Tafsirin Suratu Hud Aya ta 6: Babu wani Halitta a ban kasa face Arzikinsa na hanun Allah

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah Maɗaukakin sarki yace:

وَمَا مِن دَاۤبَّةࣲ فِی ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ رِزۡقُهَا وَیَعۡلَمُ مُسۡتَقَرَّهَا وَمُسۡتَوۡدَعَهَاۚ كُلࣱّ فِی كِتَـٰبࣲ مُّبِینࣲ

[Surah Hûd: 6]

Fassara/Sharhi

Allah Maɗaukakin sarki yace: Babu wani abu mai rarrafe a ban ƙasa face Arziƙinsa Na hanun Allah, kuma Allah yasan Mazauninsa, da wurin da zai Mutu, duka wannan yana cikin littafi bayyananne.

Wannan Ayah tana ƙara mana Ƙarfin Imani da ƙaddara, Duk wani halitta da yake ban ƙasa, a ruwa ne ko a doron ƙasa Allah yasan da zaman sa kuma Allah shine zai Azurta shi. Mutum bazai taɓa samun wani abu ba sai abinda Allah ya ƙaddara masa zai samu. Haka nan idan Allah ya nufe mutum da samun wani abu babu wanda ya isa ya hanashi samun wannan abun koda ko duniya ne suka taru don su hana shi. Haka nan in Allah ya nufi mutum ba zai samu abu ba, babu wanda ya isa yasa ya samu koda ko duniya baki ɗaya ne suka taru don su sanya shi ya samu wannan abu. Sabida haka muji tsoron Allah mu kyautata nema mu dogara ga Allah, kada mu dogara da iyawan mu. Kada kuma mu yawaita kai koken Allah wurin mutane da nuna gajan haƙuri. Duk wahala da rashi da ake ciki abinda Allah ya ƙaddara zaka samu dole sai ka samu.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates