu wasu
makamantansu daga lafuzzan
salatil fatihi, ballantanama a ce ya
kawota, wanda kuma na san Mal
Madu ya san Salatil Fatihi sosai, ya
kuma san ba yadda Ibnu Kasir ya
kawo ta daga sayyidina Aliyyu Bin
Abi Dalib (R.A) take ba. Kila dan
uwa Mal Madu ya ce, ai na ce ya
dauke wasu kalmomi a cikinta.
Anan sai in ce wannan tuhuma ce
mai girma ga babban malami Ibnu
Kasir, wanda bai kamata mal Madu
ya yi masa ita ba, saboda kuwa
Ibnu Kasir riwaya ya koro, ba wai
shi yake bayani ba, balle a ce ya
cire wani abu a ciki, ya kawo
riwaya ce yadda ya same ta, da
sanadinta, ya kuma fadi daga inda
ya rawaito ta, don haka, ba daidai
ba ne ko kadan a ce, wai ya cire
wasu kalmomi, kuma ma a lokacin
da Ibnu Kasir yake raye babu
salatil Fatihi, bai ma santa ba, bai
taba jin ta ba, to yaya zai cire wani
abu a cikinta, Sannan wani abu da
yake nuna sam ba haka lamarin
yake ba, shi ne ita wannan addu’a
da Ibnu Kasir ya kawo – wadda Mal
Madu yake son ya nuna salatil
fatihi ce – tsawonta ya ninka na
salatil fatihi sai uku alal akalli. Don
haka ina fata, mal Madu zai janye
wannan tuhuma, da ya yi wa
wannan malami anan gaba, duk
lokacin da ya zo bayani irin
wannan.
Abu na biyu, bayan Ibnu Kasir ya
kawo wannan addu’ar daga Aliyyu
(R.A) sai ya biyo da bayanin rashin
ingancinta, wanda ya wajaba a ce
Mal Madu ya kawo wannan bayani
nashi, don kiyaye wa da amanar
ilimi. Ibnu kasir (Allah ya yi masa
Rahama) ya ce – bayan ya kawo
waccan addu’a da Mal Madu ya ce
salatil Fatihi ce – “Wannan
(addu’a) abu ne shahararre daga
maganar Aliyyu (R.A), kuma Ibnu
Kutaibah ya yi magana a kan
wannan (addu’a) a cikin littafinsa
(Mushkilil Hadis) haka ma Abul
Husain Ahmad Bin Faris Allugawiy
ya yi magana a kanta a cikin wani
juzu’I da ya tatttara a kan falalar
salati ga Annabi, sai dai akwai
duba a cikin sanadinta,
Malaminmu Alhafiz Abul Hajjaj Al-
mizzi ya ce, “Salamatul Kindiy –
wanda daya ne daga cikin
maruwaita waccan addu’a – ba
sananne ne ba (wato Majhul ne)
kuma ma bai riski Aliyyu ba”.
(Duba Ibnu Kasir 3/517).
Da wadannan abubuwa guda biyu
zamu gane cewa, Ibnu Kasir bai
kawo salatil fatihi kwata-kwata a
cikin tafsirinsa ba, addu’ar da ya
kawo kuwa mai dauke da lafuzza
guda biyu irin na salatil fatihi daga
Sayyidina Aliyyu bata inganta ba.
Kuma wannan riwayar ce dai Mal
Madu yake cewa mai Ashafa ya
kawo salatil fatihi, wanda ita ma ba
salatil fatihi ba ce, waccan addu’ar
ce da Ibnu kasir ya fada, kuma
mun ji cewa bata inganta ba,
saboda salamatu (ba salma ba
kamar yadda Mal Madu ya rubuta)
bai riski Aliyyu ba, kamar Alhafiz
Abul Hajjaj Al-mizziy ya fada cikin
abin da Ibnu kasir ya nakalto.
Leave a Reply