Shin a Matsayinka Na Musulmi kanayin Abinda ya dace?

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah(Subhanahu wa ta’ala) bai samar damu akan wannan doron kasa ba face domin mu bauta masa, Duk wani abinda zamuyi toh bai dace ya zamto gaba da Bautar Allah ba. Amma sabida Gafala da ya shiga zukatan musulmai da yawa sun mance menene ya kawosu duniya, kuma wacce Hadafi sukazo cimmawa, Ya dace ya zamto musulmi a kowani lokacinsa yana lissafi, kada ya bari Gafala ta daukeshi, ya dace ko yaushe mutum ya rinka yi wa kansa hisabi shin Abinda Allah ya halicceni domin sa shi din nakeyi? Ya kamata musulmi ya zamto ya shagala da bautar Allah da kuma neman ilmi mai amfani na Addini da Kuma duniya, ta yadda zai sami damar Fahimtar Addininsa da kyau sannan kuma ya sami daman taimaka wa Al’ummarsa, Kada musulmi ya zamto kullun tunaninsa kansa da iyalansa kawai, A’a. Ya zamto Al’ummah ce a gabansa, ya za’ayi a sami ingatacciyar Al’ummah mai cikakken ilmi da Fahimtar Addini da kuma duniya, ta yadda da hakane za’a sami damar fitar da mutane daga kangi na Talauci da Jahilci da suke ciki.

Daga yanzu ka fara tunani. Shin acikin awowinka 24 Me kakeyi dasu? Kana amfani dasu yadda ya dace wurin bautar Allah da neman ilmi mai amfani ko wani aiki mai amfani? Ko kuma kana amfani dasu ne wurin wasa Da sharholiya? Ka tambayi kanka shin inda yanzu zan mutu Zanyi Farin cikin saduwa da Allah a irin halin da nake ciki? Ya kamata kullum a koda yaushe musulmi ya rinka tambayar kansa da kansa tambayoyi masu yawa irin wa’innan, domin Shi mutuwa Zuwa takeyi babu zato babu tsammani. Kuma iya abinda mutum yayi shi zai tarar, alkhairi ko Sharri. Allah yasa mudace, ya shiryar damu, ya rabamu da Gafala.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates