Allah maɗaukakin sarki yace:
{ وَمَن یَبۡتَغِ غَیۡرَ ٱلۡإِسۡلَـٰمِ دِینࣰا فَلَن یُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِی ٱلۡـَٔاخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَـٰسِرِینَ }
[Surah Âl-`Imrân: 85]
Fassara/Sharhi
Duk wanda ya nemi wanin Musulunci ya zama masa Addini, to baza'a karɓa daga gareshi ba, kuma yana daga cikin masu hasara ranar lahira.
Wannan aya tana nuna mana cewa Addini da Allah ya yarda dashi a ban ƙasa shine Addinin Musulunci, duk wanda yake kan wata Addini koma bayan Addinin Musulunci to akan ɓata yake, Allah ba zai karɓa masa ba, kuma yayi hasara duniya da lahira.
Haka nan duk wanda ya bauta wa Allah ba tare da umarnin Annabi ba, Ya ƙirƙiri wani nau’in bauta to shima wannan ba za’a karɓa masa ba kamar yadda Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayi bayani.
An Rawaito daga Ummuna Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace, Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Duk wanda yayi wani aiki na Addini wanda babu Umrnin mu aciki to an mayar masa.
Sahihu Muslim:1718
A wata riwaya kuma:
Wanda ya ƙirƙiri wani abu cikin wannan lamari namu(Addini) wanda baya cikinsa to an mayar masa.
Wannan yake nuna cewa mai ƙirƙirar wani nau’in ibada a Addini yana ɓata lokacinsa ne domin ba za’a amsa masa ba, kamar wanda yake bautar Allah ƙarƙashin wani Addini ba Musulunci ba.
Haka nan wannan Ayah tana nuna mana cewa duk wasu Addinai koma bayan Addinin Musulunci da Annabi yazo dashi an shafe su, Shari’ar Annabi ta shafe ta Annabawan da suka gabace shi.
sabida haka baya halatta Musumi ya nuna, ko ya furta cewa Yahudawa, ko Nasara suna kan daidai.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply